Na yi wa matata karyar na mutu saboda yawan tambaya na Kudi da take yi>>Magidanci

Ibrahim Auwal | August 31, 2018 | 0 Comments

Wani mazaunin kasar Amurka kuma dan kasar Honduras mai suna Danny Gonzalez ya karyata mutuwar sa domin guje wa yawan bani-bani daga wurin matar sa.

Gonzalez na daya daga cikin ‘yan kasar Honduras da iyalen su ke dogaro da su sanadiyyar zaman da suke yi a can kasar Amurka.

Gonzalez ya ce tun da ya koma zama a kasar Amurka matar sa ta zama aljihu da kulum sai dai a zuba masa kudi.

” Duk ranar Asabar matata kan kira ni a waya sannan duk kiran da za ta yi mun na tambayar kudi ne daga nan kuma babu abin da zai sake hada ni da ita.

” Ganin yawan bani-bani din da matata ke yi ya ishe ni sai na dauki wannan mataki na in karyata mutuwa ta.

Ai ko bayan ya aika mata da hotunan sa kwance kamar gwa, sai ko ‘yan uwansa suka rude, suka fara neman yadda za suyi su tabbatar da haka. Jaridu suma basu bar maganar ta wuce haka kawai ba.

Daga baya sai aka gano cewa ashe bai mutu ba yana nan da ran sa lafiya sumul.

Matar sa ce kawai ya nemi ya tada wa hankali ko ya huta da tambaya.

Daily Trust ne ta ruwaito wannan labarin.

An kama barauniyar da ke yi wa ‘yan acaba tayin alawa, da sun sha sai su mika mata mukulli

Ibrahim Auwal | August 31, 2018 | 0 Comments

A yau Alhamis ne rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wata barauniya mai suna Zinatu Abubakar da laifin sace babur.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Gambo Isa ya sanar da haka wa manema labarai a garin Katsina.

Ya ce Zinatu ta hau babur din wani mutum mai suna Gide Wada cewa zai kai ta rukunin gidajen unguwar Rima dake cikin garin Katsina daga Kofar Kaura inda ta tsayar da shi.

” Sai Zinat ta yi wa Wada tayin alewar chakulat yayin da suka fara tafiya ai ko bayan ya gama tsotsan wannan alewar sai ya fara ganin jiri.

” Sanadiyyar haka sai Wada ya tsayar da babur amma kafin ya ankare wasu abokan Zinatu masu suna Abubakar da Chairman suka diran masa inda suka yi korarin kwace babur din da karfin tsiya.

Da Wada ya ga bazai iya da su ba sai ya kwantsama ihu nan-nan ko mutane suka kawo masa agaji.

Isa ya ce mutanen sun cafke Zinatu sannan Abubakar da Chairman suka tsere.

Ya ce bincike ya tabbatar musu cewa Zinatu da abokanta na cikin wata kungiyar ‘yan bata gari dake sace wa ‘yan achaba babura kuma an gano sun dade suna aikata wannan ta’asa a Kaduna da Kano.

A karshe Isa ya yi kira ga duk ‘yan achaba da su guji karban abinci daga hunnun mutanen da basu san su ba.

Ya ce rundunar ta fara farautan Abubakar da Chairman don gurfanar da su.

Premiumtimeshausa.

Idan Akwai Wata Cuta Da Allah Ya Dora Min A Doron Kasa, Ba Ta Wuce Soyayyar Kwankwaso Ba Inji jarumi Naburaska

Ibrahim Auwal | August 31, 2018 | 0 Comments


Idan Akwai Wata Cuta Da Allah Ya Dora Min A Doron Kasa, Ba Ta Wuce Soyayyar Kwankwaso Ba, Kuma Ba Na Fatan Samun Warakarta, Cewar Jarumin Finafinan Hausa, Mustapha Nabraska

Kiwon Lafiya Amfanin Lemongrass A Jikin Dan’Adam

Ibrahim Auwal | August 30, 2018 | 0 Comments


Ciyawa-mai-kamshin-lemu shuka ce mai dadin kamshi, wato wata irin ciyawa ce doguwa mai launin kore da kamshin lemun-zaki.

Duk da yake dai ba ta da alaka da lemun-zaki, kamshin ciyawar mai karfi da dandano ya yi kama dana lemun-zaki, amma ba ta da zaki.

Ana samun ciyawar a kasashe masu yanayin zafi ko yanayin dumi.

Anfi yawan amfani da ita a kasashen Asiya, Afirika da kuma Australia .

Haka kuma anfi yawan amfani da wannan ciyawa a kasashen Asiya wajen girki.

A kasar Indiya kuwa akan yi amfani da ita a matsayin maganin gargajiya.

Ana amfani da
busassar ciyawar ko danyar ta domin amfani na daban-daban.

Kuma anfi amfani da ita wajen hada shayi , miya ko kori domin ta zamo hadin kayan kamshin girki.

Ana samun manta a kasuwa wanda shima ake amfani dashi.

Mai yiwuwa ne kana da wannan shuka a gida ko a lambunka , koma kana amfani da ita, to amma baka san ainahin amfaninta taba ga lafiya, kawai dai ka dauke ta shuka ce domin kawata gida ko filebo mai sa kamshi a kofin shayinka a lokacin da kake kurbawa.

To ka bude idanunka, domin kuwa wannan ciyawa amfanin ta ya wuce na adon gida kadai ko kamshin shayinka da kake jin dadin sha saboda dandano da kamshin da take baka a lokacin da ka yi amfani da ita.

Ciyawar Lemongrass nada ado da za ta iya yima lafiyar ka domin inganta ta.

1. Kariya Daga Ciwon-Daji/Kansa Shukar lemongrass nada sinadari mai kamshi na “citral”, wanda binciken kimiyya ya nuna cewa yana kashe kwayoyin halitta da ciwon kansa ya harba a jiki. Haka kuma yana inganta lafiyar kwayoyin halittar jiki gaba daya.

2. Karin Jini Da Hana Rashin Jini:Lemongrass nada sinadarin “iron” mai yawa, wato sinadari maisa karin jini domin cikakkiyar lafiya da kuma hana wasu matsalolin rashin jini.

3 Rage Hawan Jini :Yawan sinadarin “potessium” a cikin lemongrass, sinadarin mai inganta lafiyar zuciya, koda da sauran sassan jiki, na taimakawa wajen hana hawan jini, cututtukan zuciya, mutuwar sashen jiki, ciwo kansa, matsalolin rashin narkewar abinci da rashin haihuwa, cikin yardar Allah.

4. Kariya Da Hana Girman Kananan Halittu masu haddasa cututtuka a jiki da kuma hana kumburi, wuri, yayi ja, da radadin ciwo a jiki, musamman taimako ce ga masu ciwon gabbobi da sassan jiki da sauransu.

5. Yaki da cututtukan bakteriya dana fangas: Don haka tana maganin zazzabin cizon sauro da taifot idan an yi shayi da ita, da sauransu. Haka kuma tana maganin cin ruwa na yatsun kafa da makero idan an yi amfani da manta dai da sauransu.

6. Maganin Mura, Zubar Hanci Da Hawaye, Kaikayin Ido, Atishawa, Toshewar Hanci

7. Tace duk wani abu mai guba ga jiki Musamman na abinci, ko wani abu mai cutarwa da fitar da su daga jiki. Tana tsaftace hanta, koda, mafitsara da sauransu.

8. Inganta Bacci Da Kuma Yakar Rashin Bacci: Lemongrass nada tasiri wajen kwantar da hankali da fada da rashin bacci domin samun cikakkiyar lafiya.

9. Taimako Ga Masu Ciwon Suga: Tana rage yawan suga cikin jini, tsarkake saifa da inganta aikinta.

10. Inganta Kwakwalwa: Lemongrass na taimakawa kwakwalwa wajen maida hankali don lakantar karatu, rike karatun da kuma taimakawa wajen sarrafa karatun dama ilimi. Sinadarin “magnesium”, “phosphorus” da “folate” da ake samu a cikin ciyawar nada tasirin kyautata lafiyar kwakwalwa.

Daga leadership


Amfanin Ganyaye Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

Ibrahim Auwal | August 30, 2018 | 0 Comments


Shekaru masu yawa da suka wuce bugu da kari kuma duk a cikin rayuwar al’umma sun gane cewa ashe yana da matukar muhimmanci su rika amfani da ganye, ko kuma ganyaye wajen da suke sa shi a cikin abinci, wani ma da shi ake dafa abincin, wani kuma sai an kammala dafawar, ake sa wa saboda suna da amfani wajen maida shi abincin aji dadin cin shi.Wasu ana sa su cikin miya ne a dafa su tare kamarsu Alaihu Shuwaka, Ugu da dai sauransu. Wasu suna amfani da shi ne saboda ya kara ma shi abincin armashi, wasu kuma suna amfani da shi a matsayin abinci saboda ya samar masu da sinadaran bitamins, da kuma amfani da ake dasu a matsayin na masu wanke ciki. Duk wadannan dalilan gaskiya ne ta bangarori daban daban wajen amfani da su ganyayen, amma duk da haka akwai wadansu mutane wadanda su ba zasu yarda da a sa masu ganye a abincin su ba. Irin wadannan mutane suna matukar asara ba karama ba, saboda shi dandanon abincin yadda zai iya canzawa, da kuma karuwar da zasu sami a jikinsu wajen mafani da ganyen. Akwai ganyaye da yawa amma kuma sai dai suma da abubuwan da ake samu na musamman, a kuma kokarin da muke yi na gane, yadda suke taimaka mana ta bangaren lafiyar jikinmu, abu mai kyau ne mu gane ko wadanne abubuwa ne suka kunsa su ganyayen da muke ci a matsayin abincinmu.

Ganyaye su kunshi wani sinadari wanda ake kira cellulose wanda shi ma kan shi wani sibnadari ne, wanda shi cikin mutum ba zai iya narkar da shi ba, cellulose wani sinadari ne wanda ya kunshi ko kuma bayani mai kyau ya kun shi fibre a cikin abinci, shi dai sinadari shi ne wanda ke taimakwa wajen abubuwan da ake kasayarwa, yana kuma samin hanyar shi da hanji amma kuma ana fitsarar da shi matsayin fitsari.

Ita dai wannan fibre tana taimakawa wajen fitar da abubuwan da basu da amfani a jikin mutum, da hanyar alimentary tract wannan a hanji take da kuma gastrict irritants. Ta wannan hanyar ce su ke fitar da duk wasu abubuwan da ka iya cutar da jiki. Cellulose wani sinadari ne wadanda akwai wasu nau’in dabbobi wadanda suke iya cin shi ya kuma samu narkewa a cikinsu, kamar su awaki tumaki da kuma shanu, saboda su wadancan halittun. Su wadannan halittun ana kiransu da suna ruminants, (wadanda suna iya ma kwana suna cin abinci da suka riga suka ci, wani lokacin ma daga kwance zasu rika yin tuka, kamar shi abincin da suka ci da farko suna dawo da shi ne domin kara nika shi da hakoransu) saboda irin wadannan dabbobin sun dogare nbe akan wadannan abubuwan da suke saboda su ci gaba da rayuwa ba kuma su kamu da ciwo. Irin wannan baiwar ana samunta wajen dan adam, dalili kuwa akwai wasu ganyayen da suke ma mutum maganin wadnasu muggan cututtuka da kuma rage nauyi. 

Ganyaye sun kunshi kashi 85 da kuman 95 na ruwa wanda yake taimakama fatar jiki da kum amaganin wasu abubuwan da asu fito kan fatar wadanda baa bin so bane, bugu da kari kuma sun kun shi wani sinadari wanda ake kira phytonutrients wanda shi kuma yana taimakawa ne wajen, tsufa wanda ya zo ake kuma ganin lokacin shi bai yi ba. Suna samun wannan damar ne ta hanyar hana wasu kwayoyin halitta lalacewa a sanadiyar gajiya, hasken rana ko kuma yadda ake lalata muhalli ta hanyar wasu abubuwan da suke taimakama hakan. Ganye wanda yake da yake da kala yana iya kasancewa ja, ko kuma mai kalar ruwan lemu, yana taimakawa jiki wajen ba shi, ko kuma kara karfafa beta carotene, wanda shi ne ke kare fatar jikin mutum daga illar rana a kan fatar fatar jikin dan adam, ya yin da kuma take kara mata wani armashi. Daya daga cikin misalin orange begetable shi ne karas, ya yin da kuma jan ne tumatari, sai dai kuma ya kunshi lycopene wanda har yanzu ba a tabbatar da cewar shi natural sunscreen ne.

Bitamin C ba wai kawai ana samun shi ne a citrus fruits ba, ana ma samun shi a tattasai da kuma tumatari, cucumber da albasa, kabeji spinach da abocado pear da kuma bell peppes. Shi wannan Bitamin yana da matukayar muhimmanci wajen yin collagen wanda shi ma wani sinadari ne, wanda idan ba tare da shi ba jiki ba zai iya kare gyara kan shi ba. Wannan ya nuna ke nan idan mutum ya yi rauni, za a dauki lokaci mai tsawo kafin shi raunin ya warke, maganar warkewar wadda ita ce gyaran. 

Irin wannan gyara ko kuma warkewar ba kasaifa take kasancewa wadda ake so ba, daga irin wadannan cututtuka koma tari abin ba a samun nasara. Sau da yawa abubuwan da jiki ya tanada na bitamin c da kuma magnesium nan da nan ake gamawa dasu, idan an samu wata gajiyawa, sai kuma idan ana cin ganyaye daban daban, hakan yana sa a koma a cikin mizanin da ake ciki tun farko.

Idan su ganyaye suna taimaka mana mu rage gajiya ko kuma wata damuwa ta hanyoyi daban daban, wadanda aka yi magana akan su, an yi hakan ne saboda amfaninmu. Wannan ya nuna ke nan ita damuwa (stress) tana sa mutum ya gaji ya zama ba wani kazar kazar a tare da shi, ba zai iya yin wani aiki na azo a gani ba, ta hakan ne wasu mutane sai su yi tunanin ko abinci ne, ko kuma barasa, saboda shi wannan halin da aka shiga. Shiga cikin irin wannan hali zai iya shafar lafiyar mutum ta hanyoyi daban daban. Wani lokaci kuma yadda mutum zai canza ga yadda aka san shi, wato kira ko kuma halittar jikin shi, kamar maganar kiba da kuma abinda zata iya haifarwa a gaba kamar anoredia da kuma asthenia.

Fibre wadda take cikin ganyaye tana taimakawa wajen rage mizanin cholesterol, ko kuma ya kasance a daidai yadda ake bukatar ya kasance, wannan yana taimakawa wajen rage yiyuwar kamuwa da cutar zuciya da kuma cardia arrest. Sai dai kuma wani abu daban folic acida na ganye na taimakawa jiki ya samar da red bloocells ( wadanda su aikinsu shi ne safarar kai iskar da ake shaka wato odygen duk wurin daya kamata ). Bugu da kari ganyaye sun kunshi bitamin a wanda yake da amfani wajen taimaka ma gani da idanu sosai. Haka nan ma sun kunshib potassium tare da shi kuma magnesium wanda shi ma yana da matukar amfani shi ma wajen daidaituwar yadda mizanin jinin mutum ya dace ya kasance. Suna iya wannan aikin ne ta hanyar dan dakatar da yadda su hanyoyin jinin suke aiki, idan an fahimta sosai, ana dan rage masu karfi ko kuma tafiya, ta haka kuma sai jini ya wuce ta hanyarsu ba kuma tare da an matsa ma ita zuciya ba yin wani aiki daban wanda aka iya kawo mata cikas. Yanzu dai an fahimci muhimmancin cin ganyaye ko kuma abincin wanda ya kunshe su akai akai, da kuma yadda ya kamata, mafi komai muhimmanci akan duk wani abinda za ayi saboda maganin cutar kansa da karshen hanji. An yi bayanin cewa yadda ba ko wanne lokaci bane ya kamata ace an yi ma hanji tamkam da abinci, sai kuma canza lokacin da ya dace aci shi abincin, saboda a taimakwa matsalar da a kan samu, abinda kuma shi ne ke sa kumburi, wanda masana suka ce yana da ala ka da kansar karshen hanji. Irin wannan kumburin shi ne abinda ake cema hanyar zuwa kamuwa da ita cutar ta kansar hanji. Babban abin da ya dace shi ne a rika cin ganye ko kuma ganyaye, saboda idan aka bi ta wannan hanyar za a kauce ma kamuwa da da cutar kansar karshen hanji.

Yawancin mutane basu cin ganye ko kuma ganyaye, duk kuwa da yake cin su ganyayen hanya ce mafi sauki da mutum zai bi, saboda ya kara bunkasa lafiyar jikin shi. Bayan haka ga kuma kawo tsaiko na rage kaifin su kwayoyin halittar da suke sa tsufa girma, suna samar da nutrients nau’oin abinci wadanda zasu iya taimakawa, wajen yadda za a fuskanci stress wato damuwa, wato kamar ajin Bitamins B, folic acid omega-3 fats da maganesium potassium da kuma glutathione.

Abin na farko shi ne mizanin da aka fi amfani da shi wajen bangaren kasuwanci na maganin, saboda an san yana iya warkar da ko wacce irin cutar da mutum ya sani. Abincin daya kunshi ganye ko kuma ganyaye zai iya kare mutum daga cutar cutar (sanyin kashi )arthritis dementia (cutar mantuwa) cutar zuciya, bayan cutar kansar hanji, yanzu ma ana ta maganganun cewar akwai ma maganar kawo cikas ga al’amarin daya shafi tsufa ta yadda su kwayoyin halittarcake rage masu kausashi.

Binciken da aka yi ya nuna cewa mutane wadanda suke ci sau bakwai ko kuma fiye da haka na cin ganyaye a ko wacce rana, suna da kashi 42 na yiyuwar mutauwa,ta ko wanne irin sanadi, idan aka gwada su da wadanda suke ci abinda bai kai ko sau daya ban a ganye ko kuma ganyaye.
Daga karshe magnesium wanda shi ma yana da muhimmanci ga aiki mai kyau na tsokar jiki da kuma ayyukann jijiyoyi, duk da haka yana taka muhimmiyar rawa wajen lura da daidaituwar immune system (wasu sinadaran da suke kare jiki daga kamuwa da cuta). Rashin isasshen magnesium, tun farko akwai maganar matsalar data shafi kagara da kuma da kuma migraine. Haka nan ma cin ko kuma amfani da calcium wanda idan ba tare da shi ba, ba zamu samu lafiyar kasusuwan mu ba, shi ma maganesium ne yake taimaka ma shi. Yanzu da kowa ya gane ke nan, ba za a samu cikakkiyar lafiya ba, ba tare da kullun ana samun da cin ganyaye ba. Ganyaye ba wai dole sai masu tsanwa ba, kamar yadda bayani ya nuna cikin wannan maudu’i na “amfanin ganyaye ga lafiyar jikin dan adam”.

Fasto Ya Ci Na Jaki A Lokacin Da Ya Yi Kokarin Warkar Da Mahaukaci.

Ibrahim Auwal | August 29, 2018 | 0 Comments


Wannan al'amari ya faru ne a garin lokoja. Inda rana ta kwace wa wani Malamin coci. Wanda ya yi kaurin suna wajen haɗa baki da mutane su yi haukan karya, shi kuma ya warkar da su, a ba shi kuɗi.

Sai dai a ranar sa'a ta kwace masa inda ya yi arangama da wani mahaukaci tuburan. Ko da faston ya zo kusa da shi don karanta masa adu'o'in kirista, kawai sai ya tasam masa da duka ya yi masa lillis. A hoton za mu iya ganin mahaukacin sanye da bakar riga.

Sarauniya.

Allah Sarki Tsohon daya sayar da gonarshi ya biya aikin Hajji ya rasu yana a Makka

Ibrahim Auwal | August 28, 2018 | 0 Comments

Wannan bawan Allah dan asalin kasar Pakistan ne wanda ya sayar da gonarsa sannan ya kama aikin leburanci a gonar don ya tara kudin aikin hajji kuma Ubangiji Ya biya masa bukata ya samu halartar hajjin bana amma kuma a ranar da yake cikin Ihram yana furta kalmar Labbayka, Ubangiji ya dauki ransa. Allah Ya ji kansa.

Majiya: Dakta Zakir Naik

TTirkashi aryam Gidado tasha ruwan Allah wadai akan wannan hoton

Ibrahim Auwal | August 28, 2018 | 0 Comments


Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Gidado kamar kowace jarumar fim din Hausa, takan saka hotuna lokaci zuwa lokaci a dandalinta na sada zumunta kuma masoyanta sukan yaba, saidai a wannan lokacin labari ya sha ban-ban, dan kuwa wannan hoton ya jawo mata surutai daga masoyan nata.

Da dama da suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan hoto sun ce bai dace ba sam musulma ta dauki irin wannan hoto haka kuma har ta nunawa Duniya.

Gadai wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan wannan hoton:

Dalilin da ya sa na tsunduma a harkar fim din Hausa>>Jamila Nagudu

Ibrahim Auwal | August 25, 2018 | 0 Comments

Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood watau Jaruma Jamila Umar da aka fi sani da Jamila Nagudu ta bayyana dalilin da ya sa ta tsunduma a cikin harkar fim.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a lokacin da take fira da majiyar mu ta Muryar Amurka a watannin baya a cikin shirin su na duniyar Kannywood inda ta ce ta fara sha'awar yin fim ne bayan da ta kalli wani fim a shekarun baya inda a ciki aka nuna halin wata mata maras kyau da ke kama da na wata makwaficiyar ta da kuma irin yadda karshen ta ya kasance.

Jarumar wadda yanzu haka tana cikin 'yan fim masu tsada da kuma aji ta bayyana cewa daga wannan lokacin ne ta fahimci cewar lallai masu yin fim fadakarwa suke yi shine ma ita ta shigo domin ta bada gudummuwar ta.

Yan fim din Hausa dai a lokuta da dama suna fuskantar kyama da tsangwama daga al'ummar da suke cikin su sakamakon kallon da ake yi masu na masu bata tarbiyyar mutane, zargin da a kullum suke karyatawa.

Naija.ng.

Ku Kalli Hotunan Jikan Sheik Ja'afar Mahmud

Ibrahim Auwal | August 25, 2018 | 0 Comments

Wannan shine Ja'afar Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo, jikan marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, dan wajen Zainab Ja'afar Mahmud Adam babbar 'yar Marigayin.


Muna addu'ar Allah ya raya shi, ya kuma sa ya gado kakansa da mahaifinsa.
Rariya.

Ku kalli Hotunan Maryam Booth da suka birge

Ibrahim Auwal | August 24, 2018 | 0 Comments

Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da suka birge, tasha kyau, muna mata fatan Alheri.

Ku Kalli kwalliyar Sallah ta Maryam Yahaya

Ibrahim Auwal | August 23, 2018 | 0 Comments

Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan kayatattun hotunan nata data sha kyau, tubarkallah, ta yiwa masoyanta gaisuwar barka da Sallah, muna mata fatan Alheri.
 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger