Home » » Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 9

Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng 9

HAUSA NOVELS MASTER | December 16, 2017 | 0 Comments

ganin kamar har yanzu bai nitsuba da abin gaba yasa
Mlm Abubakar ciro woyarsa
Mahmoud d'in ya kira yana d'agawa yace.
"Kazo gani a Parlon Abban ka".
Toh ya amsa tare da tasowa cikin happy ya iso parlon,
Yana shiga gaban su ya zauna a kasa kan carpet cinkin girmamawa yace.
" Baba gani"
Abba kam ido ya tsura mai cikin mmk
Shiko kai ya sad'a k'asa.
A hankali Baba yace.
"Yana da kyau Abban ka yaji buk'a tarka daga bakinka"
Kai ya kuma shafawa sannan a hankali yace.
"Abba dama eh ni dama Abba ni Aure nake sonyi kuma Khadija ce nake so sannan mun gama mgn da ita ni nafi son ayi Auren nan kusa".
Abba kam tunda ya fara mgnar ya bud'e baki da mmk yana binshi da ido shi har tsoro Yaron ya bashi (wai Aure nake so)
Mlm Abubakar ne yace.
"Toh Ibrahim kaji ko"?
Ehh yace cikin sanyi sannan ya kalleshi cikin kura mai ido yace.
" Mahmoud Aure kake so ko"?
Kai ya gyad'a tare da cewa "ehh"
Abin yanzu dariya ya bawa Abba shiyasa cikin sanyi yace.
"Wato kun gama shirya zancenku kai da Khadijan. ita Khadijan ta yarda da Auren"?
_Kai Mahmoud ya isa dan duniyar domain ta kar karewa yayi ya rink'a tsara zance yadda abin zai tafin mai dai-dai_
Gyara zama yayi cikin sanyi yace.
"Yauwa Abba daman mun gama mgnar da ita ita tace duk abinda za,ayi kar a kirata Dan kunya yakeji ta kuma amince dani shiyasa ma tak'i komawa gidan Sulaiman"
Ido Abban ya tsura mai cikin son gane gskyar zance sai kuma yace "Khadijan ko ta amince"?
Ehh yace cikin k'arfin hali
Baba ne ya kalleshi cikin sanyi yace.
" toh tashi ka tafi"
toh yace tare da mik'ewa ya fice abin shi.
Mlm Abubakar ya juyo gunshi cikin mgn irin ta manya yace.
"Toh ka ga da idon ka dai tunda sun dai-daita Kansu to kar a shiga hak'insu
Mgnar. Khadija kuwa ni inaga kunya takeji ace ita bazawara zata Auri saurayi kuma k'aninta dan haka kar a tuntub'eta da zancen
In inna samu zama zama nanda kwana 4 zanje gun Alhj Sani muyi mgnar zanzo mu tafi da kai din
Kuma ko iyayensu mata a bari sai mun gama komai a gaya musu kasan zasu iya yin k'ananan mgn ganu a kai.
A haka suka Ajiye shawara shiko Mahmoud duk abinda ake ciki mlm kan kirashi ya gaya mai.
sannan sunje sun samu Baba Sani
Shi ba Abin da yace sai sanya Alkhairi.
Sannan sun tsaida zance za,a daura Auren randa za,ayi na Amira.
Shi kuwa Mahmoud yana sane da komai Amman baiyi gigin gayawa Khadijan da itako bata san komai ba akan zancen.
Sai dai yana yawan shige mata shak'uwa kuma mai k'arfi ta k'ara shiga tsaka ninsu.
Yau ta kama jumma,a kuma gone asabar ne ta kama Daurin Auren Amira da Amir d'inta sai kuma Mahmoud da Amarya Khadija da bata san da zancen ba.
Ran jumman kuma akayi walima mai k'aya tarwa.
Da daddere bayan sallan insha,a
Khadija ne cikin sauri ta nufi d'akin su Mahmoud d'in cikin d'an had'e fuska ta lek'a parlon hank'oshi tayi yana kwance kan 3 str daga shi sai 3 qtr a jikinshi.
ganin shi hakan sai taji wani irin nauyi ya rufeta da sauri ta juya tana.
Dan Allah ka fito kazo ka kaini
Target zan karbo dinku nanmu gun Yaxid yace yana jirana".
Cikin kasala ya mik'e tare da rataye rigarsa a kafad'a ya fito ya tsaya a gabanta da sauri ta kuma juyawa dan wlh bata son ganin shi hakan
Shi kuwa rigar yasa cikin kasala yace.
"Muje ko".
Ita kam tuni tayi gaba cikin mota ko cikin sanyi ya dan rink'a mata hira har sukaje suka karbo dinkunan suka juyo suna dawowa.
tuk'in yake cikin sanyi da k'orewa tafiya yake a hankali sun mik'e kan titin da zai maidasu cikin Yola a hankali kamar maiyin rad'a cikin kasala da wani yanayi ya juyo yana mata wani irin kallo yace.
Khady gobe fa...
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger