Home » » Dalilin Da Yasa Aurena Ya Mutu-Asmau Sani

Dalilin Da Yasa Aurena Ya Mutu-Asmau Sani

HAUSA NOVELS MASTER | December 17, 2017 | 0 Comments

Shahararriyar jarumar nan ta wasannin
fina-finan Hausa a masana'antar
Kannywood Hajiya Asma'u Sani ta fito
tayi karin haske game da ainihin
musabbabin dalin mutuwar auren ta a
kwanan baya bayan ta shafe shekaru a
gidan mijin nata.
Hajiya Asma'u da tayi tsokaci game da
hakan a yayin wata fira da tayi da
majiyar mu ta bayyana cewa mijin ta
da aura a shekarun bayan ya yi zato
ita wata hamshakiyar mai kudi ce
musamman ma saboda yadda yaga
tana fitowa amatsayin mace mai kudi
a cikin fina-finan ta da dama.
NAIJ.com dai ta samu cewa sai dai a
tun lokacin da ya gano ba haka
lamarin yake ba, a cewar ta sai ya fara
wulakanta ta yana ci mata mutunci
daga baya kuma har yazo ya sake ta.
Daga nan ne ma kuma sai jarumar ta
yi kira ga sauran al'ummar dake yi
mata kallon kamar taki son zaman
aure ne da su yi mata uzuri don kuwa
ta matukar son aure don a cewar ta
ko gobe idan ta samu miji zata sake
yin aure domin shine suturan dukkan
'ya mace
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger