Home » » Abun Da Yasa Ake Kira Na Shu'uma

Abun Da Yasa Ake Kira Na Shu'uma

HAUSA NOVELS MASTER | December 12, 2017 | 0 Comments

fitacciya kuma sananniyar jarumar nan ta dandalin
shirya fina-finan Hausa wato kannywood,
Fati Abubakar wacce aka fi sani da Fati
Shu’uma ta bayyana dalilin da yasa ake
kiranta da wannan suna.
A cewar jarumar, rashin jin da ta
nuna a cikin fim din Shu’uma ne ya sa
ake mata inkiya da wannan suna.
Fati ta bayyana cewa ta koyi tarin
darasi kan makomar mutane masu
munanan dabi’u a cikin wannan fim
din.
Ta kuma jadadda cewa tana matukar
jin dadin fitowa a matsayin muguwa
cikin fina-finai.
Ta ce: "Na fi so na fito a matsayin
muguwa saboda na fadakar da mutane irin
illar mugunta da son rai.
"Ka san yawancin jarumai sun fi son fitowa a matsayin masu kirki, amma ina ganin hakan ba ya aikewa da sako kai tsaye kamar jarumi mugu, wanda ake nuna
karshensa bai yi kyau ba" , in ji jarumar.
Share this article :
 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger