Home » » Domin Yin Apply Na Nigerian Army Na Wannan Shekarar SaikU Shiga nan ku karanta Yanda Ake Apply

Domin Yin Apply Na Nigerian Army Na Wannan Shekarar SaikU Shiga nan ku karanta Yanda Ake Apply

Ibrahim Auwal | December 30, 2017 | 0 Comments

Rundunar Sojin Kasa na Najeriya ta fara rajisatar daukan sabbin mutane masu sha'awar shiga aikin karo na 77 a ranar Juma'a 29 ga watan Disambar 2017 kuma za'a dakatar da yin rajisatar ne a ranar Juma'a 9 ga watan Febrairu na 2018.
Sanarwan da ta fito daga Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Brigediya Janar Sani Usman ya ce rundunar tana bukatar matasa maza da mata daga duka jihohin Najeriya masu shekaru 18 zuwa 22 ko kuma masu shekaru 22 zuwa 26 ga fanin masu koyan sana'o'i.
Rundunar Sojin Kasa na Najeriya ta fara rajistar daukan sabbin ma'aikata

Masu sha'awar rajisatar sai su ziyarci shafin intanet na hukumar a http://recruitment.army.mil.ng domin cike bayannan da ake bukata. Ana kuma iya kiran wadannan lamabobin wayar domin tambaya ko neman karin bayani; 08038575725 / 08037234828.
Har ila yau, Ana iya samun karin bayani daga jaridun Daily Sun da kuma Leadership bugun gobe Lahadi 31 ga watan Disamba na 2017. Ku sani cewa rajisatar kyauta ne.
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger