Ibrahim Auwal | May 30, 2017 | 0 Comments
Yadda zaka Bude Email Address Cikin Mintina
Qalilan Da Wayar Ka Ko Computer: So
dayawa mutane suna tambaya ya zasu bude
email ta waya,kuma akwai masu son su shiga
tsarin mu na v.i.p amma basu da email,to yau
ka tsaya ka natsu ka bude email dinka cikin
sauki. wasu tambaya suke shin hakan na
yiwuwa kuwa? Amsar itace YES... Mene Ne
Email? Email wata fasaha ce ta masu irinta,
wacce aka bullo da ita dan asan ka da ita
kuma ta zame maka makullin shiga gurare da
dama a internet, wanda wasu mutane sukan
samu matsala musamman idan sunje cika
form se a tambaye su email kaga sun fasa, da
email zaka iya tura saqo kuma kaima a turo
maka saqo, zaka iya tura hoto har da video
duka. kadan kenan daga bayanin email... Ya
ake bude email? kafin na amsa wannan
tambayar zan lissafo wasu daga cikin
sannanun email domains... 1. GMAIL
www.gmail.com 2. Yahoo!
www.yahoomail.com 3. AOL www.aol.com 4.
Hotmail www.hotmail.com 5. msn
www.msn.com Wacce ni nafi recommending
domin features dinta da sauqi gurin budeta
itace google mail wato GMAIL… gmail tana da
dadin sha’ani kuma suna baka kyauta 15 Gig
a idan ka budeta sabuwa, zaka iya tura saqon
sms kyauta ta gmail, kuma duk wanda yayi
maka reply zaka samu 5 additonal cikin gmail
sms dinka, zaka iya samun text msg a yayin
da sabon email ya shigo, zaka iya storing
contacts dinka ko kayi importing daga wayar
ka, idan kana da bb ka hadata da mail to
kwantar da hankalin ka domin nambobin
wayan ka na hawa kan gmail suna zama
incase ka yarda wayan ko an sace. Infact
gmail qarshe ne, kuma ku sani gmail duk
wata features ne dake tattare da google,
wanda goggle ko ba’a fada ba kasan babba
ce a yanar gizo, in Allah ya yarda zanyi
bayani akan google… Matakan da zaka bi
gurin bude gmail account, 1. Ka tanadi waya
ko computer wacce zaka iya hawa internet da
ita Idan kana da waya koda nokia C1 ce in
har zakayi browsing da ita to zata bude maka
email… Da farko>>> ka bude www.gmail.com
idan ta bude se kaje create account (with
computa or phone). Idan Ta Bude>>> da
computa zata nuna maka gurin saka suna,
sunan baba, username dinda kake so,
shekara, number waya, email din da kake
amfani da ita a wannan lokacin (idan baka da
email tun dama to ba lallai ne ka saka komai
a gurin ba), gurin saka password (password
din gmail daga takwas ne zuwa sama, zaka
iya saka number dinka yafi sauqin tunawa)
sannan zai fito maka da wasu rubutun aljanai
wai ka rubuta ka tabbatar masu kai ba robot
bane, ka duba da kyau ka rubuta yadda suka
rubuta tare da space idan sun saka… kana
haka se kayi markin din accept, kada ka
manta dole zaka fada masu ko kai male ne
ko female domin susan ko waye kai… idan ka
gama wannan duka se kayi next step, zai fito
maka da number dinka, sannan yace voice call
ko text (abun da suke nufi shine sunaso su
kiraka ko su tara maka saqo da wasu
nambobi domin verifying account din) se ka
saka number din da za’a iya kiranka da ita ko
a tura maka saqo, (in case kace su kira, dan
Allah kada su kira kace hello, domin computer
ne zata maka Magana, idan kuwa ina kusa
google suka kira kace hello ni dariya zanyi
maka).. kana saka number din da suka fada
maka ko kuma suka turo maka se kasa
continue, shikenan ka gama bude gmail, zasu
nuna maka congratulation, can qasa zasu ce
your email address is
Ibrokhan2016@gmail.com. Shikenan Da Fatan
An Gamsu. If You Have Question u are free to
ask?
Copied
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger