Home » » Jama'a Mu Tashi Mui Karatu-Wani Yace Ya Gano Wani Kauye Da Manzon Allah s.a.w yai Bauta Acikinsa A Jahar Katsina.

Jama'a Mu Tashi Mui Karatu-Wani Yace Ya Gano Wani Kauye Da Manzon Allah s.a.w yai Bauta Acikinsa A Jahar Katsina.

Ibrahim Auwal | December 29, 2017 | 0 Comments
Ku kalla yanda rahoton yazo,yakamata ace mutashi mudinga karatu saboda kada wani makaryace ya saka mu a kwali.

WATA SABUWA!!!
********************
MANZON ALLAH (S.A.W) YA ZO WANI KAUYE A CIKIN JIHAR KATSINA.
********************
YANZU HAKA, DUBUN DUBATAR JAMA'A NA TA TURURUWA DON GANI DA IDO DA NEMAN TABARRUKI.
********************
An gano inda Manzon Allah (S.A.W) ya yi Bauta a Karamar Hukumar Matazu ta jihar Katsina.
********************
A Karamar Hukumar Matazu da ke jihar Katsina, a wani Kauye da ake kira "KOGARI" wani bawan Allah mai suna ASHIRU da ke zaune a GIDAN DAMO, ya gano wurin da Manzon Allah (S.A.W) ya yi Sallah kuma ya Kwanta.
********************
Yanzu haka, maza da mata, da tsofaffi, da matasa, da matan aure sun cika wurin dankam, abin sai wanda ya je ya gani, Dubban Mutane ne ke ta yin tururuwa har daga wasu jihohi.
********************
A yanzu haka, domin ganin wannan abin mamaki da neman TABARRUKI, kuma yanzu haka, akwai wata mata da ta haihu a wajen, ana yin Sujjada a kuma rungumi wajen.
********************
Itacen wajen duk an kwakule su ana cinyewa domin neman TABARRUKI, sannan akwai ruwa a wajen mutane na zuwa da robobi da butoci domin samun ruwan, ana nuna inda MANZON ALLAH (S.A.W) ya yi SALLAH da inda ya KWANTA.
Ana zuwa wurin ayi Sujada da Zikiri, da sauran abubuwa na nau'in bautar Allah (S.W.T) domin neman tabarruki.
********************
JAMA'A MASANA TARIHIN MANZON ALLAH (S.A.W) YA YA KU KE GANIN WANNAN AL'AMARI???
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger