Cikakken Sakon Tsohuwar Jaruma Fim Ummi Zeezee Zuwa Ga Yan Nigeria

Ibrahim Auwal | June 28, 2018 | 0 Comments

Ga Sakon Tsohuwar Jarumar Fim Ummi Zeezee Zuwa Ga Yan Nigeria Ta Rubuta Wannan Sakon A Shafin Instagram Dinta

""Salam dear nigerians ,wasu suna amfani da sunana a face book sunamin karya iri iri da kuma bata suna a gareni Wanda ina kyautata zaton masoyan APC ne.hakan ya samo asaline domin sunsan bana shiri da boss dinsu Mr president.last week sun hada hotona Dana wani gardin banza a daji wai yana lalata dani sukaga hoton baiyi tasiri ba domin Allah ba azzalumin bawansa bane baya kuma kama bawa da laifin da bai aikata ba.to da suka ga hotona da suka hada da gardi Wanda kuke cewa timaya ne baiyi tasiri ba sai kuma suka dawo suka ce wai ni yar shi'A ce,shima suka ga baiyi tasiri ba da suka dangan tani da shi'A.sai kuma yau suka sake cewa wai na fita daga shi'A har na dawo ina addu'a Allah ya dauwa Mar da "sir zazzaky " a gidan yari .to karya ake min ni Sam banyi maganah akan sir zazzaky cewar Allah ya dauwa Mar dashi a gidan yari ba domin ni ina tsananin girmama sir zazzaky saboda sunansa daya Dana mahaifina kuma ni aduniya duk mai sunan mahaifina to ina daraji shi saboda duk mai sunan kallon uba nake masa a sakamakon kaunar da nakewa babana sosai.dan haka karya akemin .

Kuma ku masu son batamin suna ina son ku sani cewa annabi Muhammad s.a.w.yace :in duniya zata taru bata ISA ta daurawa bawa abunda Allah bai dauramasa ba na masifa ko alkairi haka kuma yace in da duniya zata taru bata ISA ta daukewa bawa abunda Allah ya daurawa bawansa na masifa ko alkairi.dan haka na dogara ga Allah kuma zai kare ni a bisa sharrin da kukemin iri iri akan buhari.sannan naji kunce na tuba wai na dena adawa da buhari ko ?to shima karya kukemin.ni yanzu ma na fara adawa dashi indai akan siyasa ne ,nagode.

daga ummi ibrahim(zeezee)""

Bana Jin Tsoron Ka Kore Ni A Kannywood - Inji Umma Shehu

Ibrahim Auwal | June 24, 2018 | 0 Comments

Jaruma fina-finan hausa na dandalin Kannywood, Umma Shehu, ta shirya saka wando daya da mai yi mata bita da kulli a masana'antar fim.

Duk da cewa bata bayyana suna wanda take mayar ma raddi, jarumar ta bayyana cewa baza ta damu ba idan har aka kore ta daga Kannywood.

A sakon da ta wallafa a shafin ta na kafar sada zumunta, tauraruwar fim ta bata boye irin rashin mutunci da zata iya yi ga wanda ke neman fushin ta.

Tana mai cewa " Na fika rashin mutunci kuma ni da kake kallo bana tsoron kowa sai Allah ".
Ga cikakken sakon da ta fitar kamar haka;

"Babu abunda yadameni dakai idan kaga dama kasa a koreni a kannywood dan nasan bakaine me bada daukaka ba allah ne dan haka wallahi nafika rashin mutunci nida kake kallona bana tsoran kowa sai allah ni ummah Shehu nafi karfin nabaka hakuri batare da namaka laifiba dan kasa anyi dcasting dina saime kamanta da allah shine meyi kafin kaima kanka ai ammaka dan haka bacire ni yakamata ayiba korana yakamata kayi nonsense nibazansa hoto ina fadanci ba don babu abunda nake nema agun kowa sai gun Allah kaje katambayi waye ummah shehu za’agayamaka irin rashin mutuncin dazanyi kuma idan katashi tambaya kazo unguwarmu katambaya anan ne zakaji ainihin halin ummah babu wanda ya isah naime fadanci idan ina sonka Ina sonka idan bana sonka bana sonka ni haka nake dan haka to hell with you ".

Lamarin dai ya jawo cece-kuce tsakanin masoyan ta masu bibiyan shafinta. Wasu sun bada ra'ayi na tayi hakuri kar ta dauki mataki.
Haka kuma wasu na ganin dai-dai ne idan ta nuna ma wanda ke neman ta da mummunar harka halin ta na rashin mutunci domin kauce ma faruwar haka nan gaba

Daga: Pulse Nigeria

Sabuwar Waka Da Mawaki Rarara Ya Sakewa Shugaba Mai Taken Buhari Karshen Zance

Ibrahim Auwal | June 23, 2018 | 0 Comments

Dauko Sabuwar Wakar da Akayi wa Shugaban buhari ...

Taken Wakar Shine Baba Buhari Karshen Zance

Download Now

Wata Mata Tace Sirikin Dangote Yayi Mata Ciki Kuma Ta Haihu

Ibrahim Auwal | June 22, 2018 | 0 Comments

Wata uku kenan bayan daurin auren Fatima Dangote tare da mijinta Jamil Abubakar Wata Mata Tace Mijin Yarinyar Dangote Yayi Mata Ciki Kuma Ta Haihu.

Irene Chiamaka Nwachukwu, wacce aka fi sani Da Goddess_Irene a Instagram tace ta samu lawya Wanda zai kare mata domin Jamil Abubakar ya dauki nauyin yaron.

Tace Jamil Abubakar yace mata zai dunga bata dubu arbain kowanne wata 40K domin ciyarda da yaron Ko Kuma ta karbi milyan biyar gabaki daya amatsayin kudin biya ta gabaki daya ..

Fatima Dangote Yarinyar Shaharren Mai Kudin bakar fata gabaki daya Aliko Dangote shi Kuma Jamil Abubakar Matukin jirgin sama Ne, baban Sa Kuma tsohon shugaban Yan Sanda Na Kasa Gabaki Daya Muhammad Dikko Abubakar.

Wata Uku Da Suka Wuce Anyi bikin Su Manyan Abokanan Arziki Sun Hallarci bikin nasu harda Mai Kudin Duniya Na Biyu Bill Gate .

Dauko Sabuwar Waka Da Akayi Ma Gwamnan Kano Mai Taken Baza'a Kuma Zaben Ganduje Bah

Ibrahim Auwal | June 21, 2018 | 0 Comments

Dauko Wakar Da Akayi Ma Gwamnan Kano Ganduje Mai Taken Baza'a Kuma Zaben Ganduje.

Dauko Wakar Domin Ji

Download Now

Abinda Yakamata Ku Sani Game Da Zuwan Ali Nuhu Kasar Russia

Ibrahim Auwal | June 20, 2018 | 0 Comments

Abinda Yakamata Ku Sani Game Da Zuwan Ali Nuhu Kasar Russia

Sarkin Kannywood ya hadu da shahararen mai tsaran ragar kungiyar Real Madrid, Kaylor Navas, tare da da wasan kungiyar Arsenal, Joel Campbell.

Yan wasan Costa rica da jarumin ya hadu dasu basu yi nasara kubutar da kasar su wanda abokan adawar su suka yi nasara.

Tauraron fim ya hadu da sune bayan wasan su da kasar Sweden wanda aka tashi 1-0 a madadi Sweden.

Gabanin wannan saduwar, jarumin ya kalli wasan Nijeriya kai tsaye daga filin Kiliningard.

Kafin a fara wasan, ya hadu da yan wasan Super eagles, Abdullahi Shehu da Ahmed Musa inda ya saka hoton siu tare tare da yi masu fatan samun nasara

Sai dai Nijeriya bata yi nasara a wannan wasan ba domin, abokan wasan su Croatia ta lallasa su da kwallo biyu a raga.

Gasar na cigaba da gudana har yau kuma Nijeriya na shirin karawa da kasar Iceland ranar 22 ga wata wasan su na biyu a gasar.

Kalli Hotunan Fatima Ganduje Tare Da Mijinta Lokacin Bikin Sallah

Ibrahim Auwal | June 18, 2018 | 0 Comments

Kalli Hotunan Shagalin Sallah Da Fatima Ganduje Tayi Tare Da Mijinta A Wata Kasa Ta Spain

Ga Hotunan

Marigayya Hauwa Maina Ta Samu Jika

Ibrahim Auwal | June 17, 2018 | 0 Comments

Fitacciyar jaruma kuma furodusa Hauwa Maina, wadda Allah ya yi wa rasuwa a ranar 2 ga Mayu, 2018, ta samu jika, domin kuwa diyar ta Maryam ta haihu a jiya.

Da ma mujallar Fim ta ruwaito a lokacin da ake jimamin rasuwar Hauwa cewar Maryam Bukar Hassan ta na dauke da tsohon ciki.

Maryam ta haihu jiya Talata, 12 ga Yuni, 2018 a garin Kaduna, kuma ta samu da namiji lafiyayye.

Wata kwakkwarar majiya ta shaida wa wakilin mu cewa ita ma maijegon lafiyar ta sumul.

Tun lokacin da ta baro Abuja inda ta ke aure ta zo Kaduna domin karbar gaisuwar rasuwar mahaifiyar ta, Maryam ta ci gaba da zama a gidan kakar ta (mahaifiyar Hauwa), ta na goyon ciki.

Ana sa ran za ta ci gaba da zama a Kaduna har zuwa lokacin da za ta yi arba'in, kafin ta koma gidan mijin ta, Umar Ahmed Zuruq, a Abuja.

A wani sako da ta rubuta a shafin ta na Instagram, Maryam ta bayyana farin cikin samun wannan k'aruwa da ta yi. Ta ce kakar yaron ta so ta yi tozali da jikan nata, to amma Allah bai kaddara hakan ba.

Ta bayyana wannan haihuwa a matsayin wani babban abin farin ciki da ya same ta a daidai lokacin da ta ke cikin jin zafin rabuwa da mahaifiyar ta.

Mu na addu'ar Allah ya raya abin da aka samu, ya ba Maryam cikakkiyar lafiya, kuma ya jikan Hauwa Maina, amin.

Daga : Fim Magazine

Sani Danja Da Matar Sa Mansura Isah Sun Ba Mara Da Kunya

Ibrahim Auwal | June 14, 2018 | 0 Comments

Tabbas, Sani Danja da Mansura Isah sun ba Mara 'da kunya. Domin sun yi abinda ba'a taba zaton zasu yi ba.Ko da yake wasu hangen nesa sun gano hakan zata iya faruwa. Ina magana ne akan auren da suka yi tun shekarun baya. Wasu suna ganin kamar auren ba zai jima ba za'a rabu. Said kuma ga shi Allah ya yi ikonsa har yanzu suna tare.

Abin burgewa shine yanda kullum su kara son juna. Duk da 'yayayen da suka tara bai hanasu soyayya ba. Suna Son junansu.

Ranar da akayi murnar shagayowar ranar da aka haifi Junior Yakubu Sani Musa Danja, a ranar duk wanda yaga Danja da Mansura Isah sai ya tabbatar suna son juna.

Wannan ma ya is a hujja ga masu zargin 'yan fim basa auren 'yar fim. Sabida tanbadewa da suke yi tun adatsa. Wannan Sani Musa Danja da Mansura Isah ya tabbatar mana ba haka bane.

Domin idan da hakane da Danja bai auri Mansura ba, kuma da Marigayi Ahmed S Nuhu da bai auri Hafsat Shehu ba.
Akwai 'yan fim mata masu tarin yawa wanda suka Auri 'yan fim kuma har yanzu suna tare.

Dan haka muna yiwa Maigida masharin kukan mu Sani Musa Danja da matar Anty Mansura mai kula da bukarmu ta kaiwa maigidanmu ubangidan mu Danja da ya share mana hawaye fatan alkairi, Allah yasa mutuwace zata raba.

Idan Ba'a Kiyaye Ba Kannywood Zata Iya Shiga Tsaka Mai Wuya - Zaharadden Sani

Ibrahim Auwal | June 12, 2018 | 0 Comments

A hira da PREMIUM TIMES ta yi da fitaccen dan wasan fina-finan Hausa kuma Furodusa a farfajiyar Kannywood, Zaharadden Sani, ya bayyana mana yadda farfajiyar ke a sannu-sannu neman ta fada halin kaka ni kayi saboda masifar ‘yan fashi teku’ wato ‘Piracy

Zaharadden ya koka kan yadda waddan dabi’a na ‘yan fashin teku ke neman ya dukusar da farfajiyar fina-finan Hausa.

Ina so in gaya maka cewa tabbas idan fa ba’a yi wani abu akai ba toh ko Allah ya kiyaye zamu fada cikin tsaka mai wuya.

Yanzu abin ya baci sai kaje kasuwa kaga babu sabbin fina-finai. Ko kuwa kaga an dade da fidda fim a Sinima amma shiru ba ka gan shi a CD ba. Toh babban dalilin kuwa shine maganan wadannan muggan Mutane. Basu da mutunci ko kadan. Da zarar an saki fim sai su je su buga shi iya yadda suke so su fara sai da shi naira 50 zuwa naira 100 a fim din da Furodusa ya kashe miliyoyin naira.

Wani abin takaici ma shine har ta waya ana tura fim kan naira 20 naira 50. Saboda Allah da me wannan yayi kama?

Sai kaga yanzu Ka kashe makudan kudi wajen shirya fim amma uwar kudin ma ta fito babu ballantana a ce wai har an samu riba.

Yanzu haka kawai ba za ka fidda kudi ka kashe wa fim ba bayan kasan baza ka sami riba ba. Biyan jarumai ma ya zama sai a a hankali, Ko sai kayi kaffa- kaffa tukuna in ba haka ba kuwa ka kira wa kan ka ruwa. Kana gani kiri-kiri wani na kwankwadan romon wahalar ka saboda bala’in irin wadannan mutane.

Zaharadden ya kara da cewa ita kanta Sinima da suke nuna fim din abin dai sai a ahankali, domin ba kowa bane zai iya fidda kamar naira 1000 zuwa sama ya shiga kallon fim daya.

Kaga shi Sinima yana da kyau sai dai masu kallon fina-finan mu da yawa ba za su iya biyan irin wannan kudi ba na shiga kallo abin sai kaga dakyar ko tanan ma ake fita.

Abu daya da zai taimaka wa wannan farfajiya sannan ya ceto mu daga gangarawar da muke yi, shine fa a samu a giggina gidajen kallo masu saukin kudi da mai sai da ruwa, dan achaba, mai keke Napep zai iya shiga ya kalla da dan naira 100n sa. Kaga hakan zai taimaka wajen samun isar da fina-finan mu duk inda muka so ya isa kuma ba za a fadi ba.

Amma tabbas idan ba haka muka yi ba toh fa kaico abin sai du’ai fa. Ba za ka iya sakin fim a CD ba kai kuma ga dukiyar a make a cikin fim din.

A karshe Zaharadden ya bayyana cewa mafi yawan su sun fara karkata zuwa yi wa tashoshin nuna finafinan ta satalat,inda sukan siya fim din idan yana kyau sannan ya cika sharuddan su su nuna a gidajen talabijin din su. Abin fa ya kai ga haka.

Dole ne fa sai gwamnati da masu hali sun sa mana hannu wajen giggina irin kananan wuraren kallon fina-finan a fadin kasar nan idan dai ana so a sai nasara wadannan miyagun mutane da sannan muma mu sami riba a kan sana’ar mu.

Ina Son In Auri Jaruma Fati Washa Inji Nuhu Abdullahi

Ibrahim Auwal | June 12, 2018 | 0 Comments

Ina Son In Auri Jaruma Fati Washa Inji Nuhu Abdullahi

Shahararren Jarumin nan na Kannywood, Nuhu Adullahi ya kasance daya daga cikin yan wasan da suka shiga farfajiyar shirya fina-finan da kafar dama.

Cikin dan kankanin lokaci da shigarsa harkar jarumin ya samu tarin daukaka da nasarori inda har yayiwa wasu da riga shi shiga harkar zarra.

A wata hira da jarumin yayi da jaridar Premium time ya bayyanawa duniya irin son da yake yiwa jaruma Fati Washa kuma har ya jaddada cewan shi zai iya auren ta.

Da aka tambaye shi jarumar da ta fi burge shi a masana’antar yace: “ Fati Washa a koda yaushe itace zabina bazanyi nadama ba inma furta cewa ina sonta.”

Jarumin ya kara da cewa ita din ta musamman ce,ta kasance tana kyautata min tabbas zan iya yin komai dan ganin nima na kyautata mata dan tana da saukin kai ga girmama manya.

Jaridar ta kara yi masa tambaya da cewa meyasa ka zabi Fati Washa ita kadai acikin duk ‘Yan matan Industry,

Sai yace “kamar yadda na gaya maka bazan iya bayyana maka yadda make jiba.

“Amma ina matukar mutunta ta duk da ina da kawaye irin su Rahama Sadau da sauran su."

Da aka tambaye shi ko zai iya auranta yace: “Tabbas in haka ta faru zanji dadi,in mutum ya kyautata maka zaifi kyau shima ka kyautata masa.”

Daga: Naij Hausa

Da gaske ne Mawaki Rarara ya ci Kudin Mawaka?

Ibrahim Auwal | June 11, 2018 | 0 Comments

Da gaske ne Rarara ya ci Kudin Mawaka?

MAI DOKAR BARCI

Rarara Mai Zagin Barayin Gwamnati, Ya Yi Sama Da Fadi Da Sama Da Naira Milyan 100 Na Kungiyar Mawaka

Sanin kowa ne mawaki Dauda Kahutu Rarara ya kware wajen yin hannun ka mai sanda a duk lokacin da aka ce an zargi wani jigo na jam'iyyar adawa da wawushe dukiyar kasa, inda yake fitar da sabuwar waka kan wanda ake zargi da handame dukiyar kasan.

Saidai a yanzu halin da mawakin ke ciki kan zarginsa da ake yi na yin sama da fadi da kudin kungiyar mawakan Arewa wato AMFO, za mu iya cewa mai dokar bacci ya buge da gyangyadi.
Kungiyar dai tana zargin Rarara ne da yin sama da fadinda sama da naira milyan 100 wanda kungiyar gwamnonin Arewa ta ba su.

Rahotanni sun nuna cewa mawaki Rarara ya gina filin kwallo ne a kauyen su Kahutu dake jihar Katsina, sannan kuma ya kafa makarantar kwallo wanda ake zargin duk da kudin kumgiyar ta mawakan ya gina.

Haka kuma wata majiya ta kara da cewa ko lokacin da Gwamna Masari ya ga katafaren filin kwallon da Rararan ya gina, sai da ya kwabe shi kan yadda aka yi ya samu kudin gina irin wannan fili.

Daya daga cikin mawakan da aka yi fadi tashi da shi wajen kare martabar APC, Abubakar Sani ya bayyanawa RARIYA cewa kusan mawaka dari biyar da suka bada gudummawa wajen nasarar gwamnatin APC wadanda suke amfana da gwamnatin ba su fi mutum biyu zuwa uku ba.

Abubakar Sani ya kara da cewa dama ya tabbatar da cewa irin wannan ranar tana nan tafe, ya san da cewa akwai wadanda suke amfani da suna mawakan APC suna cin kudi.

"Idan ka duba da yawa daga cikin mawakan da aka yi wakar "Lema Ta Yage"da su, duk sun dawo daga rakiyar Rarara saboda yadda yake amfani da sunansu yana bin manyan jiga-jigan APC yana karbar kudi".

Abubakar Sani ya kara da cewa wani kuskure da aka samu kan badakar kudin shine rashin samarwa kungiyar asusun ajiya, inda Rararan ya dinga amfani da asusun ajiyarsa wajen ajiye kudin.

Shugaban kungiyar mawakan na yankin Arewa Haruna Aliyu Ningi dake jihar Bauchi ya bayyanawa manema labarai cewa yace Gwamnan jihar Zamfara ya ba su kudin bayan sun bukaci hakan kan irin gudummawar da suka bayar a yayin zabukan 2015, kuma sun shirya bayar da gagarumar gudummawa a zabukan 2019 dake tafe.

Tunda farko Dauda Rarara shiya shige gaba wajen karbo kudaden kuma ya tabbatar mun da cewar Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya fara basu nera Milyan Sittin sai dai wadanda suka yi hanya har aka bayar da kudaden ya ba su nera milyan goma sha takwas kamar yadda Haruna Ningi ya kara da bayyanawa.

Ya kara da cewar "a matsayina na shugaban kungiya har zuwa yau Rarara bai taba yi mun maganar ba, bayan lokacin da na sake tuntubar sa, sai yace har yanzu ba a cika ragowar kudaden ba, amma na kusa da shi wanda shi ma yana daga cikin mawakan mai suna Isiyaku Oris yace tuni an baiwa Rarara ragowar nera milyan arba'in din.

"A hakan dai muka bukaci nera milyan arba'in da biyu da suka rage a hannun shi ya kawo su a zo a zauna a tattauna a kan su sai yace wai asusun ajiyar sa na banki ya sami matsala".

Manazarta dai na ganin cewa tun bayan da mawakin ya yi wakar habaici ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso farin jininsa ya soma raguwa, inda ko ya yi sabuwar waka ba ta tasiri kamar a baya.

Har ya zuwa yanzu dai mawaƙin bai ce komai ba, game da zargin da ake yi masa. Sai dai ana tunanin da ya dawo daga aikin Umarar da ya tafi zai maida raddi a kan maganar, walau ta hanyar kare kan sa a kafafen watsa labarai ko kuma ta fannin waka.

Daga:
Aliyu Ahmed

Da:
Rumbunkannywood

Mawaki Rarara Ya Saki Sabuwar Waka Mai Taken Sai Kayi Takwas Baba Buhari 2019

Ibrahim Auwal | June 11, 2018 | 0 Comments

Shahararren mawaƙin siyasar nan wato Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ya fitar da sabuwar waƙa mai taken "Sai Ka yi Takwas PMB".

Ita dai waƙar mawaƙin ya yi ta ne domin maida martani ga wasu 'yan majalissun Nijeriya, wadda wata majiya ta ce suna ƙoƙarin tsige Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga muƙami.

A cikin waƙar, mawaƙin ya bugi jaki, sannan kuma ya bugi taiki, game da ƙudirin na 'yan majalissar. Za ku iya downloading ɗin waƙar a wannan link ɗin da ke ƙasa

Download Now

Daga: rumbunkannywood

Abinda Yake Hana Cigaban Kannywood Kenan Inji Nafisa Abdullahi

Ibrahim Auwal | June 10, 2018 | 0 Comments

Ganawar da jaruman masana'antar Kannywood suka yi da shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Bukola Saraki da jarumi Ali Nuhu ya jagoranta tare da wasu taurarin fina-finan Hausa ta jawo cece-kuce tsakanin wasu manyan jaruman masana'antar.

Kamar dai yadda muka samu, wasu jaruman na ganin an saka siyasa tsagwaron ta musamman ma ganin cewa wadanda suka wakilci masana'antar musamman ma ta bangaren mata ba wasu fitattun jarumai bane da aka sani.

Majiyarmu ta samu cewa daga cikin wadanda suka nuna rashin jin dadin su game da hakan hadda Rahama Sadau da kuma Nafisa Abdullahi.

Ita dai Rahama Sadau ta yi magana me kama da shagube a dandalinta na sada zumunta na Tuwita inda ta bayyana cewa, shugaban majalisar tarayya, Bukola Sataki ya gana da sarkin mu da kuma wasu 'fitattu' daga masana'antar Kannywood a bangaren mata dake jan ragamar masana'antar fina-finan Hausa.

Nafisa Abdullahi ta mayar da martani akan wannan batun inda tace ita ba tasan wadannan matan ba ma amma gasu nan da su aka je.

Jarumar, Nafisa ta kara da cewa, babu ta yanda za'ayin masana'antar ta cigaba idan babu hadin kai da gaskiya a tsakanin su, wannan abin kunyane.

Daga nan ne sai Rahama ta kara da cewa, "a gaskiya nayi tsammanin ganin Jamila, Nafisa, A'isha ko Hadiza a cikin wannan tawagar, amma ni dake mun san yanda masana'antar ke gudana, watakila kamun kafarsune yasa akaje dasu, kinga kuwa dole su wakilcemu."

Daga: Naij Hausa

Za'a Maka Dauda Kahutu Rarara A Kotu Da Zarar Ya Dawo Daga Umrah

Ibrahim Auwal | June 09, 2018 | 0 Comments

An kori Shugaban qungiyar, Haruna Aliyu Ningi

Abubakar Sani zai maka qungiyar a kotu
A yanzu dai rikicin da ya kunno kai cikin qungiyar mawaqan jam’iyyar APC ta arewacin qasar nan da aka fi sani da ANMFO ya dauki sabon salo, inda a yanzu kwamitin majalisar qoli na qungiyar ya kori shugaban qungiyar, Haruna Aliyu Ningi.

Idan ba a manta ba shi Haruna Aliyu Ningi da kuma mawaqi Abubakar Sani ne suka tattauna da jaridar Rariya inda suka yi zargin cewa, fitaccen mawaqin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya yi sama da fadi da kudin qungiyar mawaqan Arewa na jam’iyyar APC (ANMFO) har kimanin Naira miliyan 100 da Qungiyar Gwamnonin Arewa ta ba mawaqan qungiyar a kwanakin baya.

Jaridar ta rawaito cewa mawaqi, Abubakar Sani ya ce kusan mawaqa 500 da suka bada gudummawa wajen nasarar gwamnatin APC, to wadanda suke amfana da gwamnatin ba su fi mutum biyu zuwa uku ba.

Jaridar ta ce, Abubakar Sani ya ce, “Idan ka duba da yawa daga cikin mawaqan da aka yi waqar ‘Lema Ta Yage’ da su, duk sun dawo daga rakiyar Rarara saboda yadda yake amfani da sunansu yana bin manyan jiga-jigan APC yana karbar kudi.”

Abubakar Sani ya qara da cewa wani kuskure da aka samu kan badaqalar kudin shi ne, rashin samar wa qungiyar asusun ajiya, inda Rarara ya riqa amfani da asusun ajiyarsa wajen ajiye kudin.

Shugaban qungiyar mawaqan kafin majalisar ta yi iqrarin korar sa daga qungiyar, Haruna Aliyu Ningi da ke Jihar Bauchi, ya bayyana wa Rariya cewa, Gwamnan Jihar Zamfara ne ya ba su kudin bayan sun buqaci hakan sakamakon irin gudunmuwar da suka bayar a yayin zabukan 2015.

Jaridar ta rawaito cewa Ningi ya ce, tun da farko Rarara ne ya shige gaba wajen karbo kudaden kuma, “ya tabbatar mun da cewar Gwamnan Jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya fara bayar da Naira miliyan 60, sai dai wadanda suka yi hanya har aka bayar da kudaden ya ba su Naira miliyan 18.”

Sai dai a yayin zaman kwamitin majalisar qolin qungiyar wanda aka yi a Kano a ranar Asabar din da ta gabata, majalisar ta yanke hukuncin korar shugaban qungiyar Haruna Aliyu Ningi bisa zargin da suka yi cewa ya canza sheqa zuwa jam’iyyar NNPP.

Wata majiya ta tabbatar wa Aminiya cewa a yayin zaman kwamitin akwai Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Isma’il Na’Abba Afakallah da jarumi Nura Hussaini da sauransu, inda kuma kwamitin nasu ya kuma kori Ibrahim Yala sakamakon zama ummul’aba’isin kitsa duk fitunun da suke damun qungiyar.

A takardar bayan taron da majalisar qungiyar ta fitar a ranar 2ga Yuni, 2018 wanda Alhaji Garba Gashwa ya sa mata hannu, ta bayyana cewa sakamakon zama da Kwamiti na Koli (Board of Trustee) na qungiyar ANMFO ya yi a kan matsalolin da suke damun wannan qungiya ta ANMFO ne, sai majalisar qoli ta dattawa ta samar wa qungiyar matsaya uku.

Takardar ta qara cewa matsaya ta farko ta qunshi korar shugaban qungiyar na qasa, Haruna Aliyu Ningi sakamakon ficewarsa daga jam’iyyar APC ya koma mai Kwando wato NNPP mai kayan dadi.

“Kuma har ya yanki katin jam’iyyar zai yi mata takarar dan majalisar qasa, kuma har ya yi waqoqi na batanci ga ’yan wannan jam’iyya tamu ta APC. Sharadin zama a qungiyar ANMFO shi ne ka zama dan jam’iyyar APC, kuma ka kare mutuncin gwamnoninta da yada muradun shugaban qasa Muhammadu Buhari, wannan dalili ya sa Ningi muka sallame shi.” Inji majalisar.

Majalisar ta qara da cewa matsaya ta biyu da ta cimma ita ce, yanke hukuncin korar mambanta Ibrahim Yala saboda duk fitunun da suke damun qungiyar to shi ne ya qulla su, sannan ya ci gaba da yada su a kafar sada zumunta ba tare da yana da hujja ko makama ba.

Majalisar ta ce, “Sannan (Yala) ya yi qoqarin bata wa shugaban dattawa na wannan qungiya suna da hada fitina tsakanin ’yan qungiya don biyan buqatar kansa da ci wa masu taimaka wa wannan qungiya mutunci da kuma yi musu sharri don bata musu suna. Wannan dalili ya sa muka kore shi.”

Majalisar ta kuma bayyana cewa ta dakatar da mambar qungiyar na Kano, Jamilu Jadda Garko da Ma’aji na qasa na qungiyar, Isyaku Muhammad Forest da Shugaban qungiyar na Abuja, Ahmad Kaka da Shugaban qungiyar na Kano, Jamilu Darmanawa da kuma mamban qungiyar ta Jihar Yobe, Jamilu Roja.

Majalisar ta bayyana cewa an dakatar da su ne bisa wadansu dalilai, inda da zarar an kammala bincike za a sanar da sauran mambobin qungiyar.
Majalisar ta kuma sanar da cewa mawaqi Abubakar Sani da yake ta batatu a kan batun ma ba dan qungiyarsu ba ne.

A lokacin da Aminiya ta tuntubi daya daga cikin wadanda aka kora Ibrahim Yala don jin ta bakinsa, sai ta samu lambobinsa ba sa tafiya, inda bayan Aminiya ta gudanar da bincike ne ta tabbatar da cewa Yala yana qasar Saudiyya don gudanar da Ummara.

Aminiya ta tuntubi Al-Ameen Afandaj wanda shi ne Manaja kuma mai magana da yawun fitaccen mawaqi Dauda Kahutu Rarara kan batun lokacin da mawaqin zai kira taron ’yan jarida don ya yi bayani kan zargin da ake yi masa na yin sama da fadi da Naira miliyan 100, sai ya bayyana cewa mawaqin yana qasar Saudiyya don yin Ummara.

“Rarara yana Saudiyya don yin ummara, amma da zarar ya dawo to zai kira taron ’yan jarida, kuma kai ma kana cikin wadanda za a kira.” Inji Afandaj.

Aminiya ta tuntubi mawaqi Abubakar inda ya tabbatar da cewa shi ba dan qungiyar ba ne, inda a yanzu ya shirya shi da mabiyansu kimanin 300 don maka qungiyar a kotu.

Ya ce, “Mun kai kimanin 300, kuma na shirya jagorantar mawaqan don maka qungiyar ANMFO a kotu matuqar ba su daina kiran kansu qungiyar mawaqan APC na Arewa ba, qungiyar nan gaba daya watanta takwas, sannan indai maganar wadanda suka yi wa APC wahala ne akwai wadanda suka mutu ma, shi ke nan don sun mutu sai a ce babu hakkinsu a cikin tallafin da aka bayar, ba zai yiwu ba, kamar biyan bashi ne, idan har an bada kudin, to ya kamata a ba kowa.”

Ya qara da cewa “ka tuna tun da aka aka ci zabe ba a yi waqa kamar ‘Lema Ta Yage’ ba, don haka wadanda suke cikin qungiyar da aka yi ‘Lema Ta Yage’ da su ba su wuce daga Rarara sai Alfazazee ba, sai kuma irinsu Umar M Shareef, babu ni, babu Adamu Nagudu da Adam A Zango da Hussaini Danko, shi ke nan an bayar da tallafi kan wadanda suka yi wa jam’iyya hidima a 2015 sai a manta da mu? Don haka ba ta zama qungiyar mawaqan Arewa na APC ba.”

Har yanzu ni ne shugaban qungiya – Ningi

A lokacin da Aminiya ta tuntubi Haruna Aliyu Ningi kuwa sai ya ce takardar korarsa da aka fitar daidai take da wasan kwaikwayo, domin wadanda suka zauna har suka zartar da wannan takarda ba wai ’yan asalin qungiyar ANMFO ba ne, ba kuma dattawan qungiya ba ne.

Ya ce, domin asalin dattawan qungiyar babu wanda bai yi magana da shi, kama daga Ibrahim dan dagwas da Shu’aibu dan Midi da Garba Gashuwa, kuma sun ce ba su san komai dangane da takardar ba.

Ya ce, a takardar sun sa sunan shugaban majalisar qoli na qungiyar amma ba shi ya sa hannu ba.

“Abin da ya faru shi ne, an ma tashi daga zama cewa za a kafa kwamiti na mutum biyar don ya duba rikicin qungiyar, an sa ’yan kwamitin su yi bincike, inda kafin wani abu shi aka fitar da wannan sanarwar kora da kuma dakatarwar, an ce za a tattauna komai zuwa bayan Sallah, amma wadansu suka je suka yi gaban kansu, ka ga ya zama wasan yara,” inji shi.

Da Aminiya ta tambaye shi cewa a takardar an yi zargin ya koma jam’iyyar NNPP shi ya sa aka kore shi daga qungiyar, sai ya ce,

“ita ANMFO ba a kafa ta a kan jam’iyyar APC ba ne, an kafa ta ne a kan maganar Buhari ne kawai, ko kana APC ma idan ba ka Buhari to ba za ka shiga cikinta ba, akwai mawaqa ’yan APC ne, amma an qi a sa su saboda ba sa ra’ayin Buhari, irinsu Abubakar Sani da Naburuska da suke Kwankwansiyya an qi tafiya da su, don haka ko ba ka APC idan kana tafiyar Buhari to ka cancanta ka shiga ANMFO.”

Ya jaddada cewa don haka har yanzu yana nan a kan shugabancin qungiya, kuma babu wanda ya sauke shi.

Naira miliyan 20 muka ba qungiyar – Gwamnatin Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bakin mai taimaka wa Gwamna Abdul’Aziz na Jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya ce gwamnati ba ta da masaniya dangane da batun Naira miliyan 100 da ake zargi an ba qungiyar mawaqan.

Ya ce, gwamnatin Jihar Zamfara ta ba qungiyar mawaqan gudunmuwar Naira miliyan 20 ne a lokacin da shugabannin qungiyar mawaqan suka gana da Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’Aziz Yari a kwanakin baya.

Ya qara da cewa gwamnan ya ba da kudin ne bayan mawaqan sun buqaci ya ba su gudunmuwarsa don su bude ofis a Kaduna, sannan kuma su sayi mota.

Dosara ya qara da cewa a yanzu Gwamna Yari ya tafi qasar Saudiyya don yin ummara, don haka batun ko qungiyar gwamnoni ta ba mawaqa miliyan 100 ta hannunsa, to sai ya dawo za a ji bayani.

Daga: Aminiya

Na Cigaba Da Karatu Kuma Zanyi Aure Inji Tsohuwar Jaruma Hafsat Shehu

Ibrahim Auwal | June 09, 2018 | 0 Comments

Allah abin tsoro, duniya kasuwa mai ci tana tana tashi. Hafsat Shehu tana daga jerin kyawawan matan industry, matsawar ana batun kyawawan mata to Hafsat Shehu tana ciki.

Tun bayan rasuwar mijinta Ahmed S Nuhu aka daina jin labarin jaruma Hafsat Shehu. To da yake waiwaye adon tafiyane shine dalilin da yasa mu bin ciko labari inda Hafsat Shehu ta boye tun bayan rasuwar mijinta Ahmed S Nuhu.

Hafsat Shehu tana raye cikin kwanciyar hankali da lumana. Domin yanzu haka tana makaranta ci gaba da karatun ta. Mun zanta da ita ta wayar salula, acikin tattaunawar da muke yi da itane ga sanar mana halin da take ciki.

A cewar Hafsat Shehu: gaskiya yanzu rayuwata ta sauya ba kamar shekarun baya ba. A baya nayi rayu tareda mijina amma yanzu rayuwa nake daga ni sai halina. Yanzu haka ina ci gaba da karatuna kuma na kusa kammalawa.

Ya maganar aure idan an gama makaranta?

Gaskiya tun da na rasa Ahmed bana tunanin wani aure yanzu. Amma da yake ni musilmace dole inyi aure. Dan haka yanzu ma akwai wanda iyayena suke so na aura kuma nima yayi min.

Na ji kamar kina kuka menene dalilin zubar hawayenki?

Wallahi duk lokacin da akayi maganar aure sai na tuna da tsohon mijina wanda zuciyata take so da kauna. Amma mutuwa tayi mana yankan kauna. To mun gode Allah domin wanda ya dauke shi {Allah} ya fi ni son Ahmed.

Yanzu idan kin tashi yin aure wanne irin miji ki ka fi so?

Ni kowanne kala inaso, matsawar yana sona da gaskiya. ba ruwana da kudinsa ko kyan fatarsa matsawar yana da tsafta da rikon addini to ina maraba da shi, koda kaine.

Ni kuma Hafsat? Me hakan ke nufi?

Ji nayi ka damu da maganar aurena nasani ko kawata zaka yi kishiya mu zama mu uku kenan.

Dariya mukayi ni da ita. Haffsat macace mai barkwanci da yawan son raha. Yanzu atakaice Hafsat Shehu tun rasuwar mijinta ba ta kuma yin aure ba. Ta kama mutuncin kanta bata shigar banza bare ayi mata fassara ta daban.

Ku Kiyaye Da Masu Amfani Da Sunana Na Bogi - Inji Hadiza Gabon

Ibrahim Auwal | June 08, 2018 | 0 Comments

Jaruma Hadiza Gabon ta haska wani shafin bogi da aka bude da sunan ta wanda ke rokon jama'a da su tallafa da kudi domin tallafawa mara hali.

Ta nisantar da kanta da shafin tare da yin kira ga jama'a da su kaurace ire-iren shafukan bogi masu bukatar kudi daga masu bibiyan ta.

wannan yana daya daga cikin abubuwa dake ci ma jaruman kannywood tuwa a kwarya shine yawan bude shafukan bogi da sunan su tare da neman kudi daga jama'a ta hanyar da wasu bata gari keyi.

Tauraruwar kannywood tana mai cewa "Wallahi wannan ba ni bace ba pls beware and pls repost #beware » #fraud » #fakeaccount » " kamar yadda ta rubuta a shafin ta na instagram tare da hoton shafin bogi wanda aka bude da sunan ta a facebook.

Daga: pulse Nigeria

[Music] Dauko Wakar Da Akayi Mai Taken Mawaki Rarara Yaci Kudin Mawaka

Ibrahim Auwal | June 08, 2018 | 0 Comments

Tab Anyi Ma Mawaki Rarara Waka Akan Yaci Kudin Kungiyar Mawaka ..

Download Music Now

Daga: presshausa

Dalilin Daya Sa Nake Shigar Kayan Turawa A Wakokina -Adam A Zango

Ibrahim Auwal | June 05, 2018 | 0 Comments

Jarumi mai tauraro yace dabarar yin haka shine domin jawo hankalin samari da yan mata masu kallon wakoki kasar waje da na kudancin kasa zuwa kallon nashi.

Fitaccen jarumin fim kuma mawaki, Adam A.Zango yayi karin haske game da korafe-korafe da jama'a keyi akan kayan da yake sakawa a cikin bidiyon wakokin shi.

A wata hira ta musamman wanda ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunta, Prince Zango ya bayyana cewa ya kan sanya ire-iren kayan zamanin ne domin jawo hankalin jama'a wajen kallon wakokin yan arewa.

"Na san so dayawa mutane sukan yi korafi a irin kayan da nake sakawa a cikin wakoki na na album. Amma abun da nake so ku fahimta shine bazai yiuwu inyi wakar da kalmar hausa kuma idan zanyi shooting bidiyo dinta kuma in saka kaya zalla irin ta hausawa" yace.

Yace dabarar yin haka shine domin jawo hankalin samari da yan mata masu kallon wakoki kasar waje da na kudancin kasa zuwa kallon nashi.

Ya kara da cewa mafi yawanci mabiyan sa masu bibiyan wakokin turawa da na india basu san kalamai da mawakan ke furtawa a cikin wakokin su kuma mafi yawanci kalamai ne wanda bata dace ba wanda bahaushe kuma musulmi ya dinga furtawa.

A cewar sa yana kokari wajen yoin waka cikin yaren hausa kuma ya sanya mata kida irin ta zamani kuma ya sanya kayan zamani a cikin ta domin janye hankalin jama'a zuwa kallon nashi.

Matakin yin haka yunkuri ne na jawo al'ummar arewa wajen yin alfahari da mawakan arewa tare da gina wakoki arewa a cikin yan arewan.

Daga karshe dai jarumin ya sanar cewa kofa a bude take ga duk wanda yake da shawara ko ya gan wani abu wanda bai dace ba.

Jarumin yayi wannan karin hasken ne yayin da yake yi ma masoyan sa godiya bisa karbuwar da kundin wakokin shi mai taken "Mai laya" ta samu.

Martanin Mawakin Hausa Zuwa Ga Maganar Sheikh Gumi Akan Buhari

Ibrahim Auwal | June 04, 2018 | 0 Comments

Mun zabi zama jahilai a karkashin Buhari da zama masu ilimi a karkashin barayi, Saeed Nagudu ya mayarwa da Sheikh Gumi martani

Tun bayan da Shehin malamin addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari sanadin kamun da EFCC tawa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Muktar Ramalan Yaro, wasu sun rika mayarwa da malamin kalamai masu zafi a yayin da wasu suka goyi bayanshi, tauraron mawakin Hausa, Saeed Nagudu shima ya mayarwa da Malamin martani.

Saeed yace, Malam Gumi, mun zabi mu zama jahilai magoya bayan Buhari fiye da zama masu ilimi a karkashin barayi.

Daga: Presshausa

Kalli Bidiyon Dan Fashin Daya Ce Su Yaran Sanata Bukola Saraki Ne

Ibrahim Auwal | June 04, 2018 | 0 Comments

Hukumar Yan Sanda Nijeriya Sun Saki Wani bidiyo Wanda Dan Fashi  bankin Offa Da Ake tuhuma Mai Suna AY Yace Shi Yana Ma Sanata Bukola Saraki Aiki Ne .

Danna Download Domin Dauko Bidiyo

Download Now

Babu Jarumar Kannywood Da Zata Iya Fice Kamar Rahma Sadau

Ibrahim Auwal | June 04, 2018 | 0 Comments

Babu Jarumar Kannywood Da Zata Iya Fice Kamar  Rahma Sadau

Rahama Sadau wata Jaruma ce a kasar Najeriya wadda tayi fice wajen a fannin wasan kwaikwayo na masana’antar Kannywood. An haifi Sadau a ranar 7 da watan Disamba na shekara ta alif dari tara da casa’in da uku (7 December 1993) a unguwar Sarki dake cikin garin Kaduna na Jihar ta Kaduna a Najeriya.

Ta shiga masana’antar Kannywood a shekarar 2013. Sadau ta kasance daya tilo wajen tafka mahawara a cikin yaren Hausa, Turanci da Indiyanci baki daya. Jaruma Sadau ta samu fice bayan fitowar ta a wani shiri mai suna “Gani Ga Wane” tare da Jarumi Ali Nuhu.

Duk da dai cewar Jaruma Rahama Sadau ta samu fice a ita masana’antar ta Kannywood, sai dai kuma a ranar 2 ga watan Oktoba na wannan shekata ta dubu biyu da sha shida (2 October 2016) kungiyar MOPPAN ta samu dakatar da Jarumar kasancewar samunta da laifin rungumar wani mawaqi a wani faifan bidiyo mai suna ClassiQ wanda ya fito daga yankin Jos na jihar Filato a Najeriya. Ita dai wannan dakatarwa bata samu cirewa ba har a yanzu inda wadansu kan kalle ta a matsayin kora gaba daya daga cikin masana’antar.

Kungiyar MOPPAN tayi tsokaci da cewar rungumar da Jarumar tayi ya saba tarbiya da tsari irin na duk wani mai yin shirin fim na Hausa. Sai dai korar Jaruma Rahama Sadau bai hana fina finai masu hoton ta fita ba duk da cewar masu wallafa shirin na fina finan basu ci gaba da sakata ba a cikin shirin sabbin fina finai. Hakan kuwa tana faruwa ne sakamakon cewar akwai fina finai da dama wadanda Jaruma Sadau take cikin su da basu samu fita ba a kasuwannin fina finai a lokacin da akayi kata ita waccan kora.

Duk Da Hakan Kamfanin Google Suna Nuna Cewa Anfi Duba Labarin Rahma Sadau Fiye Da Sauran Jaruman A Lokacin Da Majiyarmu Ta Duba.

Hakan Yasa Jarumar Ta Samu Kyautuka Da Da-ma  Daga Kamfani Da Kuma Masu Bada Award Wasu Sunce Mah Korarta Kannywood Albarka CE Agareta Domin Ya Kawo Mata cigaba Ciki Sauri Fiye Da Sauran Jarumai Mata Na Kannywood.

Akwai Manyan Mata Irin Su Hadiza Gabon,Nafisa Abdullahi Wanda Sunfi Ta Dadewa Amma Ta Kera Su Wajan Fice Duk Da Yanzu Suma Sun Koma Fim Din Kudancin Nijeriya.

Rahma Sadau Yanzu Na Koma Abun Koyi Ga Manyan Mata A Arewacin Nijeriya Inda Manyan Gidan Jarida Na Leadership Sun Kira Sunanta Amatsayin Jaruma Mai Jarumta Da Kuma Gwazo Inda Har Ta Samu Kyautar babbar jaruma ta Kannywood.

Wasu Suna Ganin Cewa Ilmin Ta Shine Ya Taimake ta Sosai Wajan Kara Kaita Sama Sosai.

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger