Diyar Shugaban Kasa Buhari Ta Haihu A Wata Kasa

Ibrahim Auwal | July 10, 2018 | 0 Comments

'Yar gidan shugaban kasa Buhari ta haihu a kasar Andalus

Kimanin watanni goma sha takwas da bikin yar gidan shugaban kasa Muhammad Buhari wato Zahra Buhari, wani rahoto da ya riske mu yanzu daga kafar sadarwa ta yanar gizo ta kikiotolu, ya bayyana cewa 'yar shugaban kasar ta haifi santalelen jaririnta cikin koshin Lafiya, a wani asibiti da ke kasar Spain.

Wata Majiya daga zuri'arta, sun bayyana yadda wannan haihuwa ya sanya farin ciki a tsakaninsu.

Idan za'ai iya tunawa dai a cikin Shekarar 2016 ne, Zahra Buhari ta auri Ahmed Indimi dan gidan babban attajiri nan Alh. Mohammed Indimi.

Daga: Naij Hausa

Tsoron Zaman Kashe Wando Ya Sanya Ni Shiga Harkar Fim - Adam Zango

Ibrahim Auwal | July 08, 2018 | 0 Comments

Wato jarumi Adam A Zango wanda akafi sani da suna Yarima, wanda ya bayyana mana cewa rashin aikin yi ne ya shigar dashi masana’antar fina finai bayan da ya kammala karatun sa.

Yarima dai yace bayan gama karatunsa na sakandare ne yayi tunanin maimakon ya zauna (zauna gari banza), sai yaga ga sana’ar da ta dace da shi kuma zai iya yinta kasancewar yayi wasanni da kade-kade da raye-raye a makaranta.

Tun dai shekara ta 2001 wato shekaru goma sha uku kenan da suka wuce Adam A Zango ya fara aikin yin fina finai.

Alokacin da Adam yazo masana’antar hada fim ya fara koyar kida a dalilin rashin samun shiga fim, inda ya fara koyar kida a gurin Ibrahim Danko har ya kware, hakan ne yasa ake ta neman sa domin yayi waka Allah kuma ya bude masa domin duk wakar yayi sai ta karbu.

Daga baya bayan ya rasa wanda zai saka shi a fim sai Adam A Zango, ya fara tara kudin sa da niyyar yim fim dinsa na kansa, ya kuma nemi abokansa dake yin sana’ar har suka nemo labari da darakta da jarumai aka biya su suka fara aikin fim din har ya kammala, fim din mai suna “Sirfani” shine fim din san a farko.

Bayan fitowar “Sirfani” ne wasu daga cikin masana’antar ne kamar su Ali Nuhu da Naja CSB Jakara da Bauni suka gano cewa lallai wannan zai iya cin abinci a wannan harka, daga nan dai suka fara saka shi cikin wasannin su

Allah kuma ya daukaka shi. Cikin fina finan da yayi “Ahalil Kitabi” itace ya kira bakandamiyar sa.

Daga: DandalinVoa

Dauko Wakar Da Akayi Ma Gwamnan Kano Ganduje Mai Taken Baza'a Kuma Zaben Ganduje

Ibrahim Auwal | July 02, 2018 | 0 Comments
Dauko Wakar Da Akayi Ma Gwamnan Kano Ganduje Mai Taken Baza'a Kuma Zaben Ganduje.
Dauko Wakar Domin Ji

Babu Abinda Kiristanci Ya Tsinanamin, Inji 'Yar Tsohon Gomnan Oyo.

Ibrahim Auwal | July 02, 2018 | 0 Comments

Babu Abinda Kiristanci Ya Tsinanamin, Inji 'Yar Tsohon Gomnan Oyo.

Sananniyar 'yar jaridar nan me yawan jawo cece-kuce kuma diya a gurin tsohon gwamnan jihar Oyo, Kemi Olunloyo ta bayyana sha'awarta da shiga addinin musulunci, tace babu abinda addinin kiristanci da take kanshi a yanzu ya jawo mata banda dimuwa da rudani.
Kemi ta bayyana hakane a wani rubutu da tayi a dandalinta na sada Zumunta da muhawara inda ta sanya hotunan ta sanye da Hijabi sannan ta rubuta cewa:
Kwanannan zata karbi addinin musulunci, kuma a da ta kasance tare da kakarta wadda ta rasu tana da shekaru dari da biyu a Duniya, makarantar da take zuwa kusa da gidan kakartane shi yasa ta koma can da zama, su kanyi sallah sau biyar a rana ba sau daya a sati ba kamar yanda take yi tare da shaidanun mutane yanzu ba, tace, suna shagulgulan sallah babba da karama tare.
Tace Musulunci addinine na zama lafiya kuma a cikinshine zata samu nutsuwa.
Ta dai karkare zancenta da cewa, yanzu babu ruwanta da addinin kiristanci, dan kuwa babu abinda ya tsinana mata a rayuwa banda rudani, musulunci zata koma kuma duk wanda baya son addinin musulunci sai ya dena bibiyarta da lamurranta, komai yana da lokaci dama, yanzu dai ta tabbata cewa a addinin musuluncine zata samu nutsuwar da take nema.

Zan Iya Kayar Da Shugaban Buhari Idan PDP Zata Zabe Ni - Kwankwaso

Ibrahim Auwal | July 01, 2018 | 0 Comments

Rabiu Musa Kwankwaso, daya daga cikin jiga jigan jam'iyyar APC wanda ke ware kanshi daga jam'iyyar mai mulki, yace za a kada shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 mai tunkarowa.

Ya bayyana jam'iyyar PDP a matsayin jam'iyyar da tafi adawa da APC kuma mai karfin kayar da shugaban kasan a zaben mai zuwa, wanda za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.

Ya kara da cewa, shine Dan takara mafi cancanta da zai iya rike tutar jam'iyyar kuma yaci zaben shugabancin kasar.

Kwankwaso, Sanata ne mai ci a yanzu kuma tsohon gwamnan jihar Kano, yana yawan ikirarin cewa da taimakon shi Buhari ya samu kuri'u miliyan 1.9 a jihar tashi. Ya kuma taimakawa gwamna Umar Ganduje, mataimakin shi a lokacin da ya rike Gwamnatin jihar, cin zaben 2015.

Wannan sukar jam'iyyar APC ta fito ne bayan kwanaki kadan bayan da yaki halartar zaben jam'iyyar da akayi a Abuja. Wannan ya faru ne sakamakon fadan da ke tsakanin magoya bayan shi da na gwamna Ganduje, wanda duk haduwar su sai sun raba abin fadi.

Daga : Naij Hausa

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger