INA MATUKAR SON AURE_SADIYA KABALA

Ibrahim Auwal | February 14, 2018 | 0 Comments

A sakamakon yadda ra'ayoyi na rayuwa suke banbanta, wata fitacciyar jarumar fim ta dandalin Kannywood, ta bayyana yadda take matuƙar muradin aure, a yayin da wusu jaruman suke cewa ina ba yanzu ba sai sun shirya zuwa gaba. 

Ita dai wannan jarumar ta fina-finan hausa, Sadiya Kabala, ta bayyana irin yadda tale son taga tayi aure a rayuwa, inda har take rokon Mai duka da cewar, Allah ka aurar da mu. 

HausaMini.com ta fahimci cewa, akwai da yawan jaruman kannywood dake buƙatar aure, sai dai lokaci bai basu ikon samun abokan zama na rayuwar su ba, duba da kasancewar yanayi na rayuwa da mata suke ƙara yin yawa tare da samari ke gudun sa a sakamakon rashin abin hannu. 

A baya kadan jaridar NAIJ.com ta ruwaito cewa, akwai miliyoyin 'yan mata santala-tala a ƙasar Indiya dake buƙatar aure, sai dai suna kukan cewa har yanzu basu samu mazajen aure ba. 

Abubuwan Da Yakamata Ku Sani Game Da Fati Ladan Bayan Aurenta

Ibrahim Auwal | February 14, 2018 | 0 Comments
Fitacciyar tsohuwar jarumar Fati Ladan nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta shaidawa duniya cewa babu wani aibu a cikin hada zaman aure da kuma yin sana'ar fim don kuwa abu ne mai yiwuwa.
Shahararriyar jarumar dai da tayi shuhura a wasu fina-finai da dama a da kafin tayi aure ta ce ita bayan ta yi aure mijin na ta ma ne ya bukaci ta ci gaba da sana'ar ta amma ita da kanta ta ki.
dai ta samu cewa haka zalika jarumar ta bayyana cewa yanzu ita kam tana zaman ta lafiya a gidan mijin ta inda ta ce ta samu cikakken kwanciyar hankali da nutsuwa.
Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa yanzu haka dai ta koma makaranta inda tuni ma har ta kai aji uku a tsangayar koyon kimiyyar siyasa kuma tana sana'ar ta ta kiwon kaji da kifaye.
Daga: Naij Hausa

Jaruma Ummi Zeezee Ta Zagi Fim Din Gwaska Na Adam A Zango

Ibrahim Auwal | February 14, 2018 | 0 Comments
Wannan Abun Ya Dauke Mun Hankali Shine Nace Bari In Sa Muku ..

A Instagram A Comments Din Ali Nuhu Inda Yake Bawa Masoya Haquri Jaruma Ummi Zeezee Tayi Mummunan Comments Akan Fim Din Adam Zango Na Gwaska Return.
Ga Hoton Domin Ganewa Idon Ku...

Ali Nuhu Ba Ubangida Na Bane Uba Ne - Inji Adam A Zango

Ibrahim Auwal | February 14, 2018 | 0 Comments
Kannywood da wajen ta sun yi zaton cewa, budadiyar wasikar da jarumi Adam A Zangn ya rubuta da irinsu Alh Nuhu yake. Domin ana ganin a kwana kin baya tayi tsami tsakaninsu. Duk da yake sunyi silhu da juna, sanin duk mai hankaline cewa silhu alkairi ne.
Ganin mutane zasu yanke hukunci da igiyar zato, shine dalilin da yasa Adam A Zango ya wallafa wata sanarwa gajeriya a Instangram. Sanarwar dauke take da nuna cewa yanzu tsakanin Adam A Zango da Ali Nuhu da rikici bare kuma gaba.
Ga abinda Adam A Zango ya rubuta a Instangram:
''Ali Nuhu ba Uban gida na ba ne Uba na na ne''.
Inji Adam A Zango.
Wannan ya nunawa duniya cewa, budadiyar wasikar da Adam A Zango ya yi zuwa ga makiyansa to bada Ali Nuhu yake ba. Bisala'akari da abinda yaje a Instangram. Duk wanda ka kira da uba to yana da mahimmanci awajen ka. Dan haka ya zama masoyin ka ba makiyanka ba.
Dan haka Ali Nuhu masoyin Adam A Zango shima A Zango ya yarda da haka.
Daga : Adamu Ciroma

Jaruma Sadiya Kabala Tasha Dakyar Akan Sanya Wannan Hoton A Shafinta Na Instagram

Ibrahim Auwal | February 14, 2018 | 0 Comments

Ga kadan daga cikin abinda mutane ke cewa akan wannan lamari:

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger