Home » » Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 8

Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 8

HAUSA NOVELS MASTER | December 16, 2017 | 0 Comments

"Mahmoudu Aure dai ina Aure kake so toh wannan ba wani matsala shi Aure nufin Allah ne kuma insha Allah gobe zanje muyi mgn da Abban naku
Sannan ka dena damuwa da batun masu zuwa gareta in dai rebonka ce ba makawa zaka samu".
Shi kuwa kai ya sunkuyar cikin jin dad'i da k'arfin guiwa yace
"Baba Amman da yau za,ayiwa Abba mgn dan fa su iyayen Nazir d'in sunce goben zasuzo ai kuma gwara mu rigasu".
murmushi yayi tare da kallon yaron yana tunani shiko wanne irin hallitta Allah ya mishi
Cikin dan fara,a yace
" toh yau zanzo da dare"
Toh yace cikin jin dad'i tare da mik'ewa zai fita
Adam da yanzu ya shigo kuma yaji mgnar tasu kad'an cikin mmk yabi Mahmoud d'in da ido shiko hannu ya mik'a mai suka gaisa sannan ya juya gun
Goggo Zahra ya kalleta a dan sokane
ya karya wuya cikin sanyi yace
"Ayyah Goggo Zahra baki yi Allah sanya Alkhairi cikin Auren ba "
dariya sukayi baki d'aya Adam yace
"Tab har anyi Auren kenan har kuna Neman sanya Alkhairi mijin bazawara manya"
Juyawa yayi gun Adam d'in cikin shafa kanshi yace
"Sunnah ce babba Annabinmu ma da bazawara ya fara".
Mlm ne da Goggo Zahra sukace
" wannan haka yake
Allah baka ladan raya sunnar"
Amin yace tare da yi musu slm ya tafi.
A wunin ranar Mahmoud ya wuni cikin farin ciki sai dai kuma yakanji far gaba bai San ya iyayenshi zasu d'auki zancen ba sannan uwa uba Khadijan,
Cikin wunin ya kuma gano yadda zai boye zancen gareta in yaso sai taji abin daga baya,
Da dare bayan anyi sallan inshah
Malam Abubakar ya fito cikin kamala bai zame ko ina ba sai
gidan Alhj Ibrahim.
cikin mutun ta juna suka isa parlon shi
Bayan sun gaggaisa malam ya gyara zama tare da gyaran murya cikin nitsuwa yace.
"Ibrahim wata mgn ce mai mahinmanci ke tafe dani fatan zamu samu fahimtar juna"
Shima zaman ya gyara tare da juyowa gareshi cikin kula yace.
"Insha Allah zamu fahimci juna".
Kai ya jinjina sannan cikin hikima ya koro mai jawabin da Mahmoud din yaje ya fad'a mai,
Shiru Abban yayi tare da jinjina kai sannan ya kalli
Mlma Abubakar tare da sauk'e ajiyar zuciya yace.
" Abubakar yanzu kai me ka fahimta a zancen Yaron nan,?
Yanzu ina Mahmoud ina Aure?
yanzu anyama Mahmoud yasan me ake cewa Aure?
Abubakar Yanzu nefa Mahmoud d'in ya jona University anya yaro nan yasan me ake cewa Aure ai ko yayunshi mata ban tab'a Aurar dasuba har sai sun gama secondary sun fara zuwa F,C,E kafin suke Aure"
Tunda ya fara mgnar Malam Abubakar ke binshi da ido har saida yazo k'arshe sannan yace.
"Amman nayi mmkin jin zantu kan nan daga bakinka shin
A sheri,a ace akece sai yaro yayi digiri zaiyi Aure?
Shin Wanne matsayin da sharad'u musulunci ya gindayar in NAMIJI ko mace sun kai za,a basu damar suyi Auren?
Shin a cikin su wanne Mahmoud ya gaza bai kaiba?
Ibrahim ase baza ka marawa Mahmoudu baya ba ko dan a kauda shi daga sharrin zina, shin baka tsoro yaron fa ya fito fili yace Aure yake so in mun hanashi zai iya aikata komai
shin kana tunanin bazai san ya zai zauna da maceba?
Ko ka manta Mahmoudu yaro ne mai ilimin Addini duk abin da kake tunani bai saniba K'ur,ani da hadisai sun sanar dashi,
Haba Ibrahim ase kaima kana da tuaninnan Na tauye rayuwar yaro ko yarinya Wai da sunan sai Sunyi karatu mai zurfi kuma kana sane da illan da hakan ke jazawa yaran mu shin kasan irin halittar da Allah ya masane? kana da yakinin zai iya danne buk'a tarsa har yayi shekarun da kake tunani? Kuma kana da dukiyar da damar da zaka warewa rayuwarsa da matarsa komai cikin wadata haba Ibrahim kayi tunani mu a shekara nawa iyayenmu suka Aura mana mata"?
Tun da ya fara jero mai tabb'ayoyi sai shiru yayi mgnganusa Na ratsashi cikin sanyi ya rink'a gyad'a kai,
alamar a,a a,a.
Shi kuwa mlm cikin sanyi yace.
"Toh matuk'ar dai ba so kake muyi sanadin yaduwar barna da fasadiba to ayi mishi abinda yake buk'atar dan wlh illace baba iyaye su kafe kan yayansu bazasu yi Aureba har sai sunkai wani mataki a karatu boko hakan Na jawo yawan barna da fasadi ".
Kai ya kinji yace.
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger