Ku kalli. Hoton Maryam Gidado da ya dauki hankula

Ibrahim Auwal | September 11, 2018 | 0 Comments

Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Gidado kenan a wannan hoton nata da ya dauki hankula, ta saka hoton a dandalinta na sada zumunta inda wasu suka yaba, wasu kuwa cewa suka yi hoton be dace ba.

Ga wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan wannan hoton.

Bayan labarin cewa ya saki matarshi: Adam A. Zango ya saiwa matar tashi sabuwar mota

Ibrahim Auwal | September 09, 2018 | 0 Comments

A makon da ya gabata ne mujallar Fim Magazine ta ruwaito cewa, tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A.

Zango ya saki matarshi, labarin da ya dauki hankulan mutane sosai musamman masoya fina-finan Hausa to saidai da safiyar yau, Lahadi, Adamun yace ya sayawa matarshi sabuwar mota.

Badai aji komai ba daga Adamu akan labarin sakin matarshi da ya watsu ba
Masu iya magana na cewa tsakanin mata da miji sai Allah, a cikin wani labari da ya wallafa da safiyar yau, Lahadi, Adam A.

Zango ya bayyana cewa ya saiwa matarshi sabuwar mota.

Wannan bayani ya dauki hankulan mutane inda wasu ke tambayar to in maganar cewa ya saki matarshi da akayi?.

Abinda zamu ce dai anan shine Allah ya kar dankon soyayya.

Ga hoton motar.Ku Kalli Nazir Sarkin waka da Jamila Nagudu suna Nishadi

Ibrahim Auwal | September 09, 2018 | 0 Comments

Tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin Waka kenan tare da tauraruwar fina-finan Hausa, Jamila Umar, Nagudu a wadannan hotunan nasu suna Nishadi, muna musu fatan Alheri.
So ko hauka: Wani saurayi ya kashe kansa saboda an kwace masa budurwa a Najeriya

Ibrahim Auwal | September 07, 2018 | 0 Comments

- Wani saurayi ya kashe kansa saboda an kwace masa budurwa a Najeriya

- Saurayin mai suna Prince dan jihar Bayelsa ne

- Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin


Wani matashin saurayi mai suna Prince dake a makarantar Sakandare ta jeka-ka-dawo ta Isaac Jasper Boro a karamar hukumar Sagbama, jihar Bayelsa ya kashe kansa lokacin da ya gano wani saurayi ya kwace masa budurwa.


Shi dai Prince wanda akace dan asalin kauyen Kaiama ne a karamar hukumar Kolokuma/Opokuma ance ya kwankwadi maganin kwari na fiya-fiya ne wanda sandiyyar haka ya margaya.

NAIJ.com ta samu cewa tuni dai iyalan mamacin suka rufe shi a ranar kamar yadda al'adar su ta tanada.

Wasu abokan mamacin da majiyar ta mu ta zanta da su sun nuna matukar kaduwar su da mutuwar ta sa sannan kuma suka yi takaicin dalilin da ya sa ya kashe kan sa.

'Yan sanda a jihar dai sun tabbatar da aukuwar lamarin.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya, shiyyar jihar Kwara sun sanar da samun nasarar cafke wasu gawuratattun matsafa 'yan kungiyar asirin nan ta Badoo da suka addabi al'ummar jihar.

Majiyar mu ta Tribune, ta tabbatar mana da cewa jami'an 'yan sandan sun cafke matsafan ne bayan wani samame da suka kai masu sakamakon bayanan sirri da suka samu daga wasu masu kishin kasa.

Naij

Ku Kalli kwalliyar Juma'a ta Nafisa Abdullahi

Ibrahim Auwal | September 07, 2018 | 0 Comments

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi kenan a wadannan rangada-rangadan hotunan nata da suka kayatar, tasha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

Wata Mata ta kashe kanta a dalilin kama mijinta da wata a gadon su na aure

Ibrahim Auwal | September 06, 2018 | 0 Comments

Wata matar aure mai suna Kafilat ta kwankwadi ruwan guba a dalilin kama mijinta Ismail da ta yi da wata a kan gadon su na aure.

Wannan mummunar abu ya faru ne ranar Laraba gidan su dake unguwar Egan-Igando, jihar Legas.

Dama can Kafilat Oriade ta yi yaji daga gidan mijinta mai suna Ismaila Oriade kan matsalar yawan neman mata da mijin ke yi.

Wani makwabcin su ya bayyana wa PREMIUM TIMS cewa wannan ba shine karo na farko ba da Kafilat take kwankwadan ruwan guba iadan suka sami sabani da mijinta.

” Ko a kwanankin baya sai da Kafayat ta kwankwadi ruwan guba, Allah ne ya sa ran ta na gaba.

” A wannan karo abin ya zo da ajali. Domin kuwa bayan ta sha wannan ruwan guba muka gaggauta kaita asibiti har guda biyu. Da suka ga halin da take ciki sai suka ki amsar ta, ana haka ne ta Allah yayi mata cikawa.

Mijin nata, wato Ismail ya bayyana cewa shi dama tuni sun rabu da Kafilat duk da cewa ba a san inda yake ba a lokacin domin ya gudu.

Premiumtimeshausa.

Lalacewa: Miji ya cizge leben matar sa yayin da suke dakuwa

Ibrahim Auwal | September 05, 2018 | 0 Comments
Wani mutumin kasar Kenya, David Munga, ya shiga hannun hukuma bayan ya cizge leben matar sa na kasa yayin da suke fada.

A cewar wani gidan talabijin na kasar Kenya, Citizen TV, Mungai na yawan dukan matar sa, Anne Waireri, tare da ji mata rauni a wasu lokutan.

Mungai da Anne sun yi wani fada ne a ranar 29 ga watan Agusta, ranar da ya cizge mata lebenta na kasa.

Makwabtan Mungai ne suka tona asirin inda yake boye bayan ya jiwa matar tasa ciwo.
Matar da miji ya cizgewa lebe

A wani labarin na naij.com kun ji cewar wasu mata guda 6 dake takarar kujerar shugaban kasa sun bayyana dalilinsu na son karbar mulkin Najeriya daga shugaba Buhari.

Matan 6 – Farfesa Olufunmilayo Adesanya-Davis, Dakta Oluremi Comfort Sonaiya, Dakta Elishama Rosemary Ideh, Adeline Iwuagwu-Emihe, Eunice Atuejide da Princess Oyenike Roberts – sun bukaci masu zabe su bawa mace dama domin kawo canji nan gaskiya a Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar matan na wakiltar kasha 60% na dukkan ‘yan takarar dake burin ganin sun karbi mulkin Najeriya daga hannun shugaba Buhari a zaben 2019.

Wannan matar ta dau alkawarin sayar da kadarorinta dan sayawa shugaba Buhari Fom din takara

Ibrahim Auwal | September 04, 2018 | 0 Comments

Wannan Baiwar Allah Mai Suna Ronke Ajayi Ta Dauki Alwashin Ko Za ta Siyar Da Kadarorin Ta Ne Kaf Za ta yi Hakan Don Ganin Shugaba Buhari Ya Sayi Fom Ya Tsaya Takara Karo Na Biyu Kuma Ya Ci Da Yardan Ubangiji.

Domin Ta Ce Tana Da Yakinin Cigaban Buhari Zai Daura Nijeriya Akan Turbar Cigiban Da 'Ya'yanmu Wadanda Basu Zo Duniya Ba ma Za su Amfana.
Rariya.

Ku kalli Hotunan Nafisa Abdullahi tare da 'yan uwanta

Ibrahim Auwal | September 04, 2018 | 0 Comments

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi kenan a wadannan kayatattun hotunan nata tare da 'yan uwanta, muna musu fatan Alheri.


An bude gidan karuwan roba na farko a Duniya

Ibrahim Auwal | September 04, 2018 | 0 Comments

A kwanakin bayane aka kera wasu matan roba da maza zasu iya amfani dasu wajan biyan bukatarsu, wannan lamari ya dauki hankulan Duniya akaita muhawara wajan tunanin ko zasu iya maye mata ko kuwa a'a.

To ashe dai abin mamakin ba a nan ya tsaya ba, dan kuwa jiya Litinin a birnin Turin na kasar Italiya, an bude gidan karuwai inda aka saka irin wadannan matan roba dan biyan bukatar masu ra'ayi, wannan gidan karuwai na matan roba shine irinshi na farko a Duniya.

Masu gidan karuwan matan robar sun bayyana cewa, tuni mutane sai tururuwar sayen tikitin zuwa su biya bukatarsu da wadannan matan roba suke, bayanin da gidan karuwan ya fitar na cewa, yanzu haka layi ake bi wajan siyan tikitin dan kuwa ya riga ya kare, sai an jira wani ya shiga ya fito tukuna.

Ba matan roba kawai aka ajiye ba, hadda namiji daya dan biyan bukatar mata.
Ana biyan kimanin sama da dubu talatin dan yin awa daya da matan robar, ko kuma sama da haka ga wanda yake da bukata, akwai kuma wasu kudi na musamman da mutum zai biya kamin ya shiga dakin matan robar koda tsautsai zai sa ya ji mata ciwo.

Matan robar zasu iya saka duk kalar kayan da mutum yake so sannan kuma su mai duk irin abinda yake so dan biyan bukatarshi.

Bayan mutum ya gama da macen robar, ana tsaftaceta ta hanyar wanki na musamman na tsawon awanni 2 kamin wani ya kara shiga dan ganawa da ita.

Fatima Ganduje da Idris Ajimobi sun zama fuskar mujallar George Okoro

Ibrahim Auwal | September 04, 2018 | 0 Comments

Ma'aurata, Diyar Gwamnan jihar Kano, Fatima Abdullahi Umar Ganduje da mijinta, Dan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi ne suka zama fuskar mujallar labaran aure ta George Okoro.

Hoton nasu ya kayatar, muna musu fatan Alheri.Rai bakon duniya: Yadda wata Kada ta yi kalaci da wata Uwa da jariryarta

Ibrahim Auwal | September 03, 2018 | 0 Comments

Kaico, ba mutuwa ake tsoro ba, hanyoyin mutuwar ake ji, don kuwa idan ajali yayi kira tabbas ko ba ciwo sai an je, hakan ne ya tabbata akan wasu masoya biyu, Uwa da diyarta, inda suka gamu da mummunan ajali a kasar Uganda.

Wata mata da diyarta sun fuskanci mutuwarsu a hannnun wani mayuwacin Kada a ranar Juma’ar data gabata a kasar Uganda, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya ya bayyana.


Wani Kada
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a tafkin Albert dake yankin Arewa maso yammacin kasar Uganda, inda matar ta tafi debo ruwa dauke da jaririyarta yar watanni biyar a bayanta.

Hukumar kula da namun daji ta kasa ta bayyana kisan a matsayin wani hari da namun daji ke kaiwa mutane, wanda ta bayyana cewa yana faruwa ne a lokacin da dabbobi ke gasar neman abinci a tsakaninsu, sa’annansu kuma jama’an yankin basu da ruwan famfo, don haka suke fita neman ruwa.

“Muna shawartar jama’a dasu guji duk wani yankin da ake samun Kadoji masu cin naman mutum, su Kadoji suna zama ne a inda ake samun kifaye a cikin rafi ko tafki, amma idan adadin kifayen dake ruwan suka ragu, sai su fito waje suna su yi farautar mutane.” Inji kaakain hukumar, Bashir Hangi.

Rahotanni sun tabbatar da cewar mazauna yankin da wannan mummunan hadari ya faru sun yi iya bakin kokarinsu don ceto matar da jaririyartata, amma basu samun nasara ba, yayin da tuni Kadar yayi awon gaba dasu cikin ruwa.

A wani labarin kuma, wani jami’in hukumar kare namun daji na kasar Uganda yace ana iya kama Kadar daga baya, inda yace a ko a ranar Asabar din data gabata sai da suka kama wani Kada mai tsawon kilomita 700 daya cinye mutane biyu a shekarar 2013.

“A yanzu haka ina yankin tsakiyar Uganda, Ngoma, inda farautar wani Kada daya cinye bunsurai guda 32 a wani kauye, don haka muna kamasu.” Inji jami’i Peter Ogwang.

Naij

Mahaukaci Ya Yi Kokarin Yi Wa Matar Aure Fyade A Kasuwa

Ibrahim Auwal | September 02, 2018 | 0 Comments

Wani wasan kwaikwayo ya auku a sananniyar kasuwar Ogbeogonogo dake garin Asaba, cikin jihar Delta a yayin da wani da ake zargin mahauci ne ya yi mai matsakaicin shekara lokacin da ya yi kokarin yiwa wata matar aure fyade a cikin kasuwar.

Lamarin ya auku ne a ranar asabara data gabata kuma lamarin ya auku ne da misalign karfe biyu na rana a lokacin da matar take kan sa’anar ta ta sayar manja da kayan masarufi.

Wata ganau mai suna Janet Agbou ta shedawa kafar Daily Post cewar, mahaukacin mai suna Simeon wanda yake sanye da yagaggun sitira ya yi kokarin hawan bayan matar, inda hakan ya janyo farfashewar kwalaben ta dake cike da manja.

Janet Agbou ta kara da cewar, mahaukacin ya samu nasarar cire mata zani har ya samu danne ta kuma ga dukkan alamu mutumin mahaukaci ne.

A cewar Janet Agbou mahaukacin ya yi kokarin sanya alurar sa a cikin gaban matar, inda masu wucewa suka kawo mata dauki suka kuma fara danawa mahaukacin na jaki.

Daga baya an mika mahaukacin ga ‘yan sanda na gundumar “A”, inda bayan da suka gudanar da bincike suka gano cewar mahaukaci ne. Da take hira da kafar ta Daily Post matar wadda ta bukaci kar a ambaci sunan ta tace lamarin ya girgizata.

A cewar matar, “ Ji kawai na yi an kama ni ta baya, kuma wanda ya kama ni din yana ta kokarin keta mutuncina, wanda a kokowar da muke yi ne sai muka fadi a kasa a tare, inda na fara ihun a kawo mini dauki. Gungun mutane sun bashi kashi daga baya aka mika shi ga ‘yan sanda.

Ta kara da cewa, ni matar aure ce mai ‘yaya uku, wannan aikin shedan ne kuma na godewa Allah da ya tsyar da abin a nan domin ban taba sanin wannan lamarin zai auku dani ba. Da yake jawabi akan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Aniamaka Andrew ya ce, duk da jibgar da mahaukacin yasha bai ce uffan ba.

Ya sanar da cewar munyi amannar a bisa binciken da muka gudanar mutumin mahaukaci ne kuma baza mu iya tsare shi ba mun dai kashi asibi don ayi masa magani.
 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger