Home » » Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng

Namiji Baya Kadan By ArewaNow.Com.Ng

HAUSA NOVELS MASTER | December 12, 2017 | 0 Comments

Bayan shi ta kuma Aure da Adam Wanda ko tarewa basuyi ba ya saketa so daga nan tace ita ta hak'ura da Aure.
Kuma duk yan uwa ba wanda yasan cewa Khadija Na tare da budur cinta sai ita sai Mahaliccinta.
Yayinda shiko yake sonta a matsayin bazawarar shi kam Mahmud ya sa aranshi Khadija matarsa ce rebonsa ke juyawa da ita zata dawo kanshi ya kuma yiwa kanshi alk'awari a yan kwana kinsan zai Aureta ya tabbata tarwa kanshi shi zai iya rik'eta...... Wannan kenan!
Kashe gari da safe yana tashi ya shirya tsaf cikin riga da wondo na galila kalar pink ya amshesa ras ya fito cikin k'uriciyarsa da zafin jini sai k'amshi yake zubawa,
11 dai-dai ya Sakai cikin d'akin Anty ita kuwa dai-dai lkcin tana tsaye gaban mirror atampa ce a jikinta riga da siket siket d'in ya zauna ras a jikinta k'ugunta ya fito fes a cikin hips d'inta kamar sunyi mgn ga rigar itama ta wani lafe a jikinta gashinta take ta kiciniyar tubkewa,
Cikin bugawar zuciya da tsinkewar jini ya matsota a ranshi yake cewa
"Wayyo zata karya min Azumi".
Matsota yayi yasa hannu ya karb'i ribbon d'in cikin kamo gashin yana mai tsurawa k'irjinta ido ta jikin madubin ita kuwa k'ara matsoshi tai da nufin ya tufke matan, cikin rashin Sani hips d'inta ya gogi jikinsa,
Cikin wani irin daukewar numfashi ya......
Janye jikinshi yayi da sauri ya juya ya fito parlor ya zauna kan 1 str Nabila dake gefenshi ta kalleshi cikin d'oki tace
Ya Mahmoud nima zanje gidan ya Auwal ko ?".
Kai ya gyad'a mata dan in yace zai mgna muryarshi rawa zatakeyi ita kuwa tana gamawa ta fito sai k'amshi take
Cikin harara tace
"Yau kuma su Mahmoud d'inne a kusa ba mgn sai tsune ido da kauda kai".
Shi dai bayyi mgn ba sai mik'ewa yayi ya fita ita ko hannun Nabila taja suka fito d'akin Mami suka shiga bayan sun gaisa tace "Mami bari muje gidan ya Auwal dan jiya ya kirani yace inje akwai mgnar da zamuyi dashi". Cikin kula tace "toh ki gaishesu Amman ki dawo da wuri"
Toh ta amsa tare da fita ta yafa gyelenta a kafad'a sannan ta kama hannun Nabila
Suka fita a cikin matar ta sameshi zaune ya kife kanshi kan siteri ga gate an bud'e mai
Cikin tsokana ta ajiye Nabila a baya sannan ta bud'e gaba ta shiga cikin
tab'e baki tace
"Yanzu k'arfe 11:20 Am shine har azumi ya fara juya ma kai gsky Mahmoud akwai ka da ragwanta"
Cikin sanyi ya d'ago kanshi yayi motar key sannan ya harba cikin sanyi ga sanyi AC ga k'amshi turarukan jikinsu
Har saida suka hau babban titin da zai sadasu da jimeta sannan ta kuma kllonshi tace.
" nifa ba dole in zuwanne baka so"
Juyowa yayi ya tsura mata ido dai-dai lkcin da ya karya kona ya hau kan titin hayin gada
Mmk sosai tayi ganin fararen inda nunshi sunyi jazir sun kuma k'ank'ance cikin kula tace
"Broz ko dai baka da lfy ne"?
Kai ya jinjina da k'er ya bud'e baki yace
" ahhahh lfy ta lau kawai haka Na tsinci kaina"
ido ta tsura mai cikin mmkin jin yadda voice nashi ke fita gashi yak'i ya kuma mgn sai.
Ita shirun tayi har suka gaggara k'asan gadan sannan,
yace
"Khady me zakiyi a gidan ya Auwal naga satincan ma kinje"?
" nima ban saniba ya dai ce naje".
Hmm yace sannan yaci gaba da tfy,
12 dai-dai suka isa cikin Geere suna isa aka bud'e musu gate suka shiga yana tsayuwa Nabila ta bud'e mota ta fita a guje tayi cikin gida.
Itama Khadija hannu tasa zata bud'e sai kuma taji ya rufe motar,
Cikin tabb'aya ta juyo sai kuma tayi sauri kauda kanta ganin shima gaba d'aya ya juyo ya sata a gaba ya tsura mata ido,
Bata kulashi ba dan tasan fitina yake ji yanzu zai tsareta da wa,azi
Cikin sanyi kamar mai rad'a taji yace
"Khady"
Sai kuma ya d'anyi shiru sai ido da ya kafeta dasu cikin dan dak'ilewar voice yaci gaba da cewa
" Na rasa yadda zan fahimtar dake illar irin wannan shiga da kike yi ke baki san irin fitina da kike had'a sawa ba nace miki ki dena Sa gele amman bakya jin mgn ta"
ya k'arisa mgn cikin sigar fad'a da isa,
Ita kuwa dan sunkuyowa tayi ta dannan pin din da ya rufe k'ofar aiko ta kifa k'irjinta kan cinyarsa,
shi kam gaba d'aya jikinsa ya rink'a sakewa yana macewa jikin sit ya koma ya jingina ya lumshe idanshi cikin fizgar numfashi.
Ita kuma tana bud'ewa ta fita kai tsaye tayi cikin gida shiko hips d'inta yabi da ido harda baki yana mai jin tsoron abinda zai mishi katank'a da ita gaba d'aya yaji jikinshi ya mace bazai iya tuk'in ba.
Ita kuwa tana shiga
Anty Salma ta fito suka zauna a parlon sai hira suke dan Salma mace mai son Jama,a.
bayan sun gaisa ta kalleta cikin fara,a tace "ke Khadija ina Mahmoud d'in bazai shigo bane"?
Cikin mmk tace "kai Anty ya akayi kika san shi ya kamo mu"?
Dariya tayi tace
" ai nasan Mahmoud din ke kawoki"
dariya tayi sannan sukayi ta hiransu.
Suna cikin hiran ya Auwal ya fito parlon shi cikin fara,a ya amsa gaisuwar ta sannan yace
Share this article :
 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger