Home » » Korar Ma’aikata:Sanata Shehu Sani Kaduna ya kara caccakar Gwamna El-Rufai

Korar Ma’aikata:Sanata Shehu Sani Kaduna ya kara caccakar Gwamna El-Rufai

HAUSA NOVELS MASTER | December 19, 2017 | 0 Comments

- Sanata Shehu Sani ya caccaki Gwamnan Kaduna El-Rufai
- Shehu Sani yace giyar mulki ke daukar Gwamnan Jihar
- Sanatan na tsakiya yace Gwamnan ba zai koma ba a 2019
Mun samu labari cewa Sanatan tsakiyar Kaduna Kwamared Shehu Sani ya kara caccakar Gwamna Nasir El-Rufai. An dai dade ana ‘yar tsama tsakanin Gwamnan Jihar da kuma Sanatan Jihar. Sanatan yace Gwamnan ba zai koma kujerar sa ba a 2019.
Sanata Shehu Sani ya soki Gwamna El-Rufai
Sanata Shehu Sani a shafin sa na Facebook ya bayyana cewa an gama yin sak ko kuma a daga hannun wani ‘Dan siyasa a Jihar Kaduna. Sanatan ya koka da rashin adalcin da ake yi na korar Ma’aikata a Jihar ya kuma sha alwashin cewa za su koma bakin aikin su.
ArewaNow. Ta samu cewa
Shehu Sani ya nemi Musulmai da Kiristocin Jihar su dage da addu’a wajen ganin an tika Gwamnan da kasa a zabe mai zuwa. Sani ya kuma kira Jama’a da su rika bibiyar katin zaben su a kai-a kai. Sanatan yace abin da kowa ya shuka shi zai girba watau a zaben 2019.
Kwamared yace Talakawan Jihar za su maida martani na sallamar su daga aiki da aka rika yi a karkashin Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai. Sanatan yace giyan mulki ne ke daukar Gwamnan.
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger