AISHA TSAMIYA ZATA SHIGA JAMI'A

Ibrahim Auwal | November 06, 2017 | 0 Comments
Ba mu yin Health Technology, inji jami'ar

Fitacciyar jarumar na ta kannywood wato A'isha Aliyu (Tsamiya) ta bayyana cewa ta samu gurbin karo karatu a Budaddiyar Jami'ar Njeriya,wato National Open University of Nigeria (NOUN).
A wata hira da aka yi da ita a gidan talbijin na Arewa24,jarumar ta bayyana cewar za ta karanta course din 'Health Technology' ne.

A amsar wata tambaya da mai gabatar da shirin "Kundin Kanbywood",wato Aminu A. Shariff (Momoh), ya yi mata, A'isha ta ce, "Yanzu na samu admission a Open University...Ina so in karanci Health Technology."

To amma mujallar Fim ta gano cewa ba a yin wannan kwas din a jami'ar.
Daraktan Watsa Labarai na jami'ar,Malam Ibrahim Sheme, ya fada wa mujallar Fim cewa,"Health Technology bai cikin jerin kwasakwasan da wannan jami'ar ke gudanarwa. Amma kwas din da jami'ar ke yi wanda ya kusanci abin da A'isha Tsamiya ke so ta karanta shi ne 'Public Health'."

Daraktan ya ce ya ji dadin kudirin A'isha na zurfafa karatun ta,musamman a NOUN.Ya ce yin hakan ya nuna cewa ita mace ce mai hazaka tare da kokarin inganta rayuwar ta.
Ya ba ta shawarar cewa ya kamata ta zabi kwas din da jami'ar ke gudanarwa, kuma an lissafa su a gidan yanar jami'ar,wato www.nouedu.net.

Sheme ya yi kira ga sauran 'yan fim da su yi kokari su je jami'ar Open University domin su zurfafa karatun su. Ya ce karatu a NOUN ba sai sun bar ayyukan da ke gaban su ba,domin shi karatun daga ko'ina mutum ya ke zai iya yin sa.

"Ba sai mutum ya tafi aji ba yadda ake yi a sauran jami'o'i,"inji shi."Haka kuma akwai rage kashe kudi fiye da na sauran manyan makarantu."

Ita dai NOUN,ta na daga cikin manyan jami'o'in Gwamnatin Tarayya.Daliban ta sun fi na kowace jami'a yawa a duk fadin Afrika ta Yamma,ba ma Nijeriya kadai ba.

BABU WANDA YA ISA YA TABA DARIKA YA ZAUNA LAFIYA

Ibrahim Auwal | November 06, 2017 | 0 Comments
Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya.Wanda shike kamar shugaban tijjaniya ta yankin wato Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bayyana cewa.

Naji ana rade-radin cewa 'yan "Izala na kokarin yin 'kulle-'kullen ganin cewa, an kawar da mu 'yan "Darika, kamar yadda suka zuga gwamnati ta kawar da 'yan "Shi'a.

Saboda haka ina tabbatar muku da cewa "Wallahi, da mutum ya taba 'yan "Darika a kasar nan gwara, in ana ruwa ya taba wutar "Lantarki da damuna, ya fi masa sauki__inji Sheikh Dahiru Bauchi.

Rahoto Daga :- Sirrin Siyasar Nijeriya

TSUNTUWA COMPLETE ALBUM

Ibrahim Auwal | November 03, 2017 | 0 Comments
ALBUM:Umar M. ShareeF Tsuntuwa Complete New Album 2017.
ina masu neman album din tsuntuwa na umar m sharif?
Bayan wani lokaci mai tsawo da akai ana jiran album din shahararren mawakinnan wato M Sharif mai suna tsuntuwa to yanzu ya  fito kuma kowa yana da damar saukardashi zauwa wayarsa
Yanzan Ga WaKokin Nan Kamar HaKa:


1, Umar M. ShareeF Intro Album


2, Umar M. ShareeF Best Of Tsintuwa


3, Umar M. ShareeF BanJin Dadin Labari


4, Umar M. ShareeF Ft- Abdul Mai Gashi Mama


5, Umar M. ShareeF Cikin Raina


6, Umar M. ShareeF Kiban Ruwan Zuma


7, Umar M. ShareeF Kinbani So


8, Umar M. ShareeF Gamo Dake


9, Umar M. ShareeF Na Baki Soyayyata


10, Umar M. ShareeF Kinshiga Raina


11, Umar M. ShareeF Meera


12. Umar M. ShareeF Taimakamin


14.  Umar M. ShareeF So Haka Yake Ashe


15. Umar M. ShareeF Zomu Zauna Dake


16. Umar M. ShareeF Yaki A Soyayya


17. Umar M. ShareeF Yaya ZanayiAyi sauraro lafiya

SADIK SANI SADIK MAI KWADAYI

Ibrahim Auwal | November 03, 2017 | 0 Comments
                                                   DoCLICK HERE TO DOWNLOAD
min saukar da wannan kayataccen vidiyon saiku danna link din nan dake SAMA..asha dariya lafiya

KAI DUNIYA WAI YARAN BAHAUSHE NE DA WANNAN ISKANCIN

Ibrahim Auwal | November 02, 2017 | 0 Comments
                                                    CLICK HERE TO DOWNLOAD

MAI MAGANI COMEDY BY SADIK SANI SADIK

Ibrahim Auwal | November 02, 2017 | 0 Comments

Gaskiya duk acikin yan Hausa film ba wanda ya kware a iya acting irin Sadik Sani Sadik,domin tabbatar da haka zaka iya kallan hanshakin comedinsa a wannan lin din dake kasa
                                            CLICK HERE TO DOWNLOAD
 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger