Home » » Kannywood Sun Ce Ba Zasu Yafewa Rahama Sadau Ba...ko meyasa?

Kannywood Sun Ce Ba Zasu Yafewa Rahama Sadau Ba...ko meyasa?

Ibrahim Auwal | December 21, 2017 | 0 Comments

Mujallar Fim Magazine da ta fito wannan makon ta buga wani labari dake cewa kungiyar kula da finafinan Hausa a kano MOPPAN tace bazata yafewa korarriyar jaruma Rahama Sadau laifin datayi ba a baya duk da cewa jarumar ta aike da takardar neman afuwa kuma ta fito ta gayawa Duniya cewa tayi nadamar abinda ta aikata.
Ali Nuhi ne ya yiwa Rahamar jagora zuwa gurin masu fada aji a harkar finafinan Hausa a Kano inda ta nemi Afuwa kuma ta rubuta takarda a hukumace ta neman Afuwa.
Mujallar ta Fim Magazine dai a satin daya gabata ta kwarmato cewa anyi shirin yin zama ranar laraba dan tattauna batun yafewa Rahamar laifinta ta dawo taci gaba da yin finafinan Hausa amma sai dalilin ciwon idon da Kabiru Maikaba, daya daga cikin jigon kungiyar yake fama dashi aka daga zaman zuwa ranar Asabar.
Asabar tazo ta wuce bamuji komai ba sai gashi yau labari ya fito an fasa yafewa jarumar.
Saidai abinda ke daurewa mutane kai shine Rahama Sadau kwanannan ta shirya wani fim din Hausa da kanta me suna Rariya wanda har ya samu kyautar fim din da yayi fice a wannan shekarar, to wai ko korar da akawa Rahamar iya garin Kanone kawai.
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger