Home » » Ni Ba Mata Aure Bace Amma Kuma Ni Ba Budurwa Bace-Inji Rahama Sadau

Ni Ba Mata Aure Bace Amma Kuma Ni Ba Budurwa Bace-Inji Rahama Sadau

Ibrahim Auwal | December 26, 2017 | 0 Comments
Rahotanni sun kawo cewa korarriyar jarumar kamfanin shirya fina-fina hausa na Kannywood,

Rahama Sadau ta bai wa masoyanta damar yi mata tambaya a shafinta na twitter.
Wannan dama da jarumar ta bayar ya sa masoya na ta tururuwa wajen yi mata wasu tambayoyi da suka shafi rayuwarta.
Duk da cewa wasu daga cikin tambayoyin sun kasance masu nauyi jarumar tayi kokarin baar da amshoshin day a gamsar da masu yin tambayar ba tare da ta nuna dacin rai kan tambayar ba.
Ni ba cikakkiyar budurwa ba ce amma ban taba aure ba – Rahama Sadau
Shafin al’ummata ta wallafa tambayoyin da akayi wa jarumar da amshoshin da ta bayar kamar haka:
An tambayi jaruma Rahama ko ita budurwa ce gangariya:
Ga amsar da ta bayar “Ni budurwace, amma ba budurwa fil a leda ba, domin na rasa budurcina.”
An tambayeta wanda ya koyamata rawa?
Ta amsa cewa “Ali Nuhu.”
Me ta fi jin tsoro a duniya?
Ta ce “mutuwa.”
Yaushe za ta yi aure?
Ta ce “kwanannan,” amma bata bayyana ko wanene saurayin nata ba.
Shin za ta iya daina fim?
Ta ce “a’a.”
Dan wasan da ya fi birgeta a masana’antar fina-finan Hausa
Ta ce “Sadiq Sani Sadiq.”
Fim din da ta yi wanda ta fi so, ya fi birgeta
Ta ce fim din turanci na “Sons of the Caliphate”
An tambayeta ko shekarunta nawa?
Ta ce, “24.
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger