Home » » An Kara Samun Wata Amarya Ta Yi Yunkurin Sheke Mijinta

An Kara Samun Wata Amarya Ta Yi Yunkurin Sheke Mijinta

HAUSA NOVELS MASTER | December 18, 2017 | 0 Comments

A ranar Asabar din da ta gabata ne wata sabuwar amarya da duka-duka aurenta makonni uku kacal ta kaiwa mijinta hari da sabuwar reza ta kuma raunata shi matuka
Amaryar da aka bayyana sunanta da Shafa Muhammad ‘yar shekaru 28 da haihuwa ta aikata wannan aika-aika ne a unguwar Arkillar Liman, cikin karamar hukumar Wamakko, jihar Sokoto
Majiyarmu ta gano cewa, Shafa ba ta son mijin da aka aura mata mai suna Umar Shehu a saboda haka ne ma tun da aka yi auren ta ke ajiye reza kusa da gadon kwananta ita da mijinta
Kwatsam kuwa sai a daren Asabar, 16 ga watan Disamba, 2017, makonni uku daidai da kaita daki, mijinta, Umar ya nemi da ya tara da mai dakinsa lamarin da ya sanya ta dauki rezarta ta yi ta yanyanka masa akansa da goshinsa
Kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar Sokoto, ASP Ibrahim Abarass ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce “Tuni aka kai Umar asibiti, kuma ya samu kulawa ta gaggawa kuma yana samun sauki bayan an sallamo daga asibiti”
“Ita kuwa Shafa, tana kulle a wajen ‘yan sanda kuma za a gurfanar da ita a gaban kulaya da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike” inji Abarass
Abarass ya shawarci iyaye da su guji yi wa ‘ya’yansu auren dole.
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger