Home » » Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 7

Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 7

HAUSA NOVELS MASTER | December 16, 2017 | 0 Comments

Shiru tayi cikin sanyi jin zantu kanshi Na ratsata Dan ta tabbar gsky yake gaya mata.
A haka yai ta mata jirwaye mai kama da wonka Wanda itako bata gane ba
Har dai ta fara jin bacci cikin jin baccin da raunin murya tace.
"Mahmoudu bacci nakeji fa".
dariya ya danyi cikin jin dad'i
Yace
" Yau kuma Mahmoudu na zama ne Nana"?
"ehh mana ba ka fiye son girma ba"
" A a fa bani ke son girma ba Allah ne ya bani girman"
Mik'a tayi cikin sanyi tayi hamma alamun baccin sosai,
Shima mik'ar yayi tare da cewa.
"Kiyi Addu,a toh".
"Toh" tace tare da katse kiran
Shiko gaba d'aya daran ranan ya kasa samun nitsuwa tunani yake da gske fa ya Auwal gani yake bazan iya Aureba ko kuma mugunta ce shi yana can da matarsa Niko yana had'a min zafi.
A haka ya tashi ya sake watsa ruwa tare dayin alwala yazo yai nafila tare da Addu,ar Neman zab'in Allah
Daga nan kuma yayi ta karatu k'ur,ani
A haka bai samu yayi baccin kirkiba saida akayi sallan Asuba sannan ya dawo ya konta yasamu ya fara baccin.
Shine bai tashiba sai 11 dai-dai
yana tashi wonka yayi ya sa manyan kaya ya fito ras sai k'amshi yake sumar kana sai shek'i yake ya fito ras dashi.
Cikin gida ya shiga kai tsaye d'akin Mami ya shiga kan gado ya sameta tana konce cikin sanyi ya zauna kan carpet ya kalleta a nitse yace.
"Mami barka da safiya"
Cikin son d'an nata tai murmushi tace "babana antashi lfy"
Kai ya Dan Sosa cikin sanyi yace
"Toh lfy zance" ido ta tsura mai tare da cewa
"Akwai matsala ne"?
Kai ya gyad'a alamun a,a dan baisan ta yadda zata d'auki matsalan tashi ba.
K'anwarsa Amira dake gefe ne ta kalleshi cikin raha tace "Hamma Mahmoud ni har yanzu baka bani gudumawar ka bafa gashi Aure saura 1 week"
Mami ya tsurawa ido cikin yana yin ji yarinyar nanfa Amman ni in an tashi sai ace kar nayi mgn
dariya mami tayi tare da cewa
Zai baki ai Amira"
Shiko baki ya tab'e tare da cewa "jeki kira min Khadija ta kawo min breakfast na"
Mami ce tace "a a ita Amiran ta kawo ma dan Khadija tayi bak'in suna parlon baki"
Zubbur ya mik'e tare da zare ido yana waya zo gun ta kuma Wai su mayune kam"?
yana kaiwa nan kuma ya juya ya fita
Ita kuwa Mami zare ido tayi da bud'e baki Cikin tsoro tace
"Amira kar dai mgnar yayanku gsky ne Na shiga uku Mahmoud son yarin yar nan yake Yaro k'ara mi da bazawara ina bazai yiwuba"
Ita ko Amira cikin sanyi tace
Toh Mami mene dan yazo Anty Khadija ai naga ba haramun bane ko"?
Cikin had'e fuska tace
Ke baki da hankali Mahmoud ai bai kai Aureba sannan inzai Auren ma ya nemi dedanshi mana Amman ya sunk'umo matar da tafi shi kuma sai Na kama cewa mutane Mahmoud d'ana d'an kwalisan nan ya buge da son bazawara wlh bazata sabu ba"
Haka dai tayi ta kumfar baki.
Shiko yana fita parlon ya wuce yana shiga tare da slm
bai ko kalli inda Nazir yakeba yace
"Wallahi yunwa nakeji kuma gashi ina son shiga school"
Nazir dinne yace
" Mahmoud kana gida kenan"?
Ehh yace ba tare daya kalleshi ba sannan ya juya gunta yana kizo ki ban in yaso ki dawo
cikin girma Nazir yace "a a
Mahmoud kaje dai ka jira".
Tuka rinnan ya fad'a a ranshi tare da murtuk'e fuska ya juya zai mgn kenan ya Auwal ya shigo Wanda dama yana Parlon Anty ne suna tattaunawa kan Nazir d'in cikin had'e fuska yace
" kai Mahmoud me kakeyi a nan kaje Mami Na nemanka.
Fuska ya k'ara murtuk'ewa sannan ya fice yana
Hmmm
yana fita gidan Goggo Zahra ya wuce
yana zuwa ko yayi sa,a malam Abubakar nanan mijin Goggo Zahra kuma abokin Abbanshi suna gaisawa da Gaggo Zahra yace
Goggo gun baba fa nazo.
Toh tace dashi tare da cewa "to tashi muje tun kan bak'in su fara ta ruwa"
Suna shiga parlon shi yaje gaban shi cinkin girmamawa ya gaidashi
Ya amsa cikin son yaron dan yana da nitsuwa da cikar haiba cikin halin girma yace
"Mahmoudu ya karatu ya su Abban ka"?
Kai ya dan sunkuyar tare da cewa "Alhamdulillah"
Daga nan kuma sai yayi shiru tare da sunkuyar da kai
Lkci d'aya shiko mlm ya gane da mgn a tare dashi
Shiyasa cikin kula yace
"Mahmoudu meke tafe da kaine ka gaya min kar kaji komai kaji ko".
Shiko cikin jin k'arfin guiwa yace.
"Baba dama......
Sai kuma ya dan dago ya kalli mlm da yana yin nitsuwa,
shi kuwa sei
Gyad'a mai kai yayi cikin yanayin
fad'i ina jinka.
Cikin nitsuwa yace
" Baba dama ina son a taimaka a gayawa Abba abinda nake sone"
Ajiyar zuciya ya sauk'e cikin sanyi yace "gaya min mene kake son"?
A nitsa ya korowa mlm jawabin buk'a tarsa cikin hikima da shiga zuciyar mai sauraro ya kareshi zancen da cewa
" Ni ko yau a shirye nake da Aurenta "
Shi kuwa mlm Abubakar ido ya tsura mai a ranshi kuwa Allah ya godewa da ya tsare musu imanin yaron nasu ya samai tunanin gwara yayi Aure dan badan Allah ya tare shi ba zai iya aikata komai tunda har yakai matsayin da zai fito kai tsaye ya bayya na buk'a tarshi ga Auren.
Cikin kula yace.
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger