Home » » Izala Ta Nemi APC Ta Cika Alkawuran Da Ta Dauka A 2015

Izala Ta Nemi APC Ta Cika Alkawuran Da Ta Dauka A 2015

Ibrahim Auwal | December 19, 2017 | 0 Comments

- Kungiyar Izala ta nemi APC ta cika alkawarin ta ga ‘Yan Najeriya
- Shugaban Majalisar Malamai ne yayi wannan jawabi kwanan nan
- Sheikh Jingir ya tunawa Shugaba Buhari da alkwarin da yayi a 2015
Kungiyar Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ta Kasa ta nemi Gwamnatin APC ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta cika alkawarin da tayi wa Jama’a. Malamin yace Talakawa da kan su su ka rika kokarin ganin Buhari ya samu mulki.
Kungiyar Musulunci ta yi kira ga Buhari da babban murya
Kungiyar ta tunawa APC da alkawarun da ta yi wa ‘Yan Najeriya lokacin yakin neman zabe a 2015. Jaridar Dily Tryust tace Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar addinin Sheikh Sani Yahaya Jingir ne yayi wannan kira a Garin Jos.

Babban Malamin yayi wannan jawabi ne wajen wani taron dalibai a wata kwalejin kiwon lafiya a jiya. Jingir ya tunatar da Gwamnatin Muhammadu Buhari irin alkawarin da ta dauka na gyara harkar ilmi, noma, da ma gyara hanyoyi a Najeriya.
Bayan nan APC tayi alkawarin kawo karshen rashin aikin yi har da ba masu zaman kawai N5000 duk wata. Malamin ya yabawa yakin Shugaba Buhari na kawo karshen ta’addanci da sata amma akwai sauran aiki wajen habaka tattalin kasar.
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger