Airtel 500mb New Year Bonus Codes

Ibrahim Auwal | December 31, 2017 | 0 Comments

Airtel Free Data Bonus Offers Codes
*141*13*200# – which gives you 200MB worth of data.
*141*13*100# – which gives you 100MB
Bonus.
*141*13*50# – you get 50MB offer.
*141*13*1# – 1MB free data for you.
The above codes when dialled can give you up to 500MB worth of data if you are Lucky as they can be repeated up to at most 2times.
TIP: Works only on selected airtel sim cards

Bidiyon Yan Shi'a Mabiya Zakzaky A Coci

Ibrahim Auwal | December 31, 2017 | 1Comments

Lallai yan shi'a sun nunawa duniya cewa su musulmuƙa ne saboda taya zaka raira waka a lokacin bukin sallar addinin da baka so a duniya ko baka tare da su.
a so da kauna ga mutum yana nuna kana sonsa dari bisa dari.
Saboda daman a lokacin da shugabansu zazakky ya sha ruwan harsashe, shuganan can yaje na jajanta mishi da jama'arsa sai yake cewa daman su da su dan jumma ne da dan jummai to gashi abun ya fito a fili.
Sai ku saukar da wannan video domin kallon suna rera wannam wakar a cikin coci ranar kirsimati.
Click here to download the video

Wata Yar Film Tace Malama Addini Ma KwaiKwayensu Suke,Ko Zaku Iya Yarda Da Maganarta?

Ibrahim Auwal | December 31, 2017 | 0 Comments

Wata sabuwar jarumar Kannywood da wasu masu fashin baki ke cewa ta shigo masana’antar da kafar dama tayi ikirarin cewa malaman addini suna samun salon yadda za su yi wa’azin su ne daga fina – finan hausa.
Rashida Lobbo dai tana daya daga cikin jaruman da suka karbi kyauta a bikin karama jaruman fim da mujalar city people ta shirya kwanakin baya a jihar Lagos.
Rashida Lobbo wacce ake wa lakabi da yar Yola tana cikin sabbin jarumai da tauraronsu ke haskawa kuma da alama ta shirya damawa da sauran fitattun jarumai dake masana’antar cikin shekarar 2018 da zamu shiga.
Kamar yadda ta bayyana a shafin ta na sada zumunta na facebook, jarumar tana karkashin kamfanin shirya fina-fina na FKD wato mallakar shahararen jarumi, Ali Nuhu.
# Arewamobile.

Domin Yin Apply Na Nigerian Army Na Wannan Shekarar SaikU Shiga nan ku karanta Yanda Ake Apply

Ibrahim Auwal | December 30, 2017 | 0 Comments

Rundunar Sojin Kasa na Najeriya ta fara rajisatar daukan sabbin mutane masu sha'awar shiga aikin karo na 77 a ranar Juma'a 29 ga watan Disambar 2017 kuma za'a dakatar da yin rajisatar ne a ranar Juma'a 9 ga watan Febrairu na 2018.
Sanarwan da ta fito daga Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Brigediya Janar Sani Usman ya ce rundunar tana bukatar matasa maza da mata daga duka jihohin Najeriya masu shekaru 18 zuwa 22 ko kuma masu shekaru 22 zuwa 26 ga fanin masu koyan sana'o'i.
Rundunar Sojin Kasa na Najeriya ta fara rajistar daukan sabbin ma'aikata

Masu sha'awar rajisatar sai su ziyarci shafin intanet na hukumar a http://recruitment.army.mil.ng domin cike bayannan da ake bukata. Ana kuma iya kiran wadannan lamabobin wayar domin tambaya ko neman karin bayani; 08038575725 / 08037234828.
Har ila yau, Ana iya samun karin bayani daga jaridun Daily Sun da kuma Leadership bugun gobe Lahadi 31 ga watan Disamba na 2017. Ku sani cewa rajisatar kyauta ne.

Jama'a Mu Tashi Mui Karatu-Wani Yace Ya Gano Wani Kauye Da Manzon Allah s.a.w yai Bauta Acikinsa A Jahar Katsina.

Ibrahim Auwal | December 29, 2017 | 0 Comments
Ku kalla yanda rahoton yazo,yakamata ace mutashi mudinga karatu saboda kada wani makaryace ya saka mu a kwali.

WATA SABUWA!!!
********************
MANZON ALLAH (S.A.W) YA ZO WANI KAUYE A CIKIN JIHAR KATSINA.
********************
YANZU HAKA, DUBUN DUBATAR JAMA'A NA TA TURURUWA DON GANI DA IDO DA NEMAN TABARRUKI.
********************
An gano inda Manzon Allah (S.A.W) ya yi Bauta a Karamar Hukumar Matazu ta jihar Katsina.
********************
A Karamar Hukumar Matazu da ke jihar Katsina, a wani Kauye da ake kira "KOGARI" wani bawan Allah mai suna ASHIRU da ke zaune a GIDAN DAMO, ya gano wurin da Manzon Allah (S.A.W) ya yi Sallah kuma ya Kwanta.
********************
Yanzu haka, maza da mata, da tsofaffi, da matasa, da matan aure sun cika wurin dankam, abin sai wanda ya je ya gani, Dubban Mutane ne ke ta yin tururuwa har daga wasu jihohi.
********************
A yanzu haka, domin ganin wannan abin mamaki da neman TABARRUKI, kuma yanzu haka, akwai wata mata da ta haihu a wajen, ana yin Sujjada a kuma rungumi wajen.
********************
Itacen wajen duk an kwakule su ana cinyewa domin neman TABARRUKI, sannan akwai ruwa a wajen mutane na zuwa da robobi da butoci domin samun ruwan, ana nuna inda MANZON ALLAH (S.A.W) ya yi SALLAH da inda ya KWANTA.
Ana zuwa wurin ayi Sujada da Zikiri, da sauran abubuwa na nau'in bautar Allah (S.W.T) domin neman tabarruki.
********************
JAMA'A MASANA TARIHIN MANZON ALLAH (S.A.W) YA YA KU KE GANIN WANNAN AL'AMARI???

Musha Dariya-Ali Artwork Tare Da Kwankwaso

Ibrahim Auwal | December 26, 2017 | 0 Comments

kamar yanda muka sani ali arwork yana nishadantar da mutane da kyawawan bidiyoyin bandariya to yau ma ga wani comedy nashi maidadi,domin saukarwa kan wayarku saiku danna download dake kasa.
click here to download

Ni Ba Mata Aure Bace Amma Kuma Ni Ba Budurwa Bace-Inji Rahama Sadau

Ibrahim Auwal | December 26, 2017 | 0 Comments
Rahotanni sun kawo cewa korarriyar jarumar kamfanin shirya fina-fina hausa na Kannywood,

Rahama Sadau ta bai wa masoyanta damar yi mata tambaya a shafinta na twitter.
Wannan dama da jarumar ta bayar ya sa masoya na ta tururuwa wajen yi mata wasu tambayoyi da suka shafi rayuwarta.
Duk da cewa wasu daga cikin tambayoyin sun kasance masu nauyi jarumar tayi kokarin baar da amshoshin day a gamsar da masu yin tambayar ba tare da ta nuna dacin rai kan tambayar ba.
Ni ba cikakkiyar budurwa ba ce amma ban taba aure ba – Rahama Sadau
Shafin al’ummata ta wallafa tambayoyin da akayi wa jarumar da amshoshin da ta bayar kamar haka:
An tambayi jaruma Rahama ko ita budurwa ce gangariya:
Ga amsar da ta bayar “Ni budurwace, amma ba budurwa fil a leda ba, domin na rasa budurcina.”
An tambayeta wanda ya koyamata rawa?
Ta amsa cewa “Ali Nuhu.”
Me ta fi jin tsoro a duniya?
Ta ce “mutuwa.”
Yaushe za ta yi aure?
Ta ce “kwanannan,” amma bata bayyana ko wanene saurayin nata ba.
Shin za ta iya daina fim?
Ta ce “a’a.”
Dan wasan da ya fi birgeta a masana’antar fina-finan Hausa
Ta ce “Sadiq Sani Sadiq.”
Fim din da ta yi wanda ta fi so, ya fi birgeta
Ta ce fim din turanci na “Sons of the Caliphate”
An tambayeta ko shekarunta nawa?
Ta ce, “24.

Yanda Ake Redirect Na Blogger Zuwa Waniii Site Ko Wani Bloggg Cikin Sauki

Ibrahim Auwal | December 26, 2017 | 1Comments

Insha Allah yau zamuyi bayani akan yadda ake redirect na blog zuwa wani website ko wani url dai na daban.
Note:kada kai anfani da wannan dama wajen cutar da wani kamasa redirect a site dinsa zuwa naka,wannan post anyi shine dan ilimi badan cutarwa ba.
Kamar dai yanda kowa ya sani zai iya yiwuwa nai create na sabon website dina a wp bayan na gaji da aiki da kanfanin blogger,to wannan itace hanyar da zaka bi duk wanda ya ziyarci blogger dinka sai ta kaishi zuwa sabon wordpress naka cikin sauki.
Nazo mana da sassaukar hanya guda daya duk da cewa hanyoyin suna da yawa amma naga kamar wannan zati fi sauki.
YANDA AKEYI
na dauka hanyar da ake kira da refresh wadda take kamar haka.
Dafarko zakai login zuwa tsohon blog naka sai kaje head na blog din,a blogger zaka iya danna cntrl f sai kai search na <head>........</head>
ka tabbata kasa code din da zamu baka a cikin tsakin wadannan head tags din.
Code din shine kamar haka.

bayanin yadda zakai anfani dashi,idanka kula zakaga agaban kalmar content akwai alamar 0 to wannan shine seconds nawa kake so yayi kafin yai redirect zuwa sabon shafin,kaga tunda kasa 0 bazai ma bude tsohon blog din ba kawai direct sabon zai kaika,idan kuma kasa 2 a wurin to zai yi seconds biyu a tsohon shafin sai yai redirect naka zuwa sabon shafin haka dai abun yake idan kasa 10 secons goma.Sai kuma wurin dakaga nasa arewanow.com.ng sai kayi substite dinsa da blog din ko shafin dakake so ya ringa kai maziyarta tsohon blogger dinka.
Daga Ibrahim Auwal Ishaq.

"Ki daina saka fenti a fuskarki yana rage miki kyau" wani ya gayawa Maryam Gidado

Ibrahim Auwal | December 24, 2017 | 0 Comments

Bayan data saka wannan hoton a dandalinta na sada zumunta da muhawara, Jarumar fim din Hausa Maryam Gidado ta samu wani daga cikin masoyanta da yayi kira a gareta data daina saka wannan fentin a fuskarta, kamar yanda ya kira kwalliyar ta Maryam, mmutumin yace fentin yana ragemata kyau, kuma idan bata sakashiba tafi yin kyau.

Kimiya:Yanda Ake Hada Dan Karamin Jirgi Mai Tashi Sama Da Robar Lemon-Kwalba

Ibrahim Auwal | December 24, 2017 | 0 Comments

Kamar yanda muka sani kimiya ta maida komai mai yiwuwa a wannan zamani,kimiya zata iya yin duk wani abu da da tsafi ne kawai zai iya yinsu,tashin jirgi zuwa sararin samaniya shine fasaha ta farko da ta fi burge dan Adam kuma kowa yake ganin ita tafi kowacce fasaha.
Saboda haka ne ma yau shafin www.arewanow.com.ng ya kawo muku hanyar da zaku hada dan karamin jirginsama acikin gidajenku ta hanyar anfani da roba ko kuma nace gorar lemon kwalban da kuke siya.
Zamuyi anfani da robar sprite dan naga cewa zata fi dacewa sauran abubuwan da ake bukata sune:
1.irin ta cikin rediyo dinnan.
2.waya ta wiring yar karama.
3.sai kuma battery.
4.da dan karamar roba wadda zamuyi anfani da ita a matsayin fanka ko kuma nace propellar.
Kafin kafara wannan aiki katabbata cewa bakayi anfani da abubuwa masu nauyi ba,saboda inkai anfani da masu nauyi jirginka bazai tashi ba.
Ku danna wannan rubutun dake kasa dan saukar da bidiyon dayai bayani akan haka sosai.
click here to download the video

Sabon Bidiyon Fati Washa

Ibrahim Auwal | December 22, 2017 | 0 Comments

wannan sabon bidiyo ne na babbahr jaruma wadda aka fi saninta da fattywasha,bidiyon ya kasance hira da akayi da ita a gidan tv,domin yin download sai ku danna rubutun dake kasa.

Hotunan Da Suka Nuna Cewa Fati Washa Tafi Kowacce Mace Kyau Acikin Matan Kannywood

Ibrahim Auwal | December 21, 2017 | 0 Comments

Jaruma Fati washa A yanzu Haka Ana tunanin tafi kowace mace kyau a masana'antar Kannywood Shin Kun yarda da wannan hasashe kokuwa kunada naku ra'ayin???


Adam A. Zango ya bayyana ranar da Dabon fim din Sa Na 'Gwaska In Return' zai fito

Ibrahim Auwal | December 21, 2017 | 0 Comments
Shahararren fim din da aka dade ana jira ya fito na Hausa wanda fitaccen jarumin nan ya fitar mai suna 'Gwaska an shirya fara nuna shi a gidan kallo a ranar 1 ga watan Janairu na shekara mai kamawa ta 2018.
A ranar dai mashiryin shirin da kuma ya taka muhimmiyar rawa a ciki tare da bayar da umurni, Adam A. Zango ya bayyana cewa tabbas fim din zai kayatar sosai domin kuwa sabon fim din mai suna 'The Return of Gwaska' ya banbanta da sauran wadan da suka fita kasuwa a baya.
Dandalin Kannywood: Adam A. Zango ya sha alwashin kayatar da masoyan sa a sabon fim din Gwaska

NAIJ.com haka zalika ta samu cewa fitaccen jarumin har ila yau ya kuma bayyana cewa dalilin da yasa har yanzu fim din bai fita ba shine domin a ba dukkan masu ruwa da tsaki a harkar damar kallon fim din tare da yi mashi dukkan gyare-gyaren da suka kamata.
Fitattun yan fim din da suka taka rawa a cikin fim din dai sun hada ne da Adam A. Zango din kansa, sai Bello Muhammad da kuma Lilisco da dai sauran su.

Kannywood Sun Ce Ba Zasu Yafewa Rahama Sadau Ba...ko meyasa?

Ibrahim Auwal | December 21, 2017 | 0 Comments

Mujallar Fim Magazine da ta fito wannan makon ta buga wani labari dake cewa kungiyar kula da finafinan Hausa a kano MOPPAN tace bazata yafewa korarriyar jaruma Rahama Sadau laifin datayi ba a baya duk da cewa jarumar ta aike da takardar neman afuwa kuma ta fito ta gayawa Duniya cewa tayi nadamar abinda ta aikata.
Ali Nuhi ne ya yiwa Rahamar jagora zuwa gurin masu fada aji a harkar finafinan Hausa a Kano inda ta nemi Afuwa kuma ta rubuta takarda a hukumace ta neman Afuwa.
Mujallar ta Fim Magazine dai a satin daya gabata ta kwarmato cewa anyi shirin yin zama ranar laraba dan tattauna batun yafewa Rahamar laifinta ta dawo taci gaba da yin finafinan Hausa amma sai dalilin ciwon idon da Kabiru Maikaba, daya daga cikin jigon kungiyar yake fama dashi aka daga zaman zuwa ranar Asabar.
Asabar tazo ta wuce bamuji komai ba sai gashi yau labari ya fito an fasa yafewa jarumar.
Saidai abinda ke daurewa mutane kai shine Rahama Sadau kwanannan ta shirya wani fim din Hausa da kanta me suna Rariya wanda har ya samu kyautar fim din da yayi fice a wannan shekarar, to wai ko korar da akawa Rahamar iya garin Kanone kawai.

Rikici Ya Kara Barkewa A Jam'iya PDP

Ibrahim Auwal | December 20, 2017 | 0 Comments

- Baka raba PDP da takaddama da rikici
- Magagin faduwa zabe ne har yau bai sake ta ba?
- PDP ta lashi takobin dawowa mulki a 2019
Wani rikici ya barke a PDP
Ana ta samun baraka tun bayan da jam'iyyar ta PDP ta yi taron ta da zabuka na kasa, inda ake ta cece-kuce kan rikicin cikin gida na jam'iyyar, wasu har sun garzaya kotu.
To yanzu ma dai, rikici ne wanda Mista Emanuel Nwosu yake jagoranta, kan sai lallai an soke tare da sake zaukan da aka yi don cewa an tafka kura kurai da magudi.
Tun faduwar jam'iyyar zabe a 2015 take ta shiga halin ha'u'la'i da ma zarge zarge na tafka satar kudaden gwamnati kan mutanen ta da jami'ai.
Ya zuwa yanzu dai, jam'iyyar ta PDP bata sami nutsuwar da har zata iya wani katabus ba a zabuka masu zuwa.

Wai Rahama Sadau Ta Dawo Kannywood Ne?

Ibrahim Auwal | December 20, 2017 | 0 Comments
Da alama dai fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar
Kannywood wadda aka kora a da watau
Rahma Sadau ta shirya tarar rigima
bayan da tayi fatali da dukkan korar da
akayi mata sannan ta shirya sannan ta
kuma fito a matsayin jaruma a wani
sabon fim mai suna 'Dan Iya.'


Fim din dai kamar yadda muka samu
daga majiyar mu an shiyar kammala
shi sannan a kuma sake shi zuwa
kasuwa a watan Maris din shekara
mai zuwa ta 2018 sannan kuma
fitaccen mai bayar da umurnin nan
watau Yaseen Auwal ne ya bayar da
umurnin fim din.
NAIJ.com dai ta samu cewa fim din na
barkwanci ne kuma an shirya shi a
wani kauye ne da yake nuna rayuwar
manyan jarumai Rahma Sadau da
kuma Sadiq Sani Sadiq wanda shine
ya fito a matsayin dan iya din.
Sauran wadanda suka taka rawa a
shirin fim din sun hada da Rabi'u
Rikadawa, da kuma Aminu Sheriff
Momoh.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a
ranar 3 ga watan Oktobar bara ne dai
kungiyar masu shirya-fina-finan
Hausa shiyyar jihar Kano ta dakatar
da jarumar sakamakon wata waka da
tayi da ta sabawa addini da kuma
al'adar mutane

Meyesa Ake Faduwaaa Jarabawa A Nigeria Da Yanda Za A Magance Matsalar.

Ibrahim Auwal | December 20, 2017 | 0 Comments

Gwamnan jihar Kaduna a Najeriya Nasir el-Rufai, mutum ne da ake ganin a matsayin mai yawan kawo batu mai cike da ce-ce-ku-ce.
A lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Bankin Duniya kwanan nan, ya bayyana cewa sakamakon jarabawar da aka yi wa malaman firamare na jihar ya yi matukar ba da mamaki da takaici.
An yi musu jarabawar 'yan aji hudu ta 'yan shekara 10.
Kuma sai malaman sun ci a kalla kashi 75 cikin 100, in ji gwamnan.
Ya kara da cewa, "Amma abin bakin-cikin shi ne yadda kashi 66 bisa 100 na malaman suka fadi jarabawar warwas."
Ya yi zargin an bai wa malaman da ba su cancanta ba aiki, kuma ya yi alkawarin kawo karshen matsalar.
Sai dai sakataren kungiyar gwamnatin jihar Adamu Ango, ya musanta ikirarin gwamnan, ya kuma ce duk farfagandar kafafen yada labarai ce kawai.
Abin mamakin shi ne yadda malaman jihar suka nuna rashin jin dadinsu kan lamarin, musamman ma jarrabawar da aka yi musu a jere, inda suka ce wannan ne karo na uku da aka yi musu jarrabawar a bana.
Malaman sun ce da kamata ya yi a bayyana sakamakon sauran jarrabawar da suka yi in dai har gwamnan zai yi adalci.
Sun kuma ce har yanzu gwamnan bai biya su alawus-alawus din su ba na tsawon shekara biyu ba?
Har ila yau akwai matsalar ajujuwan karatu.
Wata rana wani abokina malamain makaranta ya gayyaceni mkarantar da yake koyar wa inda na ga ko wanne aji dauke da kusan dalibai 90 zuwa sama da 120.
Ko da yake yawancin malaman na shan fama wajen tafiyar da wadanann ajujuwa, inda yawancin yaran ma sun fi son zama a kasa, wasu suna wasa ko wannan ya tsokani wannan yadda karatun ma ba zai yiyu ba.
Shugabanni sun fi mayar a hankali wajen bayar da kwangilar gina ajujuwa da za a rika hango su daga waje, fiye da horar da su da kuma zaburar da su a kan aikinsu.
"Cibiyoyin da ake biyan kudi a ci jarrabawa"
Makarantu da dama sun fi mayar da hankali kan dalibai su samu sakamako mai kyau, amma a zahiri ba su san komai ba.
Har ila yau hakan ya sake kawo karuwar abin da ake kira "cibiyoyin da ake biyan kudi a ci jarabawa". Duk wanda ya je irin wadannan makarantu ko cibiyoyi yana da tabbacin samun kyakkyawan sakamako idan ya biya kudi.
*. Nigeria: Malamai sun fadi jarrabawar 'yan aji hudu a Kaduna
*. Buhari ya caccaki gwamnoni kan albashi
Wani da yake koyarwa a makarantar gwamnati ya shaida min cewa, yana alfahari da irin wannan makarantu, domin ya ga dalibai da dama da suka shafe shekara 12 a makaranta, amma ba za su iya kwafar amsar tambayoyin da malamai suka rubuta musu a kan allo ba.
Wannan ya nuna dalilin da ya sa ba ya ga jarrabawar da ake yi ta kasa, jami'o'i da sauran kwalejin ilimi ke shirya wata jarrabawar ta musamman kafin su dauki dalibai.
Irin wadannan manyan makarantu sun tsaya kai da fata a kan sai sun sake shirya jarabawa ta kashin kansu don tabbatar da makin da ko wanne dalibi ya samu ba na bogi ba ne.
Daukar aiki ya zama abin takaici a wurin masu daukar ma'aikata wadanda suke cin karo da daliban da suka hada digiri amma da wuya su iya hada kwararan jumloli biyar.
Irin wadannan matsalolin da ake fuskanta a makarantu musamman na gwamnati ne yasa iyaye suka gwammace su zuba kudinsu su kai 'yayansu makarantu masu zaman kansu.
Dadin-dadawa kuma, 'yan Najeriya na tunkaho da makarantun da 'ya'yansu suke zuwa.
Amma sakamakon yawan yajin aikin da jami'o'i suke yi ya sa dalibai ba su da tabbas na lokacin kammala karatunsu, duk da cewa tun da fari an tsara lokacin kammala karatun.
Wannan yana matukar tayawar wa dalibai hankali musamman wadanda ba su da halin zuwa kasashen ketare yin karatu.
Wadanda ba za su iya biyan kudin karatu da sauran kudaden da ake kashewa a Amurka ba, ko kasashen Turai ko Asiya suna zuwa kasashen da ke makwabtaka da su, kamar su Jamhuriyar Benin da Ghana da Uganda da sauran kasashen Afirka.
A takaice dai 'yan Najeriya na dokin kashe kudinsu a wasu daga cikin jami'o'i masu zaman kansu a Ghana, da Benin da Nijar don samun damar yin karatu a can.
Sai dai kadan daga cikin 'yan Najeriyar ne suke iya biyan kudin makarantu masu zaman kansu da jami'o'i.
Duka dai, yawancin 'yan Najeriyar sun amince cewa akwai kalubale da dama da ake fuskanta a bangaren ilimi, ko da yake babu wata yarjejeniya da aka cimma a kan dalilin hakan da kuma hanyar da za a bi a magance matsalar.
Kalaman da gwamnan Kaduna ya yi za su iya jan hankali, sai dai ba lallai ne hakan ya inganta kwazon malaman ba.

Shin Ana Lalata Da Yan Matan Kannywood?

Ibrahim Auwal | December 19, 2017 | 0 Comments
Tun bayan da badakalar yin lalata da mata 'yan fim din Amurka, wacce ta shafi fitaccen mai shirya fina-finan Hollywood, Harvey Weinstein, ta bayyana bangarorin fina-finai daban-daban na duniya ke aza alamar tambaya: shin ana samun irin wannan batu a bangarorinsu?
Fitattun jarumai mata irinsu Ashley Judd da Angelina Jolie da kuma Gwyneth Paltrow sun zargi Mr Weinstein da yin lalata da su kafin ya sanya su a cikin fina-finansa.
Jarumai mata fiye da 40 ne suka fito fili suka bayyana cewa fitaccen mai shirya fina-finai yi lalata da su tun bayan da jaridar The New York Times ta soma kwarmata batun ranar biyar ga watan Oktoba.
Sai dai Mr Harvey, wanda da farko ya musanta zargin, ya ce ya yi lalatar da su ne tare da amincewarsu.
Tuni dai 'yan sandan birnin New York da London suka soma gudanar da bincike kan lamarin.
Me ake ciki a Kannywood?
An dade ana yi wa masu yin fina-finan Kannywood kallo a matsayin mutanen da ke bata tarbiyar al'umma.
Kazalika ana yi musu duba na mutanen da ke aikata masha'a kamar zinace-zinace da yin luwadi da sauransu.
Sai dai sun sha musanta wannan zargi.
A shekarun baya, wani bidiyo da ya bayyana na wata tsohuwar 'yar fim inda wani ke lalata da ita, ya jawo wa 'yan Kannywood matukar bakin jini, lamarin da ya sa gwamnatin Kano ta wancan lokaci ta haramta yin fim a jihar.
Hukumar da ke tace fina-finai ta lokacin ta matsawa masu yin fim abin da ya kai ga durkushewar kusan daukacin masu harkar fim.
Daga baya dai al'amura sun daidaita, kuma ko da yake babu wata 'yar fim da ta fito fili ta ce wani furodusa ko kuma babba da ke cikin harkar ya taba neman yin lalata da ita, rahotanni da dama na cewa hakan na faruwa.

Sai dai rahotannin sun nuna cewa mata 'yan fim na jin tsoron fitowa fili su fadi abin da ke cikinsu game da zargin yi musu lalata ne saboda, a Musulince, irin wannan zargi na bukatar kwakkwarar shaida kafin a amince da shi.
Wata fitacciyar jaruma ta taba shaida min cewa manyan masu ruwa da tsaki da dama sun nemi yin lalata da ita amma ta ki yarda.
Jarumar, wacce ba ta so na ambaci sunanta, ta shaida min cewa "Wallahi mutanen da nake gani da mutunci a harkar Kannywood ba su da yawa domin kusan kowa ka ce kana son shiga fim dinsa sai ya nemi ya yi lalata da kai".
Ta kara da cewa Jarumi Ali Nuhu ne kawai bai taba nuna son yin lalata da ita ba.
Daya daga cikin jaruman mata, Hauwa Waraka, ta shaida wa BBC cewa ko da yake babu wani da ya taba bukatar ta yi lalata da shi kafin ya saka ta a fim dinsa, ba za ta kawar da yiwuwar cewa hakan na faruwa ba.
"Ni dai babu wanda ya taba bukatar na yi lalata da shi kuma ban san wata da ta ce wani ya taba son yin lalata da ita ba. Sai dai ka san wannan harkar kowa da halinsa ya zo, babu wanda za ka bayar da shaida a kansa".
Ta kara da cewa: "Su matan da suke indostri din ai ba yara ba ne, ba yadda za a yi a ce za a kama a neme su da karfi, dole sai sun yarda, don haka duk abin da ki ka ga an yi a harkar nan mutum shi ya so."
Saurari jawabin Hauwa ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke kan hotonta:
Da alama wannan batu nata na da alamun gaskiya saboda wani darakta ya shaida min cewa irin badakalar da ke faruwa a Kannywood ta sa "nake janye jikina daga cikinta."
Sai dai da BBC ta tuntubi Ali Nuhu kan wannan batu ya musanta faruwar hakan, yana mai cewa a duk shekarun da ya kwashe cikin harkokin fim din Kannywood bai taba ganin wacce ta ce an yi lalata da ita ba.
"Ni gaskiya ba taba samun wacce ta ce an yi lalata da ita kafin a sa ta a fim ba, kuma ina ganin wannan zargi ba gaskiya ba ne domin kuwa mu muna kokarin kare addini da al'adunmu ne. Akwai kwamiti da ke sanya ido kan masu neman yin lalata da 'yan fim da ma kula da yadda muke harkokinmu".
Saurari jawabin Ali ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke kan hotonsa:
Shi ma fitaccen daraktan fina-finan na Kannywood, Mallam Aminu Saira ya shaida BBC a kwanakin baya cewa bai taba neman yin lalata da mace kafin ya sanya ta a fim dinsa ba.
A cewarsa, "Wannan batu ba gaskiya ba ne; hasalima wanna ne karo na farko da aka yi min irin wannan tambayar kuma ina gani da a ce ana samun irin wannan lalata da 'yan matan fim da suka gabata sun yi korafi. kar ka manta wasu 'yan fim mata sun yi aure. Da a ce haka batun yake da idan wasu sun yi shiru, wasu sai sun yi magana".
Saurari jawabin Aminu Saira ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke kan hotonsa:
Da alama dai zarge-zargen yin lalata da kuma bata tarbiya za su ci gaba da mamaye harkokin fina-finai, ba kawai na Kannywood ba, har da na Nollywood da Bollywood da sauransu saboda yadda wadannan bangarori suka zama tamkar hatsin-bara

Izala Ta Nemi APC Ta Cika Alkawuran Da Ta Dauka A 2015

Ibrahim Auwal | December 19, 2017 | 0 Comments

- Kungiyar Izala ta nemi APC ta cika alkawarin ta ga ‘Yan Najeriya
- Shugaban Majalisar Malamai ne yayi wannan jawabi kwanan nan
- Sheikh Jingir ya tunawa Shugaba Buhari da alkwarin da yayi a 2015
Kungiyar Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ta Kasa ta nemi Gwamnatin APC ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta cika alkawarin da tayi wa Jama’a. Malamin yace Talakawa da kan su su ka rika kokarin ganin Buhari ya samu mulki.
Kungiyar Musulunci ta yi kira ga Buhari da babban murya
Kungiyar ta tunawa APC da alkawarun da ta yi wa ‘Yan Najeriya lokacin yakin neman zabe a 2015. Jaridar Dily Tryust tace Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar addinin Sheikh Sani Yahaya Jingir ne yayi wannan kira a Garin Jos.

Babban Malamin yayi wannan jawabi ne wajen wani taron dalibai a wata kwalejin kiwon lafiya a jiya. Jingir ya tunatar da Gwamnatin Muhammadu Buhari irin alkawarin da ta dauka na gyara harkar ilmi, noma, da ma gyara hanyoyi a Najeriya.
Bayan nan APC tayi alkawarin kawo karshen rashin aikin yi har da ba masu zaman kawai N5000 duk wata. Malamin ya yabawa yakin Shugaba Buhari na kawo karshen ta’addanci da sata amma akwai sauran aiki wajen habaka tattalin kasar.

Kungiyar Mata Yan Film Ta Tarwatse

HAUSA NOVELS MASTER | December 19, 2017 | 0 Comments

A'AYIN MUJALLAR FIM A MUJALLAR Fim ta watan Satumba, 2017, kun karanta yadda mata ’yan fim da su ka yi aure su ka yi wani k'warya-k'waryan taron sada zumunta a birnin Kano. Akwai k'ungiya wadda su ka kafa a baya wadda manufar ta ta farko ita ce sada zumunta, sai kuma k'udirin taimakon kai da kai ya biyo baya, da sauran su. Duk wanda ya karanta manufofin k'ungiyar, to ya san cewa abu ne mai kyau. Ya yi daidai da hob'b'asan da ake yi a sauran sassa na jama’a, inda wani ko wasu ke tashi tsaye su kafa wata k'ungiya mai zaman kan ta domin su taimaki ’yan’uwan su marasa galihu. A Turance, ana kiran irin wannan k'ungiya Non-Governmental Organisation (NGO), wato k'ungiyar da ba ta gwamnati ba, da nufin cewar ba sai mutum ya dogara da gwamnati ba wajen yi wa al’umma aiki. Mansurah Isah da Wasila Isma’il ne k'ashin bayan kafa wannan k'ungiya ta ’yan fim mata. Da farko, matan aure ne kad'ai a cikin ta, to amma saboda wasu daga cikin su auren su ya mutu daga baya, ta yadda ba za a iya cewa su fita ba, sai k'ungiyar ta had'o har da zawarawa ’yan fim. Sun lura da cewa wasu ba su da halin taimakon kan su idan wata larura ta taso masu, kamar yadda ya faru ga Fati Sulaiman a bara, inda aka tara kud'i domin yi mata aikin cire mahaifa. Su ’yan fim d'in su ne ke had'a kud'i - tare da neman agaji daga wasu ’yan fim d'in, misali maza, da ma mutanen da ba ’yan fim ba - don had'a abin taimakon da ya kamata. Kada mu manta, da man akwai irin wasu k'ungiyoyin agaji wad'anda wad'ansu ’yan fim su ka kafa wad'anda manufar su ta bambanta da wannan. Su, agaji su ke kaiwa ga mutanen da ba ’yan fim ba, kamar majinyata ko fursunoni da sauran su. Misali, Hadiza Gabon, Nafisa Abdullahi, da ita kan ta Mansurah, duk su na da irin wad'annan k'ungiyoyin. To amma a ce k'ungiyar da ta sadaukar da kan ta ga taimakon mata ’yan fim, sai ita wannan mai suna Kannywood Females Foundation. Tunani ne mai kyau wanda ya nuna cewa ciwon ’ya mace na mace ne, kuma tilas ne mata ’yan fim su tashi tsaye su taimaka wa kan su kafin su yi tsammanin taimako daga wajen wani can daban. Kwatsam, sai labari ya b'ulla cewa an samu b'araka a a k'ungiyar, wai su Saima Mohammed Raga sun ware sun kafa wata k'ungiyar, wato Kannywood Celebrities Foundation. Ita ma tasu k'ungiyar manufar ta iri d'aya ce da waccan ta farkon. Ko sunan su ma iri d'aya ne in ban da bambancin kalma d'aya da aka samu. Abin mamaki shi ne ba fad'a aka yi ba da ya janyo wannan a-raba d'in. Saboda haka dai akwai wata manufa a k'asa. Kamar yadda Mansurah ta yi zargi, kila dai an kafa k'ungiyar ne saboda abu biyu: neman shugabanci da kuma hangen samun kud'i. Abin bak'in ciki ne a ce an samu wannan babbar b'araka tun yanzu, a daidai lokacin da ake k'ok'arin gina k'ungiyar. Duk da yake Saima ta ce wai k'ungiyar su ba kishiyar d'ayar ba ce, a gaskiya ba haka ba ne; da gaske kishiya ce. Haka kuma an haifar da matsananciyar gaba a tsakanin ’yan fim mata masu aure da kuma zawarawa. Yanzu an nuna cewa akwai gida biyu masu adawa da juna, maimakon su kasance tsintsiya mad'aurin ki d'aya. Mu na bada shawara ga wad'annan mata da su daure su sake lale, su koma su had'e k'ungiya guda d'aya. A samu maslaha. Rarrabuwar su ba za ta haifar da d'a mai ido ba, sai ma b'acin rai. In da hali, maza shugabanni a harkar fim su shigo ciki domin su ba su shawara. A gano menene dalilin su Saima na warewa, a ba su hak'uri. Idan batun shugabanci ne, a yi zab'e na gaskiya, duk mai son rik'e muk'ami, ta yi takara. Kuma ya kamata su masu aure a cikin su, irin su Maryam Mashahama da su ka shiga cikin rigimar, su kiyaye shiga cikin rud'ani ko wani abu da zai jawo masu surutu a gari. Su tuna cewa a k'ark'ashin mazajen su su ke; shiga hatsaniya ba tasu ba ce. Su yi wa kan su fad'a, su ja girman su.

Korar Ma’aikata:Sanata Shehu Sani Kaduna ya kara caccakar Gwamna El-Rufai

HAUSA NOVELS MASTER | December 19, 2017 | 0 Comments

- Sanata Shehu Sani ya caccaki Gwamnan Kaduna El-Rufai
- Shehu Sani yace giyar mulki ke daukar Gwamnan Jihar
- Sanatan na tsakiya yace Gwamnan ba zai koma ba a 2019
Mun samu labari cewa Sanatan tsakiyar Kaduna Kwamared Shehu Sani ya kara caccakar Gwamna Nasir El-Rufai. An dai dade ana ‘yar tsama tsakanin Gwamnan Jihar da kuma Sanatan Jihar. Sanatan yace Gwamnan ba zai koma kujerar sa ba a 2019.
Sanata Shehu Sani ya soki Gwamna El-Rufai
Sanata Shehu Sani a shafin sa na Facebook ya bayyana cewa an gama yin sak ko kuma a daga hannun wani ‘Dan siyasa a Jihar Kaduna. Sanatan ya koka da rashin adalcin da ake yi na korar Ma’aikata a Jihar ya kuma sha alwashin cewa za su koma bakin aikin su.
ArewaNow. Ta samu cewa
Shehu Sani ya nemi Musulmai da Kiristocin Jihar su dage da addu’a wajen ganin an tika Gwamnan da kasa a zabe mai zuwa. Sani ya kuma kira Jama’a da su rika bibiyar katin zaben su a kai-a kai. Sanatan yace abin da kowa ya shuka shi zai girba watau a zaben 2019.
Kwamared yace Talakawan Jihar za su maida martani na sallamar su daga aiki da aka rika yi a karkashin Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai. Sanatan yace giyan mulki ne ke daukar Gwamnan.

An Kara Samun Wata Amarya Ta Yi Yunkurin Sheke Mijinta

HAUSA NOVELS MASTER | December 18, 2017 | 0 Comments

A ranar Asabar din da ta gabata ne wata sabuwar amarya da duka-duka aurenta makonni uku kacal ta kaiwa mijinta hari da sabuwar reza ta kuma raunata shi matuka
Amaryar da aka bayyana sunanta da Shafa Muhammad ‘yar shekaru 28 da haihuwa ta aikata wannan aika-aika ne a unguwar Arkillar Liman, cikin karamar hukumar Wamakko, jihar Sokoto
Majiyarmu ta gano cewa, Shafa ba ta son mijin da aka aura mata mai suna Umar Shehu a saboda haka ne ma tun da aka yi auren ta ke ajiye reza kusa da gadon kwananta ita da mijinta
Kwatsam kuwa sai a daren Asabar, 16 ga watan Disamba, 2017, makonni uku daidai da kaita daki, mijinta, Umar ya nemi da ya tara da mai dakinsa lamarin da ya sanya ta dauki rezarta ta yi ta yanyanka masa akansa da goshinsa
Kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar Sokoto, ASP Ibrahim Abarass ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce “Tuni aka kai Umar asibiti, kuma ya samu kulawa ta gaggawa kuma yana samun sauki bayan an sallamo daga asibiti”
“Ita kuwa Shafa, tana kulle a wajen ‘yan sanda kuma za a gurfanar da ita a gaban kulaya da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike” inji Abarass
Abarass ya shawarci iyaye da su guji yi wa ‘ya’yansu auren dole.

Rahama Sadau Tasha Da Kyar Daga Wasu Daliban Jami'a

HAUSA NOVELS MASTER | December 18, 2017 | 0 Comments

Rahama Sadau, Jarumar wasan Hausa, ta sha da kyar a hannun dalibai masoyanta
- Lamarin ya faru ne a jami'ar Umaru Musa dake Jihar Katsina
- Jami'an tsaron jami'ar sun yi nasarar tserar da ita ba tare da samun lahani ba
Rahama Sadau, Shahararriyar jarumar wasan Hausa, ta sha da kyar a hannun wasu masoyanta, daliban jami'ar Umaru Musa dake jihar Katsina.
Tun farko shugabannin kungiyar daliban jami'ar ne suka gayyaci jarumar domin karramata a bikin ranar Mata ta duniya. Saidai lamarin ya kwacube bayan isowar jarumar harabar taron, Students Centre, dake cikin jami'ar.
Majiyar mu ta bayyana mana cewar jarumar ta iso wurin taron a makare, kuma zamanta keda wuya a teburin manyan baki sai dalibai suka barke da sowa da murnar ganin ta. Dalibai da dama sun nufi jarumar domin samun damar daukan hoto tare da ita, lamarin da ya kai an kasa sarrafa dandazon matasa masoya ga jarumar dake son yin hoton da ita.
Rahoton da muka samu ya tabbatar mana da cewar wasu daga cikin daliban ba iya son daukan hoto ya kai su ga wurin da jarumar ke zaune ba. Majiyar mu ta shaida mana cewar wasu daliban sun so afkawa jarumar ba don jami'an tsaron jami'ar dake wurin sun yi gaggawar shiga tsakani ba.
Da kyar jami'an tsaron jami'ar suka yi nasarar raba Rahama Sadau da janjamim masoyan dake ta kokarin kusantar ta da manufa daban-daban.
Babu rahoton samun lahani ko yin wata illa ga jarumar, an fitar da ita lafiya daga harabar jami'ar.
Kokarin Majiyar mu na jin ta bakin Jarumar ko kungiyar daliban jami'ar Umaru Musa yaci tura.
A satin da ya gabata ne jaruma, Rahama Sadau, ta yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta a kasar Cyprus.

Ingantacciyar Hanyar Hacking Din Facebook Account A Kowacce Kalar Waya

HAUSA NOVELS MASTER | December 18, 2017 | 0 Comments
Ingantacciyar Hanyar Da Ake Yin Hacking Din Facebook

da farko dai ba wani babbar na'ura kake bukata ba hasali ma zaka iyayi da kowacce kalar waya matukar tanayin browsing.
Mataki na farko shine ka ziyarci shafin www.z-shadow.co idan ya bude zasu bukaci kayi register,to shawarar da zan baka shine kada kai anfani da email dinka wajen rijistern,kasa kowanne email ne saboda ba'a bukatar kayi verify,bayan ka yi rijista sai kayi login da username din sa kasa da password.
Shafin arewanow.com.ng ya yi bincike akan wannan hanya wadda masana suke kiransa da phishing.
Bayan kayi login zasu baka wani link wanda zaka turwa mutum duk sanda yayi login ta link din zasu turoma details din da yai login dasu.
Shi wannan link din dakabasu zasu gansa kamar facebook ne sai susa details din login nasu.

Zafafan Hotunan Maryam Yahya Na Wannan Satin

HAUSA NOVELS MASTER | December 18, 2017 | 0 Comments
Zafafan hotunan Maryam Yahya kenan daga shafinta na intagram.

Kungiyar Izala Tayi Gargadi Ga Rainin Wayon Da Akayi Wa Firdausi

HAUSA NOVELS MASTER | December 18, 2017 | 0 Comments

Izala Tayi Gargadi kan Wasa Da Hakkokin Addini a Najeriya
Kungiyar tayi Allah wadai da Nuna tsangwama Ga Firdausi
akan sanya Hijabi
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jawo hankalin
hukumomi zuwaga wani labari da ya yadu akan wata daliba
musulma, mai suna Amasa Firdaos, wacce ta kammala
karatunta na zama lauya amma aka hanata samun shaida
saboda ta saka hijabi.
Sheikh Bala Lau yayi gargadin cewa addini baitaba zama
ginshiki ko mizani ba a tsarin gwamnatin Naijeriya. Saboda
haka, muna jawo hankalin mahukuntan kasar, malamai da
shuwagabanni da masu alhakin daukan ma'aikata ako wani
sashi da sauran jaami'an kasar da sukiyaye sanya banbancin
addini a matsayin mahangar duba cacanatar 'yan kasar a
kowane irin lamari musamman duba da yawan addinan dake
kasar.
Shugaban yaci gaba da cewa A yayinda muke kushe wannan
Al'amari danuna rashin dacewar sa, a gefe guda kuma muna
taya sauran 'yan Najeriya neman ayiwa wannar dalibar adalci
kuma a gurfanar da duk masu hannu a cikin wannan cin zarafi.
Muna kara jaddada kira ga hukumomi da 'yan kasar da suyi
koyi da sauran kasashen duniya domin wayewarsu takai har ga
kyale kowa yayi mu'amala gwargwadon yadda addininsa
yatanadar batareda tsageranciba ga dokokin ubangiji" Inji shi"
A karshe Muna tunatar da hukumomi cewa lokaci yayi da za'a
waiwayi karuwar rashin mutunta addini dayake aukuwa a baya
bayannan a najeriya, Shige gona da iri da yunkurin tozartarda
masu riko da addini Domin daukan matakin bai daya a kasar.
(C) JIBWIS Nigeria.

Kungiyar Izala Tayi Gargadi Ga Rainin Wayon Da Akayi Wa Firdausi

HAUSA NOVELS MASTER | December 18, 2017 | 0 Comments

Izala Tayi Gargadi kan Wasa Da Hakkokin Addini a Najeriya
Kungiyar tayi Allah wadai da Nuna tsangwama Ga Firdausi
akan sanya Hijabi
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jawo hankalin
hukumomi zuwaga wani labari da ya yadu akan wata daliba
musulma, mai suna Amasa Firdaos, wacce ta kammala
karatunta na zama lauya amma aka hanata samun shaida
saboda ta saka hijabi.
Sheikh Bala Lau yayi gargadin cewa addini baitaba zama
ginshiki ko mizani ba a tsarin gwamnatin Naijeriya. Saboda
haka, muna jawo hankalin mahukuntan kasar, malamai da
shuwagabanni da masu alhakin daukan ma'aikata ako wani
sashi da sauran jaami'an kasar da sukiyaye sanya banbancin
addini a matsayin mahangar duba cacanatar 'yan kasar a
kowane irin lamari musamman duba da yawan addinan dake
kasar.
Shugaban yaci gaba da cewa A yayinda muke kushe wannan
Al'amari danuna rashin dacewar sa, a gefe guda kuma muna
taya sauran 'yan Najeriya neman ayiwa wannar dalibar adalci
kuma a gurfanar da duk masu hannu a cikin wannan cin zarafi.
Muna kara jaddada kira ga hukumomi da 'yan kasar da suyi
koyi da sauran kasashen duniya domin wayewarsu takai har ga
kyale kowa yayi mu'amala gwargwadon yadda addininsa
yatanadar batareda tsageranciba ga dokokin ubangiji" Inji shi"
A karshe Muna tunatar da hukumomi cewa lokaci yayi da za'a
waiwayi karuwar rashin mutunta addini dayake aukuwa a baya
bayannan a najeriya, Shige gona da iri da yunkurin tozartarda
masu riko da addini Domin daukan matakin bai daya a kasar.
(C) JIBWIS Nigeria.

Yanda Zaki Kula Da Fatarki/ka A Lokacin Sanyi

HAUSA NOVELS MASTER | December 17, 2017 | 0 Comments

A daidai irin wannan lokaci,sanyi ya fara kwankwasa kofa a wurare da dama. Da zarar an fara ganin hazo ko hunturo lallai wannan alama ce ta nuna cewa sanyi ya shigo. A wannan lokutan ne yakamata a fara takatsantsan wajen kulawa da fatar jiki. Idan ba’a kula da fatar ba, har sai da ta gama bushewa ko yin gautsi, hakan na daukan lokaci kafin a samu a magancesu. Don haka ne a yau na kawo muku yadda za’a magance matsalolin fata a lokacin sanyi. · Man kadanya; tun yanzu ne yakamata a fara amfani da man kadanya a fata. Yin hakan kamar rigakafi ne domin magance matsalolin fata. Idan fata ta fara datsewa sakamakon sanyi, dole ne a yawaita shafawa domin man kadanya na dauke da sinadarai masu warkar da cututtukan fata. · Kaushin fata; idan an kasance ana da kaushin fata, dole ne a dunga sanya man ‘glycerin’ a cikin man shafawa. Koda alwala akayi yana da kyau a yawanta shafa man domin samun saukin lamarin. · Fason kafa; yana da kyau a rika sanya takalma masu laushi ba masu tauri sosai wadanda zasu rika illata fatar ba. Idan an kasance ana da fason kafa, sai a rika tsoma kafar a ruwan dumi da gishiri na mintuna goma sannan a rika gogewa da dutsen goge kafa sannan a shafa man ‘glycerin’ sannan a sanya safa kafin a kwanta a kullum domin samun saukin matsalar. · Sulbin fatar fuska; a samu ayaba sannan a kwaba ta tare da kindirmo sannan a rika shafawa a fatar fuska a bari na tsawon mintuna ashirin sannan a wanke da ruwan dumi a bari fuskar ta bushe da kanta kafin a shafa mata man fuska. · Karyewar gashi; kada a rabu da man zaitun a koda yaushe. A kasance ana sanya shi a gashi da zarar anji fatar kai ta fara bushewa. Yawaitar sanya man zaitun ko kuma man kwa-kwa na hana gashin kai zubewa.

Dalilin Da Yasa Aurena Ya Mutu-Asmau Sani

HAUSA NOVELS MASTER | December 17, 2017 | 0 Comments

Shahararriyar jarumar nan ta wasannin
fina-finan Hausa a masana'antar
Kannywood Hajiya Asma'u Sani ta fito
tayi karin haske game da ainihin
musabbabin dalin mutuwar auren ta a
kwanan baya bayan ta shafe shekaru a
gidan mijin nata.
Hajiya Asma'u da tayi tsokaci game da
hakan a yayin wata fira da tayi da
majiyar mu ta bayyana cewa mijin ta
da aura a shekarun bayan ya yi zato
ita wata hamshakiyar mai kudi ce
musamman ma saboda yadda yaga
tana fitowa amatsayin mace mai kudi
a cikin fina-finan ta da dama.
NAIJ.com dai ta samu cewa sai dai a
tun lokacin da ya gano ba haka
lamarin yake ba, a cewar ta sai ya fara
wulakanta ta yana ci mata mutunci
daga baya kuma har yazo ya sake ta.
Daga nan ne ma kuma sai jarumar ta
yi kira ga sauran al'ummar dake yi
mata kallon kamar taki son zaman
aure ne da su yi mata uzuri don kuwa
ta matukar son aure don a cewar ta
ko gobe idan ta samu miji zata sake
yin aure domin shine suturan dukkan
'ya mace

Ni Bazawara Ce Mai YaYa Biyu-Fatima Yola

HAUSA NOVELS MASTER | December 16, 2017 | 1Comments

shahararriyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood wadda ta dade tana bayar da gudummuwar ta masana'antar mai suna Fatima Isa Muhammad Yola wadda aka fi sani da Teema Yola ta bayyana cewa tabbas ta taba aure har ma tana da 'ya'ya biyu yanzu haka amma bata so tana yaya ta hakan saboda yanayin sana'a ta.
Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin da take yin fira da majiyar mu ta jaridar Blueprint inda take yin karin haske a game da rayuwar ta a baya da kuma yanzu.
HausaTutoblog dai ta samu cewa Teema Yola ta bayyana babban dalilin da yasa bata son tana yayata zawarcin nata shine saboda kada ta kori wasu mazan dake son ta da aure.
Haka zalika jarumar ta bayyana cewa a kowane lokaci idan dai har ta samu namijin da take so zata yi auren ta domin a cewar ta cikar mace kenan a dakin mijin ta.

Yanda Zaka Samu Kyautar 150MB Zuwa 1GB Alayin MTN da Yanda Zakai Anfani Dasu.

HAUSA NOVELS MASTER | December 16, 2017 | 0 Comments
Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.
Kamar yanda kuka sani shafin ArewaNow ya kanyi kokari wajen samar muku hanyoyin da zakusha garabasa daga layikan waya,to yau munzo muku da wata garabasa ta MTN.
Yanda zaka Samu Kyautar 150mb alayin mtn tare da kyautar kudi #500
ta hanyar tura sakon kamar haka
XMAS zuwa 2200 nantake zaka samu insha Allah.
Yanda zakayi amfani da mb cikin sauki.
Abin bawuya matukar ka iya yadda ake setting prove na whatsapp zeyi kawai server zaka chanza
dafarko kasanya game.mtnonline. com
nanta ke xefara aiki
amma kayi setting kamar yanda ake seta whatsapp server Wadan da Basu iya Settings na Mb din nan da Ake samuba na Games ga Yadda zakuyi
Kaje ka naimo opera Handler ko Uc browser hamdler Amma fa ta wayar ka in Symbian ce ka dauko opera handler.sis in java ce ka dauko
Opera handler.jar
Ucbowser handler.jar
Idan kuma Android ce
Karshen sunan Handler yazama .Apk
Allah yasa ku gane abokai na
saiku dawo ku bude opera
handler dinku bayan kun budeta zakuga ta bude muku shafin handler menu saikuyi click akan
sannan kuyi chan kasa ku duba
inda aka rubuta saiku shiga ku xabi
sannan kuyi kasa ku shiga saiku Rubuta Game.mtnonline. comshikkenan sai kuyi save ku bude operar shikkenan sai kuci gaba
da more browsing Allah ya bada sa,a.
Ga masu android zasu iya duba wainnan hotunan.

a kula shi wannan mb zaka iya tarasu dayawa ta hanyar aika sakon STOP zuwa 2200,sai kasake request na mb ta hanyar dann XMAS zuwa 2200.

Zan So Yarinyata Tayi Harkar Films

HAUSA NOVELS MASTER | December 16, 2017 | 0 Comments

Jarumin nan na fina-finan Hausa a
masa'antar Kannywood mai suna Sadiq
Ahmad ya bayyana cewa shi zai so diyar
sa ta yi harkar fim don bai ga wani abu
ba a cikin ta.
Jarumin ya bayyana haka ne a yayin
da yayi wata fira da majiyar mu dake
wallafa mujallar da ta jibanci harkar
fim a watannin baya.
NAIJ.com ta samu cewa jarumin yayi
wannan bayanin ne a lokacin da yake
ansa wata tambaya da aka yi masa
game da ko zai iya barin diyar sa ta
cikin sa tayi harkar fim.
A ansar da jarumin ya bayar kuwa ya
bayyana cewa tabbas zai iya barin ta
domin kwa ba wani abu bane.
"E, zan iya barin ta ta yi. Ai ba wani
abu bane," in ji shi.
Sai dai kuma ya bayyana cewa ba zai
tursasa mata ba wajen cewa dole sai
ta yi fim din ba inda yace duk abun
da take so shine za ta yi.
A cewar sa: " Kasan bahaushe yace ka
haifi mutum, baka haifi halin sa ba; za ta iya yiwuwa na ce tayi amma ita kuma tace burin ta ta zama lauya ko likita, kaga kenan babu yadda zan yi da ita."

Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 9

HAUSA NOVELS MASTER | December 16, 2017 | 0 Comments

ganin kamar har yanzu bai nitsuba da abin gaba yasa
Mlm Abubakar ciro woyarsa
Mahmoud d'in ya kira yana d'agawa yace.
"Kazo gani a Parlon Abban ka".
Toh ya amsa tare da tasowa cikin happy ya iso parlon,
Yana shiga gaban su ya zauna a kasa kan carpet cinkin girmamawa yace.
" Baba gani"
Abba kam ido ya tsura mai cikin mmk
Shiko kai ya sad'a k'asa.
A hankali Baba yace.
"Yana da kyau Abban ka yaji buk'a tarka daga bakinka"
Kai ya kuma shafawa sannan a hankali yace.
"Abba dama eh ni dama Abba ni Aure nake sonyi kuma Khadija ce nake so sannan mun gama mgn da ita ni nafi son ayi Auren nan kusa".
Abba kam tunda ya fara mgnar ya bud'e baki da mmk yana binshi da ido shi har tsoro Yaron ya bashi (wai Aure nake so)
Mlm Abubakar ne yace.
"Toh Ibrahim kaji ko"?
Ehh yace cikin sanyi sannan ya kalleshi cikin kura mai ido yace.
" Mahmoud Aure kake so ko"?
Kai ya gyad'a tare da cewa "ehh"
Abin yanzu dariya ya bawa Abba shiyasa cikin sanyi yace.
"Wato kun gama shirya zancenku kai da Khadijan. ita Khadijan ta yarda da Auren"?
_Kai Mahmoud ya isa dan duniyar domain ta kar karewa yayi ya rink'a tsara zance yadda abin zai tafin mai dai-dai_
Gyara zama yayi cikin sanyi yace.
"Yauwa Abba daman mun gama mgnar da ita ita tace duk abinda za,ayi kar a kirata Dan kunya yakeji ta kuma amince dani shiyasa ma tak'i komawa gidan Sulaiman"
Ido Abban ya tsura mai cikin son gane gskyar zance sai kuma yace "Khadijan ko ta amince"?
Ehh yace cikin k'arfin hali
Baba ne ya kalleshi cikin sanyi yace.
" toh tashi ka tafi"
toh yace tare da mik'ewa ya fice abin shi.
Mlm Abubakar ya juyo gunshi cikin mgn irin ta manya yace.
"Toh ka ga da idon ka dai tunda sun dai-daita Kansu to kar a shiga hak'insu
Mgnar. Khadija kuwa ni inaga kunya takeji ace ita bazawara zata Auri saurayi kuma k'aninta dan haka kar a tuntub'eta da zancen
In inna samu zama zama nanda kwana 4 zanje gun Alhj Sani muyi mgnar zanzo mu tafi da kai din
Kuma ko iyayensu mata a bari sai mun gama komai a gaya musu kasan zasu iya yin k'ananan mgn ganu a kai.
A haka suka Ajiye shawara shiko Mahmoud duk abinda ake ciki mlm kan kirashi ya gaya mai.
sannan sunje sun samu Baba Sani
Shi ba Abin da yace sai sanya Alkhairi.
Sannan sun tsaida zance za,a daura Auren randa za,ayi na Amira.
Shi kuwa Mahmoud yana sane da komai Amman baiyi gigin gayawa Khadijan da itako bata san komai ba akan zancen.
Sai dai yana yawan shige mata shak'uwa kuma mai k'arfi ta k'ara shiga tsaka ninsu.
Yau ta kama jumma,a kuma gone asabar ne ta kama Daurin Auren Amira da Amir d'inta sai kuma Mahmoud da Amarya Khadija da bata san da zancen ba.
Ran jumman kuma akayi walima mai k'aya tarwa.
Da daddere bayan sallan insha,a
Khadija ne cikin sauri ta nufi d'akin su Mahmoud d'in cikin d'an had'e fuska ta lek'a parlon hank'oshi tayi yana kwance kan 3 str daga shi sai 3 qtr a jikinshi.
ganin shi hakan sai taji wani irin nauyi ya rufeta da sauri ta juya tana.
Dan Allah ka fito kazo ka kaini
Target zan karbo dinku nanmu gun Yaxid yace yana jirana".
Cikin kasala ya mik'e tare da rataye rigarsa a kafad'a ya fito ya tsaya a gabanta da sauri ta kuma juyawa dan wlh bata son ganin shi hakan
Shi kuwa rigar yasa cikin kasala yace.
"Muje ko".
Ita kam tuni tayi gaba cikin mota ko cikin sanyi ya dan rink'a mata hira har sukaje suka karbo dinkunan suka juyo suna dawowa.
tuk'in yake cikin sanyi da k'orewa tafiya yake a hankali sun mik'e kan titin da zai maidasu cikin Yola a hankali kamar maiyin rad'a cikin kasala da wani yanayi ya juyo yana mata wani irin kallo yace.
Khady gobe fa...

Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 8

HAUSA NOVELS MASTER | December 16, 2017 | 0 Comments

"Mahmoudu Aure dai ina Aure kake so toh wannan ba wani matsala shi Aure nufin Allah ne kuma insha Allah gobe zanje muyi mgn da Abban naku
Sannan ka dena damuwa da batun masu zuwa gareta in dai rebonka ce ba makawa zaka samu".
Shi kuwa kai ya sunkuyar cikin jin dad'i da k'arfin guiwa yace
"Baba Amman da yau za,ayiwa Abba mgn dan fa su iyayen Nazir d'in sunce goben zasuzo ai kuma gwara mu rigasu".
murmushi yayi tare da kallon yaron yana tunani shiko wanne irin hallitta Allah ya mishi
Cikin dan fara,a yace
" toh yau zanzo da dare"
Toh yace cikin jin dad'i tare da mik'ewa zai fita
Adam da yanzu ya shigo kuma yaji mgnar tasu kad'an cikin mmk yabi Mahmoud d'in da ido shiko hannu ya mik'a mai suka gaisa sannan ya juya gun
Goggo Zahra ya kalleta a dan sokane
ya karya wuya cikin sanyi yace
"Ayyah Goggo Zahra baki yi Allah sanya Alkhairi cikin Auren ba "
dariya sukayi baki d'aya Adam yace
"Tab har anyi Auren kenan har kuna Neman sanya Alkhairi mijin bazawara manya"
Juyawa yayi gun Adam d'in cikin shafa kanshi yace
"Sunnah ce babba Annabinmu ma da bazawara ya fara".
Mlm ne da Goggo Zahra sukace
" wannan haka yake
Allah baka ladan raya sunnar"
Amin yace tare da yi musu slm ya tafi.
A wunin ranar Mahmoud ya wuni cikin farin ciki sai dai kuma yakanji far gaba bai San ya iyayenshi zasu d'auki zancen ba sannan uwa uba Khadijan,
Cikin wunin ya kuma gano yadda zai boye zancen gareta in yaso sai taji abin daga baya,
Da dare bayan anyi sallan inshah
Malam Abubakar ya fito cikin kamala bai zame ko ina ba sai
gidan Alhj Ibrahim.
cikin mutun ta juna suka isa parlon shi
Bayan sun gaggaisa malam ya gyara zama tare da gyaran murya cikin nitsuwa yace.
"Ibrahim wata mgn ce mai mahinmanci ke tafe dani fatan zamu samu fahimtar juna"
Shima zaman ya gyara tare da juyowa gareshi cikin kula yace.
"Insha Allah zamu fahimci juna".
Kai ya jinjina sannan cikin hikima ya koro mai jawabin da Mahmoud din yaje ya fad'a mai,
Shiru Abban yayi tare da jinjina kai sannan ya kalli
Mlma Abubakar tare da sauk'e ajiyar zuciya yace.
" Abubakar yanzu kai me ka fahimta a zancen Yaron nan,?
Yanzu ina Mahmoud ina Aure?
yanzu anyama Mahmoud yasan me ake cewa Aure?
Abubakar Yanzu nefa Mahmoud d'in ya jona University anya yaro nan yasan me ake cewa Aure ai ko yayunshi mata ban tab'a Aurar dasuba har sai sun gama secondary sun fara zuwa F,C,E kafin suke Aure"
Tunda ya fara mgnar Malam Abubakar ke binshi da ido har saida yazo k'arshe sannan yace.
"Amman nayi mmkin jin zantu kan nan daga bakinka shin
A sheri,a ace akece sai yaro yayi digiri zaiyi Aure?
Shin Wanne matsayin da sharad'u musulunci ya gindayar in NAMIJI ko mace sun kai za,a basu damar suyi Auren?
Shin a cikin su wanne Mahmoud ya gaza bai kaiba?
Ibrahim ase baza ka marawa Mahmoudu baya ba ko dan a kauda shi daga sharrin zina, shin baka tsoro yaron fa ya fito fili yace Aure yake so in mun hanashi zai iya aikata komai
shin kana tunanin bazai san ya zai zauna da maceba?
Ko ka manta Mahmoudu yaro ne mai ilimin Addini duk abin da kake tunani bai saniba K'ur,ani da hadisai sun sanar dashi,
Haba Ibrahim ase kaima kana da tuaninnan Na tauye rayuwar yaro ko yarinya Wai da sunan sai Sunyi karatu mai zurfi kuma kana sane da illan da hakan ke jazawa yaran mu shin kasan irin halittar da Allah ya masane? kana da yakinin zai iya danne buk'a tarsa har yayi shekarun da kake tunani? Kuma kana da dukiyar da damar da zaka warewa rayuwarsa da matarsa komai cikin wadata haba Ibrahim kayi tunani mu a shekara nawa iyayenmu suka Aura mana mata"?
Tun da ya fara jero mai tabb'ayoyi sai shiru yayi mgnganusa Na ratsashi cikin sanyi ya rink'a gyad'a kai,
alamar a,a a,a.
Shi kuwa mlm cikin sanyi yace.
"Toh matuk'ar dai ba so kake muyi sanadin yaduwar barna da fasadiba to ayi mishi abinda yake buk'atar dan wlh illace baba iyaye su kafe kan yayansu bazasu yi Aureba har sai sunkai wani mataki a karatu boko hakan Na jawo yawan barna da fasadi ".
Kai ya kinji yace.

Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 7

HAUSA NOVELS MASTER | December 16, 2017 | 0 Comments

Shiru tayi cikin sanyi jin zantu kanshi Na ratsata Dan ta tabbar gsky yake gaya mata.
A haka yai ta mata jirwaye mai kama da wonka Wanda itako bata gane ba
Har dai ta fara jin bacci cikin jin baccin da raunin murya tace.
"Mahmoudu bacci nakeji fa".
dariya ya danyi cikin jin dad'i
Yace
" Yau kuma Mahmoudu na zama ne Nana"?
"ehh mana ba ka fiye son girma ba"
" A a fa bani ke son girma ba Allah ne ya bani girman"
Mik'a tayi cikin sanyi tayi hamma alamun baccin sosai,
Shima mik'ar yayi tare da cewa.
"Kiyi Addu,a toh".
"Toh" tace tare da katse kiran
Shiko gaba d'aya daran ranan ya kasa samun nitsuwa tunani yake da gske fa ya Auwal gani yake bazan iya Aureba ko kuma mugunta ce shi yana can da matarsa Niko yana had'a min zafi.
A haka ya tashi ya sake watsa ruwa tare dayin alwala yazo yai nafila tare da Addu,ar Neman zab'in Allah
Daga nan kuma yayi ta karatu k'ur,ani
A haka bai samu yayi baccin kirkiba saida akayi sallan Asuba sannan ya dawo ya konta yasamu ya fara baccin.
Shine bai tashiba sai 11 dai-dai
yana tashi wonka yayi ya sa manyan kaya ya fito ras sai k'amshi yake sumar kana sai shek'i yake ya fito ras dashi.
Cikin gida ya shiga kai tsaye d'akin Mami ya shiga kan gado ya sameta tana konce cikin sanyi ya zauna kan carpet ya kalleta a nitse yace.
"Mami barka da safiya"
Cikin son d'an nata tai murmushi tace "babana antashi lfy"
Kai ya Dan Sosa cikin sanyi yace
"Toh lfy zance" ido ta tsura mai tare da cewa
"Akwai matsala ne"?
Kai ya gyad'a alamun a,a dan baisan ta yadda zata d'auki matsalan tashi ba.
K'anwarsa Amira dake gefe ne ta kalleshi cikin raha tace "Hamma Mahmoud ni har yanzu baka bani gudumawar ka bafa gashi Aure saura 1 week"
Mami ya tsurawa ido cikin yana yin ji yarinyar nanfa Amman ni in an tashi sai ace kar nayi mgn
dariya mami tayi tare da cewa
Zai baki ai Amira"
Shiko baki ya tab'e tare da cewa "jeki kira min Khadija ta kawo min breakfast na"
Mami ce tace "a a ita Amiran ta kawo ma dan Khadija tayi bak'in suna parlon baki"
Zubbur ya mik'e tare da zare ido yana waya zo gun ta kuma Wai su mayune kam"?
yana kaiwa nan kuma ya juya ya fita
Ita kuwa Mami zare ido tayi da bud'e baki Cikin tsoro tace
"Amira kar dai mgnar yayanku gsky ne Na shiga uku Mahmoud son yarin yar nan yake Yaro k'ara mi da bazawara ina bazai yiwuba"
Ita ko Amira cikin sanyi tace
Toh Mami mene dan yazo Anty Khadija ai naga ba haramun bane ko"?
Cikin had'e fuska tace
Ke baki da hankali Mahmoud ai bai kai Aureba sannan inzai Auren ma ya nemi dedanshi mana Amman ya sunk'umo matar da tafi shi kuma sai Na kama cewa mutane Mahmoud d'ana d'an kwalisan nan ya buge da son bazawara wlh bazata sabu ba"
Haka dai tayi ta kumfar baki.
Shiko yana fita parlon ya wuce yana shiga tare da slm
bai ko kalli inda Nazir yakeba yace
"Wallahi yunwa nakeji kuma gashi ina son shiga school"
Nazir dinne yace
" Mahmoud kana gida kenan"?
Ehh yace ba tare daya kalleshi ba sannan ya juya gunta yana kizo ki ban in yaso ki dawo
cikin girma Nazir yace "a a
Mahmoud kaje dai ka jira".
Tuka rinnan ya fad'a a ranshi tare da murtuk'e fuska ya juya zai mgn kenan ya Auwal ya shigo Wanda dama yana Parlon Anty ne suna tattaunawa kan Nazir d'in cikin had'e fuska yace
" kai Mahmoud me kakeyi a nan kaje Mami Na nemanka.
Fuska ya k'ara murtuk'ewa sannan ya fice yana
Hmmm
yana fita gidan Goggo Zahra ya wuce
yana zuwa ko yayi sa,a malam Abubakar nanan mijin Goggo Zahra kuma abokin Abbanshi suna gaisawa da Gaggo Zahra yace
Goggo gun baba fa nazo.
Toh tace dashi tare da cewa "to tashi muje tun kan bak'in su fara ta ruwa"
Suna shiga parlon shi yaje gaban shi cinkin girmamawa ya gaidashi
Ya amsa cikin son yaron dan yana da nitsuwa da cikar haiba cikin halin girma yace
"Mahmoudu ya karatu ya su Abban ka"?
Kai ya dan sunkuyar tare da cewa "Alhamdulillah"
Daga nan kuma sai yayi shiru tare da sunkuyar da kai
Lkci d'aya shiko mlm ya gane da mgn a tare dashi
Shiyasa cikin kula yace
"Mahmoudu meke tafe da kaine ka gaya min kar kaji komai kaji ko".
Shiko cikin jin k'arfin guiwa yace.
"Baba dama......
Sai kuma ya dan dago ya kalli mlm da yana yin nitsuwa,
shi kuwa sei
Gyad'a mai kai yayi cikin yanayin
fad'i ina jinka.
Cikin nitsuwa yace
" Baba dama ina son a taimaka a gayawa Abba abinda nake sone"
Ajiyar zuciya ya sauk'e cikin sanyi yace "gaya min mene kake son"?
A nitsa ya korowa mlm jawabin buk'a tarsa cikin hikima da shiga zuciyar mai sauraro ya kareshi zancen da cewa
" Ni ko yau a shirye nake da Aurenta "
Shi kuwa mlm Abubakar ido ya tsura mai a ranshi kuwa Allah ya godewa da ya tsare musu imanin yaron nasu ya samai tunanin gwara yayi Aure dan badan Allah ya tare shi ba zai iya aikata komai tunda har yakai matsayin da zai fito kai tsaye ya bayya na buk'a tarshi ga Auren.
Cikin kula yace.

Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 5

HAUSA NOVELS MASTER | December 16, 2017 | 0 Comments

Ita ma Azumin take
5 dai-dai ta shiga kitchen ta had'a musu abin bud'a baki kamar kullum,
Bai shigo ba sai da akayi sallah sannan ya shigo a parlon Anty suka zauna,
Fruit salad ta samai a Cup ta mik'a mai tana
"Gashi kaci Sa,a na regema wlh da shanyewa zanyi,
shi kuwa
Ido ya d'an tsura mata tare da cewa
" ai duk d'aya ne inma kin shanye ni kikewa tanadi gaba,
Cikin rashin gane mgnar da ya nad'e mata tace
"ai yayi dad'i ne shiyasa bazan hanaka ba"
Wani irin kallo ya bita dashi
A ranshi yace Na tabbata kinfi haka dad'i
A zahiri kuwa cewa yayi
"Ngd baby"
Jin haka yasa ta had'e fuska ta bud'e baki da nufin cewa yaro
Shiko gane Abinda take son fad'a yasa cikin sauri ya had'e bakinta da.......
Manna mata cup d'in yayi a bakinta,
Sanyin cup d'in ya ratsata cikin jin sanyin ta d'an kad'a mai ido alamar zan shanye fa ka rasa,
Shi kuwa ido ya tsurawa fuskarta tare da kafesu kan pink lips d'in ta idonshi yana ganin yadda take motsasu alamar zata shad'in.
Ido ya lumshe tare da sauk'e ayijar hrt ya d'aga mata giransa d'aya cikin alamun kisha,
aiko ta k'ara manne lips d'inta kan Cup d'in shiko ya d'an tura mata yana mai kashe mata ido d'aya,
gaba d'aya ya mace da kallonta shiyasa har baisan sanda ya tura mata shi har ya haura sanan lips d'in ta na saman cup d'in
Da sauri ta janye kanta cikin Sa hannu ta ture nashi hannun ido ta zare mai cikin had'e fuska tace
"Jifa zaka tura min har cikin hanci dan mugunta ai kai ka nuna bai dameka ba".
Murmushi ya d'anyi dan ganin ya cika mata lips d'inta da fruit salad d'in
cikin lumshe ido a ranshi yake ina ma da Aure a tsaka ninsu wlh da da harshensa zai tsotse na kan lips d'in nata sai dai kuma ba dama.
sai kuma ya d'an sun kuyo yasa hannu saitin kan lips d'in nata a nufunshi in ta barshi da tafin hannu shi zai goge mata.
Ita kuwa ganin hakan yasa ta mike tana
" Allah ko Mahmoud ka rainani"
Shi kam murmushi yayi a ranshi ko cewa yake
"Ai da sauran raini tunda har yanzu ban zamo shugaba a gareki ba"
Cup d'in ya d'auke ya sa harshensa yana lasar ta inda ta shad'in
Ita kuwa wonke jikinta tayi sannan ta wuce d'akin
Mami ganin shuru bata shigoba ya sashi mik'ewa ya fito rik'e da pilet d'in abinci
d'akin Mamin ya lek'a cikin kauda kai yace
"Khadija ana kiranki a phone"
juyowa tayi tare da cemai "waye ne"?
Kafad'a ya d'aga tare da tab'e baki yace
" Na sani? ke da buhun samarinki tarukuce zallah daga masu k'aton ciki sai masu bak'in fuska".
Mik'ewa tayi ta fito tana
"Wlh fad'i kake kaima kasan wlh ba Na kushewa a cikin
ni suma bawai suna gabana bane a a kaiwa banson wula k'anta mutun ne".
Tsaki yaja tare da binta a baya yana tsurawa k'ugunta ido ganin yadda yake rausaya kamar da gangan take mai abin ma yake gani.
a parlon Anty cikin kauda kai yace
" kije ki kwanta ki huta dan dare yayi"
hara ta cilla mai tare da cewa to
Hamma Mahmoud ai dole kai guda ai dole na kwanta ko banjin bacci"
K'arisa shigawa yayi yana shafa sajen fuskarsa da dan cika izza yace
"Ai na kaine dan girma ne dai Allah ya bani tunda yayini NAMIJI".
Tab'e fuska tayi tare da cewa "Hmmm ni ina da abin yi Dan wonka nake son yima"
Juyawa yayi ya fita tare da cewa
"Toh sai kin gama kimin flashing akwai mgn"
yana tafiya d'akin su Abincin ya danci sannan ya watsa ruwa ya dawo parlon ya kwanta kan 3 str
shiru yana jiran yaji kiranta amma shiru har zuwa kusan 9 sannan ya kirata yana mai tunanin ko wani mayenne ya tsareta da surutu,
aiko yana kira bata d'aga ba har saida ya kuma na 3 sannan ta d'aga
yana jinta
rai a bace yace
"Dawa kike mgn tun d'azu?
Kuma me yake gaya miki?
Sannan ba nace in kin gama kimin flashing ba"?
tsaki ta ja sannan tace " Dan Allah mlm kar ka k'ara min zafi kan zafi"
shiru yayi cikin had'e fuska yace
"zafin me kuma?"
Tsaki ta kuma ja cikin sanyi da rawar murya kamar zatayi kuka tace.
"Ba ya Auwal bane ya kirani wai gobe Nazir zai zo sannan kuma jibi zai turo iyayenshi gunsu Abba"
Mgnar ta sonki zuciyarsa har baisan sanda ya mik'e zaune ba
Cikin Neman k'arin bayani yace
"Ubban me zaizo ya miki? sannan me iyayenshi zasu zo yi mana a gida"?
Cikin sanyi tace
" Wai Auren yake so ayi da wuri kuma shi ya Auwal yace ai shi Dan mutun cine".
a kufule yace
"Zancen banza ai kowa ma nason Auren da wuri ko an gaya musu kin resa masoya ne shi wayafi buk'atar Aure zancen banza wlh bazai yiwuba insha Allah zan d'auki mata ki".
Ita har ga Allah gani take yana guje mata shiga wani haline bare da taji yana cewa
" toh shi kuma a wurin d'aurin Auren zaice ya sake ki ko"?
A sanyaye tace
"Ni banson zancen wani aurema yanzu wlh ya Auwal ne ke son jaza min".
Ajiyar zuciya ya sauk'e tare da cewa
" Khady ki dena cewa bakya son Auren shin kin manta shi Aurennan sunnace baba shin bakya fatan ki zama uwa ta gari ga y'ay'ayenki Ke a zaton ki a shekara run kin nan za,a barki bakiyi Aure bane
Sannan ai ke da kankima muddin kina da lfy toh dole zaki buk'aci Auren
Ko so kike ai ta zagin iyayenmu ace sun zuba miki ido"?

Lefe kyauta ga duk Wanda zai azure ni

HAUSA NOVELS MASTER | December 15, 2017 | 2Comments
Sananniya jarumar nan ta fina finan Hausa da ta shahara wajen fitowa mutuniyar banza kamar karuwa ko yar shaye-shaye mai suna Hauwa Waraka ta yi tayin lefe ga dukkan wanda ke da sha'awar auren ta. 

Jarumar Hauwa tayi wannan tayin ne a cikin wataa fira da tayi da majiyar mu ta BBC Hausa inda suka ruwaito ta tana cewa idan ma wakilin na majiyar ta su zai aure ta ita zata hada masa lefe ma. HAUSAMINI.com ta tattaro daga majiyar tamu cewa jarumar ta bayyana cewa dukkan mai son ta kar yaji tsoro ko fargabar fitowa ya fada mata don kuwa auren ta ko kadan ba zai yi tsada ba duba da yadda zata saukaka masa sosai a arha tubus. 

Da majiyar tamu ta tambaye ta ko me yasa take fitowa a matsayin mutuniyar banza a fina-finai kuwa sai jarumar ta ce ita tana sha'awar hakan ne domin ta fadakar da mutane game da illolin hakan. 
 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger