Home » » Lefe kyauta ga duk Wanda zai azure ni

Lefe kyauta ga duk Wanda zai azure ni

HAUSA NOVELS MASTER | December 15, 2017 | 2Comments
Sananniya jarumar nan ta fina finan Hausa da ta shahara wajen fitowa mutuniyar banza kamar karuwa ko yar shaye-shaye mai suna Hauwa Waraka ta yi tayin lefe ga dukkan wanda ke da sha'awar auren ta. 

Jarumar Hauwa tayi wannan tayin ne a cikin wataa fira da tayi da majiyar mu ta BBC Hausa inda suka ruwaito ta tana cewa idan ma wakilin na majiyar ta su zai aure ta ita zata hada masa lefe ma. HAUSAMINI.com ta tattaro daga majiyar tamu cewa jarumar ta bayyana cewa dukkan mai son ta kar yaji tsoro ko fargabar fitowa ya fada mata don kuwa auren ta ko kadan ba zai yi tsada ba duba da yadda zata saukaka masa sosai a arha tubus. 

Da majiyar tamu ta tambaye ta ko me yasa take fitowa a matsayin mutuniyar banza a fina-finai kuwa sai jarumar ta ce ita tana sha'awar hakan ne domin ta fadakar da mutane game da illolin hakan. 
Share this article :

2 Comments:

muhammed garzali said...

Gani indai tana so 08050672153

Ibrahim Auwal said...
This comment has been removed by the author.

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger