Hotunan Shagulgulan Bikin Fatima Dangote Da Jamil MD Abubakar

Ibrahim Auwal | March 20, 2018 | 0 Comments

Lilpee: RAYUWA

Ibrahim Auwal | March 20, 2018 | 0 Comments
Lilpee: RAYUWA

Let me use this shot note  to tell my fans something about this life rayuwa is something easy but deficulte to understand when you hear this song by the name rayuwa you will understand me very we'll...


DOWNLOAD:- LILPEE "RAYUWA"

Download Now

Rahama Sadau Ta bada Labarin Yadda ta Rasa Budurcin Ta

Ibrahim Auwal | March 20, 2018 | 1Comments
RAHAMA SADAU TA BADA LABARIN YADDA TA RASA BUDURCIN TA.

Tayi wannan bayanin ne lokacin da take yin hira da kafar sadarwar mu a satin dasu ka gabata.

Tace Ita ba Budurwa bace, sabida an taba mata fyade lokacin tana qaramar yarinya.

Fitacciyar Jarumar Fina-finan Hausa ta masana'antar "KANNYWOOD" wato Rahama Sadau tayi qarin bayani game da yadda ta rasa Budurcin ta, kamar dai yadda ta bada labari a watannin baya, cewa ita ba cikakkiyar Budurwa bace.

Mai karatu dai zai iya tunawa cewa an zafafa muhawara a watannin baya lokacin da jarumar ta bayar da amsa ga wani Masoyin ta daya tambayeta mene matsayin Budurcin ta a kafar Sadarwa ta zamani wato "INSTAGRAM" Inda ta bashi amsa da cewa ita ba cikakkiyar Budurwa bace.

Jarumar ta qara da cewa Abinda take so ta fadawa Duniya shine an taba yi mata Fyade ne lokacin tana, qaramar yarinya kuma a lokacin mane ta rasa Budurcin ta.


GA MASU WAYOYIN HANNU NA ANDROID MUN TANA DA MUKU MANHAJA (APPLICATION) WANDA ZAI SAUQAQA MUKU ZIYARTAR WANNAN SHAFI.

Hauka da Rashin San in ciwon kai Inji Umme ZeeZee

Ibrahim Auwal | March 20, 2018 | 0 Comments
Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee wadda sananniyar masoyiyar tsohon shugaban kasace, Janar Ibrahim Badamasi Babangida kuma a bayabayannan ta fara nuna goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar tayi wasu kalamai masu kaushi akan shugaba Buhari ta masoyanshi.


Ummi ta yi tambaya a dandalinta na sada zumunta da muhawara cewa idan ba atikuba wa kuke tunanin zai iya/ya kamata ya mulki Najeriya?, mutane sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi akan wannan tambaya ta Ummi.

Daga cikinsu akwai wani bawan Allah daya ce shi yana ganin Atiku baya daga cikin wadanda suka cancanci zama shuwagabannin Najeriya.
Ummi ta mayarwa da wannan mutumin amsa kamar haka"

kin Mutane da basa fahimtar turancin da bai taka kara ya karya ba, abunda nayi posting fa ba dogon magana nake so ba ko kushe wani dan takaran da ba naka ba. abunda post dina yake nufi shine, in Atiku ne dan takararka ka rubuta sunansa in kuma bashi bane ma ka rubuta sunan dan takaranka ko kuma ka rubuta nobody amma ba surutai na adawa nake so ba a comment pls dan in surutan adawa kuke so akan Buhari to ai in kuna da kunya baku da bakin magana domin a abubuwan da yayi alkawarin zaiwa kasa in an zabeshi har yanzu baiyi ko daya ba kuma duk wanda zaiji tsoron Allah ba tsoron Buharin ba yasan baiyiwa kasa komai ba in banda talauci da fatara da yunwa daya sa kasar a ciki ammah talaka da yake mahaukacine baisan ciwon kansa ba wai har yanzu shi yake so.

Mtwssss Allah ya sauwake da yan Nigeria hausawa.

Wallahi da a turaine bai isa yayi bakin milki irin wannan ba, da talakawan da kansu zasu ce a canja shi"

How to Check 2018 Jamb Exam Result

Ibrahim Auwal | March 20, 2018 | 0 Comments
HOW TO CHECK JAMB 2018/2019 EXAM RESULTS.

According to him, candidate who sat for the Jamb 2018 Now can Check their Exams Result by visiting the official website of the Board at www.jamb.org.ng with their individual registration numbers.1. Visit the Jamb portal at www.Jamb.org.ng/

2. Check on "Check 2018 UTME Results"

3. Enter your Jamb Registration Number in the space provided.

4. Click on "Check my Result"

5. If you participated in the Jamb Exam, your result details will be displayed.

Babu kama ta: Na zarce kowa a Duniyar kwallo - Inji Ronaldo

Ibrahim Auwal | March 20, 2018 | 0 Comments

Tauraron dan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa babu kamarshi, babu wanda za'a iya hadashi dashi a Duniyar kwallo saboda bega wani dan kwallon da ya kaishi jajircewa da kwazo da iyawaba.
onaldo yace babu wanda zai taba zama kamarshi, mutum zai yi iya yinshi amma bazai taba zama Criatiano Ronaldo ba domin shi na dabanne, Cristiano Ronaldo ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda yake sanye da wasu sabbin kayan kamfanin NIKE.

Ronaldo dai wanda ya fara haskakawa a kungiyar Manchester United a shekarar 2003 ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Ballon D'or ta farko a can a shekarar 2008 kamin daga baya yazo Kungiyar Real Madrid inda ya lashe kayutar sau hudu, dama duk wata kyauta da ko wane dan kwallo yake hankoron samu.

Ana dai hada Ronaldo ne da abokin takararshi na Barcelona, watau Messi amma masu sharhi na ganin Messi kwalllonshi ta baiwace, shi kuwa Ronaldo dagiyace da jajircewa da naci tasa yace haskakawa.

Ronaldon ya kara da cewa tun yana Manchester ya gayawa kanshi cewa sai ya zamo tauraron dan kwallon Duniya da babu irinshi.

Ali Nuhu da Adam A. Zango basu dogara da Allah ba - Inji Nura M. Inuwa

Ibrahim Auwal | March 20, 2018 | 0 Comments
Fitaccen Mawaki Nura M. Inuwa ya bayyana cewa Ali Nuhu da Adam A. Zango ba su dogara da Allah ba, sannan kuma suna wasa da nauyin da Allah ya dora masu.

M Inuwa ya kara da cewa, a duk lokacin da jaruman suka tashi yin rigima ba a iya su ta ke tsayawa ba, sai ta shafi har mabiyan su. Nura dai ya yi wannan tsokacin na sa ne a kan rikicin da ake yi tsakanin Ali Nuhu da Adamu Zango, wanda ku san kowa yanzu ya fahimci cewa jaruman ba su shiri.

A ranar asabar, 16 ga watan maris mawakin ya rubuta masu wata zungureriyar wasika a shafin sa na Instagram. Ga abin da ya rubuta:

Shawara Zuwa ga Adam A Zango da kuma Ali Nuhu, na ga alama kuna wasa da nauyin da Allah ya dora muku na jama'ar da ke karkashin ku.

Sannan kuna kokarin raunana imaninku, domin kuwa alamomi suna nuni da baku dogara da Allah ba! duba da tsoran da ku ke nunawa junanku, sannan duk lokacin da za kuyi rigimar me yasa baku barin ta a junanku sai kun nemo mabiyanku kun jefasu a bala'i, sannan in za ku shirya baku nemansu hakan yana nuni da son kai, da rashin adalci da rashin imani.
fitar ku ku ke dubawa baku duba ta wasu? Wanda suke shiga rigimarku, su sai da rai suna rasa abinci a cikin masana'antar Kannywood dalilin rigimar ku, wanda da ba ku sa su a ciki ba za suyi mu'amala da kowa kuma su nemi halak dinsu.

Amma in kuna rigima wannan ba zai yi aiki da wannan ba, wannan bavzai gaisa da wannan ba, don kawai baku shiri kuna haifar da gaba da tashin hankali da rashin zaman lafiya shi ne soyayyar da ku ke wa kannywood din?

Ko shi ne taimakon na k'asan da ku ke ikirarin kuna yi? ku cire girman kai ku cire rawunan da kuka dorawa kawunan ku na son girma, wane ne sarki, wane ne Yarima, dukanin ku babu wanda aka nadawa wata sarauta duka ku kuka sawa kanku.

In kuma da wanda aka nadawa wani rawani ya fito ya fadawa duniya wuri da kuma lokacin da akayi nadin, babu Sarki sai Allah. Haka kuma babu abin dogaro sai shi daga ALLAH sai Annabi, su ne masu girma kowa a kasa yake ba wanda yafi wani sai wanda yafi tsoran Allah.

Amma kun kasa gane hakan, in kun ga dama ku gyara a zauna lafiya, idan kuma baza ku gyara ba bakin ciki zai sa ku yi tayin baya kuna cutar da kan ku kuma kuna cutar da wasu, karshen mugunta kenan.

Ra'ayi na ba irin na kowa bane, kuma banyi don yabo ko kuma neman wani abu a gun daya daga cikin ku ba, dama bantaba yi ba, kuma Insha Allah ba zanyi ba. don Allah na yi kuma ina so na kasa su daina cutuwa, bana raina yaro kuma bana raina babba, ina son kowa da karuwa ne ba iya kaina ba.

Duk wanda yaji haushi ba zan bashi hakuri ba gaskiya ce, sai na fada komai dacin da za ta yi wa wasu. A karshe ina kira ga duk wanda yasan yana tsoran rasa abinci gun wani kada yayi reposting ni dai babu mai bani sai Allah. Alhamdulillah.

MUSHA DARIYA MATAR BOSHO DA KISHI

Ibrahim Auwal | March 07, 2018 | 0 Comments
 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger