Home » » Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 3

Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 3

HAUSA NOVELS MASTER | December 12, 2017 | 0 Comments

" Yauwa dama gobe ina so ka kani Geere"
Toh yace tare da cewa ni bari Na sake alwala sai da safe ko"
To tace tare da katsa kiran.
Shi kuma Mahmud kogin tunani ya fad'a yana kitsima yadda zai kasance shine miji kuma shugaba a gun Anuty Khadijan tasu
A fili yake cewa bana jin tsoron komai sai k'iyeyta daga gareta
Idanshi ya lumshe yana tuni surarta shi dai yasan ba matar da zata iya dashi sai itan itanma yana tausaya mata in ta iso gareshi.
A haka bacci yayi awon gaba dashi yana mai murad'in malla karta...
Suwaye Khadija da Mahmoud.?
Alh Ibrahim da Alh Sani yan uwan junane uwa daya uba daya sai k'anwarsu mace
Zahra, Y'an Asalin Fulanin Adamawa Yola suna cikin Yola sulum,
Ahl Ibrahim shine babba matansa 2 uwar gida mama yayanta 3 Sani sai Usman sai Autarsu Khadija sai Anty Zee mai yara biyu Fadil da Fadila.
Sai Alh Sani shima matansa 2 Uwar gida Mami yaran ta 4 Auwal shine babba sai Rayhana sai Fatima sannan Mahmoud sai autanta Amira sai Anuty Amarya wace take k'anwa ga uwar gidan Alh Ibrahim yaranta 4 Aysha itace baba sai Sulaiman sai Ibrahim takwaran bappanshi kenan sannan Autarta Nabila,
Ita Khadija tun sanda Alh Sani ya auro Anty k'anwar matar yayanshi sai suka dauko Khadija so ita Khadija gidan bappanta take k'anin mahaifinta sannan gaban ummarta k'anwar mahaifi yarta.
Sai Goggo Zahra yaran ta biyu babban danta Ahmad sai k'anwarsa Maryam.
So Khadija da Rayhana da Fatima da Aysha kusan tare sukayi karatu sai dai Dan fifiko da yake tsaka ninsu kad'an,
Shak'uwa ce sosai tsakanin yaran sannan iyayensu kuwa zaman lfy ne mai tarin yawa a tsaka ninsu.
Mahmoud da Khadija sunyi wani shak'uwa na daban wanda ake ganin sabo ne kawai da shak'uwa irin na yan uwan taka duk da Khadija ta girmi Mahmoud dan ko a maka ranta Khadija da Fatima da Aysha suna SS 3 yayin da shi kuwa Mahmoud yake jss 3 Rayhana ko a lkcin ta gama har tayi Aure tana cigaba a gidanta ya Auwal ko ya Dade da had'e digiri d'inshi har ya fara aikinshi sannan yayi Aurenshi.
Mahmoud da Khadija sabone mai tarin yawa a tsaka ninsu wanda ake ganin kawai iskarsu ce tazo d'aya dan Mahmoud shi ba mai yawan mgn bane sannan yana da halin ko in kula zai ganka sou goma Amman bazai sheida kamannin kaba ko yaushe kanshi a kasa, bai da yawan surutu sai in da Khadija ne zakajishi hira harda dry sam baison raini sannan yana da son girma over sam bai lamunci raini ba ita kuwa Khadija ta kasance ta kowace duk taron da suke a family d'in su muddin bata nan basa jin abin yayi armashi
ita kowa nata ne tana da faram-faram da Jama,a ta kasance so popular.
Khadija farace tas mai direrren jiki tana da sura ta ban Sha,awa da tafi ya da hankali duk wani da namiji lafiyye sannan tana da korjini ga cikar haiba komai na jikinta das kullum ka ganta sai kayi zaton yar 18 ce ga tsafta da kula da kai Khadija dai kekkyewa ce ta ajin forko kuma haka Allah yayi ta da farin jini bata fita nan da nan ba tare da wani ya biyota ba.
Shi kuwa Mahmoud Yaro ne mai k'walisa da son girma yana da cikar zati da haiba yana yin shi yasa ko manyan mutanen ke bashi girma dan tako ina ya kasance mai haiba farine tas shima yana da tsawo dan duk yafi yayunshi matan tsawo sannan yana da fad'in girji gashi mutunne shi mai halittar gashi a jikinsa hatta hannu shi da sharaban k'afafunshi suna cike da gashi maitaushi da shek'i yana konce luf a jikinsa gashin giransa ko irin Na Khadija sak wanda har ya kusa had'ewa hancishi zata har baki girjinshi ma rufe yake luf da suma so halittarsa takan sawa yana jin kanshi yes shifa namiji ne
Haka kuwa Allah ya jarabci zuciyarsa da son Khadija shi tun yana yaro ya gane yana sonta so kuma na Aure bawai so Na y'an uwan taka ba
Domain ko lkcin da zai kasance ya gama balaga da mafarkin Khadija balagarsa ta zauna gareshi.
Yayinda ita kuwa Khadija take mai so irin Na yan uwanta ka takuma daukeshi abokin shawara,.
Masu karatu zakiyi mmk ko wasu Suji takaici innace muku Khadija bazawara ce.
Amman a suna take bazawara a zahiri da bad'iri budur wace,
Domain Aurenta Na fari a deren da aka kaita
Gidan Angonta Sulaiman mahaifiyarshi tace bata yace koda d'akin ya shi gaba kuma tace muddin bai saketaba zata tsine mai dole a Daren ya saketa abinda ya k'ona ran yan kuwa yayinda shiko yake ganin rebonshi ke bibiyarta,
Lkci d'aya kuma Alh bashir ya fito shi kam Mahmoud baiji komai ba sai Aurenta yaji yayi kukan takaici da bak'in ciki ba iyaka a lkcin yawa kanshi kukan takaici da k'unci
Khadija da Alh Bashir sun zauna zaman shekara 3 Amman ba wani Abu da ya tab'a giftawa tsaka ninsu a dalilin matan shi da suka shuka mai tsiya dan kishi duk ran girkinta dashi da mace basu da banbanci,
Shi da kanshi yana tausaya mata yakuwa yi yunk'urin sakinta tun tuni
ita kuwa tace zata iya zama dashi a haka Dan inya sake ta bata San me mutanen zasu ce da itaba
Shi da kanshi yaga dai yana cutar da ita dole ya saketa,
Share this article :
 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger