Home » » Rahama Sadau Tasha Da Kyar Daga Wasu Daliban Jami'a

Rahama Sadau Tasha Da Kyar Daga Wasu Daliban Jami'a

HAUSA NOVELS MASTER | December 18, 2017 | 0 Comments

Rahama Sadau, Jarumar wasan Hausa, ta sha da kyar a hannun dalibai masoyanta
- Lamarin ya faru ne a jami'ar Umaru Musa dake Jihar Katsina
- Jami'an tsaron jami'ar sun yi nasarar tserar da ita ba tare da samun lahani ba
Rahama Sadau, Shahararriyar jarumar wasan Hausa, ta sha da kyar a hannun wasu masoyanta, daliban jami'ar Umaru Musa dake jihar Katsina.
Tun farko shugabannin kungiyar daliban jami'ar ne suka gayyaci jarumar domin karramata a bikin ranar Mata ta duniya. Saidai lamarin ya kwacube bayan isowar jarumar harabar taron, Students Centre, dake cikin jami'ar.
Majiyar mu ta bayyana mana cewar jarumar ta iso wurin taron a makare, kuma zamanta keda wuya a teburin manyan baki sai dalibai suka barke da sowa da murnar ganin ta. Dalibai da dama sun nufi jarumar domin samun damar daukan hoto tare da ita, lamarin da ya kai an kasa sarrafa dandazon matasa masoya ga jarumar dake son yin hoton da ita.
Rahoton da muka samu ya tabbatar mana da cewar wasu daga cikin daliban ba iya son daukan hoto ya kai su ga wurin da jarumar ke zaune ba. Majiyar mu ta shaida mana cewar wasu daliban sun so afkawa jarumar ba don jami'an tsaron jami'ar dake wurin sun yi gaggawar shiga tsakani ba.
Da kyar jami'an tsaron jami'ar suka yi nasarar raba Rahama Sadau da janjamim masoyan dake ta kokarin kusantar ta da manufa daban-daban.
Babu rahoton samun lahani ko yin wata illa ga jarumar, an fitar da ita lafiya daga harabar jami'ar.
Kokarin Majiyar mu na jin ta bakin Jarumar ko kungiyar daliban jami'ar Umaru Musa yaci tura.
A satin da ya gabata ne jaruma, Rahama Sadau, ta yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta a kasar Cyprus.
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger