Bana Gaba Da Mawakiya Fati Nijar - Maryam Baba

Ibrahim Auwal | October 29, 2018 | 0 Comments

Baya ga kasancewarta shahararriyar mawakiyar Hausa ta zamani, Maryam A. Baba tana taka muhimmiyar rawa wajen fadakarwa da nishadantarwa a fagen sana’arta. Kamar yadda ba a raba duniyar mawaka da ’yan fim da abin kwarmato, a ’yan kwanakin nan ne aka rika baza jita-jitar cewa mawakiyar ba ta ga maciji da abokiyar sana’arta, Fati Nijar.

Sai dai a wannan tattaunawa da Maryam ta yi da Aminiya, ta karyata batun, inda ta ce babu wata rashin jituwa a tsakaninsu. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu so ki gabatar da kanki

Sunana Maryam A. Baba, wasu kuma kan kira ni da lakanin Maryam Sangandali. An haife ni a Unguwar Sani Mainagge, Kano. A nan na fara karatun Islamiyya ta Rabi’u Sipikin. Bayan sauyin wurin zama na yi makarantar firamare ta Babban Giji. Daga nan na tafi makarantar Arabiyya ta GGASS danzabuwa.

Daga nan na sami sauyin makaranta, na koma GGSS KABO, inda a nan ne na kammala karatuna na gaba da firamare. Daga nan na fara karatun Shari’ar Musulunci a makarantar Legal ta Aminu Kano. Daga bisani na ga karatun ya yi min tsauri sai na sauya sheka zuwa Kwalejin Sa’adatu Rimi ta Kano, a nan na yi karatun NCE. Daga nan na fara aikin wucin gadi da gidan talabijin na NTA Kano, na yi irin wannan aikin da gidan rediyon Freedom, sannan da Dala FM, duk a Kano. Yanzu kuma ga ni ina sana’ar waka.

Ko ya kika sami kanki a sana’ar waka?

Na fara waka tun a lokacin da muke makarantar Islamiyya, baya ga nan ina yawan sauraron wakokin Indiya; ina bibiyarsu da kuma lokaci ya yi aka fara amfani da waka a fina-finan Hausa sai na yi amfani da wannan damar ni ma na ce bari na shiga a yi da ni; domin na ba da gudunmawata ta hanyar waka.

Domin ita waka hanya ce ta isar da sako da akan yi gargadi, tunasarwa da tsoratarwa, baya ga nishadantarwa.

Saboda dimbin jama’a da suke saurare, tarin fadakarwar da ake samu a waka kan sanya wanda ke yin abin da ya saba ka’ida ya gyara; wanda yake yin abin da ya dace kuma ya kara kaimi.

Ko akwai alaka tsakaninki da Murja Baba?

Eh, alakarmu da Murja Baba ita ce sana’armu ta waka sai kuma addinin Musulunci da ya hada mu, wannan ita ce babbar alakarmu.

Ana maganar cewa soyayya ta kullu tsakaninki da Aminudeen Alan Waka, ko ya abin yake?

Ahhh, inji waye? Ehhh, Alan waka dai kamar dan uwa ne a gare ni kuma yana taimaka mini sossai a sana’ata ta waka. A taikaice dai yayana ne, wannan shi ne abin da yake a kasa.

Wane irin taimako kungiyarku ke ba mawaka?

kungiyarmu na taimaka wa sabbin mawakan da suka shigo ta hanyar ba su kwarin gwiwar yin kyakkyawan rubutu mai ma’ana ba tare da batsa ba ko zambo ko zagin wani, tare da dora su a kan turbar girmama na gaba da kamun kai da dai makamantan haka.

Ana kuma taimakon su ta fuskar kudi da makamantan haka.

Ana maganar cewa ba kwa ga miciji da Fati Nijar, ko haka abin yake?

Subhanallahi! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Wallahi duk wanda ya fadi haka karya yake. Ni da Fati kud-da-kud muke, akwai soyayya a tsakaninmu mai karfi. Takan zo gidanmu ta gai
da iyayena, ni ma nakan je inda take mu kulla zumunci.

Ko akwai wani kalubale da kika fuskanta a lokcin da kika fara waka?

A lokcin da na fara waka yayana ya sanar da mahaifina, sai ya ce wakar me zan yi? Nan fa ya hana ni, to da ma daga makaranta nake biyawa wajen wakar.

Da ya ga na ki bari sai ya hana ni zuwa makarantar baki daya. Ni kuma saboda muhinmancin karatu sai na ga ba zan iya bari ba, har ya kai ga na yi yajin cin abinci.

Daga bisani ya hakura na koma makaranta na ci gaba da waka, wacce a yanzu ta zama sana’ata.

Wane salo kike dauka a wakarki?

A albam dina na Rabo-Rabo da jinsin mata, akwai wakar da na yi ta halin dan Adam sannan akwai wakar da na yi ta Auren Sunnah, yadda ake yin aure a musulunce, yadda a da ake da kunya a tsakanin maza da matan, da yadda ake bin tsarin neman aure ta fuskar neman yardar iyaye.

Sai kuma wakar da na yi ta Mace Tagari, ka ga duk namijin da bai samu mace tagari ba, yana cikin wani hali.

Na kuma yi waka a kan safarar mata, irin yadda ake dauko ’yan mata daga kauyuka ana sanya su ayyukan aikatau na bauta da yadda ake safarar mata zuwa kasashen ketare, ana sanya su karuwanci, ana gurbata masu rayuwa, da dai ire-irensu.

Wane alfanu kika samu a wannan sana’a taki ta waka?

To, alhamdu lillahi, na samu amfani da dama da ba za su misaltu ba sai dai na gode wa Allah a cikin wanna sana’ar ta waka ce na biya wa iyayena suka sauke farali, ni ma na je Hajji na sauke nawa faralin, a cikinta na gina gida na sanya iyayena, da dai sauran alfanu da ba zai yiwu na fade su duka ba.

A ina aka kwana a maganar aure?

E, to muna nan muna ta addu’a kuma muna so masu sauraronmu, masoyanmu su ci gaba da taya mu da addu’a, Allah Ya ba mu miji mafi alheri; mutum nagari.

Lokaci muke jira, muna fatan wannan jinkiri ya zame mana alheri, don ni babban burina in yi aure in gina makarantar Islamiyya, in sadaukar da ita ina kuma fatan cin ma wannan buri nawa matukar ina da sauran numfashi a duniya.

Daga: Jaridar Aminiya

Matan Gwamnoni Sunyi Alkwarin Taimakawa Mawakan Kannywood

Ibrahim Auwal | October 28, 2018 | 0 Comments

Matan Gwamnonin Arewacin kasar nan hudu da suka hada da matar Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab Bagudu da matar Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya A’isha Muhammad Abubakar da matar Gwamnan Jihar Kogi, Misis Rashida Bello da kuma matar Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya A’isha Ummi El-Rufa’i sun yi alkawarin taimaka wa mawakan Arewacin kasar nan musamman na masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood.

Matan gwamnonin sun bayyana kudirinsu na taimaka wa mawakan ne yayin taron kalankuwa da kadammar da albam mai suna ‘Lobe’ da fitaccen mawaki Ali Isa (Jita) ya shirya a dakin taron na Lagos Hall da ke otal din Transcorp Hilton da ke Abuja a ranar Asabar da ta gabata.

Matan gwamnonin sun bayyana niyyarsu ta taimaka wa mawakan Arewa ne saboda irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ilimantarwa da fadakarwa da wa’azantawa da kuma nishadantar da al’umma.

A lokacin da Hajiya Zainab Bagudu take jawabi a wurin taron, ta ce ofishinta zai taimaka wa mawakan Arewa musamman na Kannywood don ganin sun bunkasa sana’arsu ta waka.

Ta bayyana cewa mawaka suna da basira da kuma hazaka, kuma suna bayar da gudunmawa sosai kamar yadda likitoci suke ba da gudunmawa a duniya, “Don haka ina sauraren wakoki kuma a cikin mawaka Ali Jita ne gwanina, don haka na sayi albam din ‘Lobe’ a kan Naira miliyan biyar.”

Ta kuma yi alkawarin za ta taimaka wa mawaka sakamakon gudunmawar da suke ba al’umma ta hanyar wakokinsu.

A lokacin da take jawabi, matar Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya A’isha Muhammad Abubakar ta yi alwashin taimaka mawaka ta hanyar ofishinta don ganin mawakan Arewacin kasar nan sun tsaya da kafafunsu.

“Ba zan fadi kudin da zan bayar a wurin wannan kaddamarwar ba, Ali Jita dan gida ne, abin da zan ce shi ne, sai ka zo Bauchi kawai,” inji ta.

Matar Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya A’isha Ummi El-Rufa’i ta kara nanata alkawarinta na taimaka wa mawakan Kannywood.

Ta ce, “Saboda yanayi na siyasa da ake ciki, idan na ambaci kudin da zan sayi albam din zai iya sa a mayar da abin siyasa duk da kyakkyawar manufata ta taimaka wa harkar waka a Arewacin kasar nan.

Amma zan ba ka gudunmawa sai dai ba zan fadi ko nawa ba ne.”

Ita ma matar Gwamnan Jihar Kogi, Misis Rashida Bello ta ce za ta taimaka wa mawaka ta ofishinta inda za su yi amfani da wakokinsu wajen yaki da Cutar Sankara.

Daga: Aminiya

An Tsare Mahaifiyar Maryam Sanda A Kotu

Ibrahim Auwal | October 25, 2018 | 0 Comments

Ma’aikatan hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta a Najeriya (ICPC) sun tsare mahaifiyar Maryam Sanda Maimuna Aliyu a yau Laraba.


An dai tsare Maimuna ne lokacin da take fitowa daga cikin babbar kotun Abuja a Maitama bayan sauraren karar da aka shigar na tuhumar ‘yarta Maryam Sanda akan zargin kashe mijinta Bilyaminu Bello.
An tsare Maimuna ne tare da danta Aliyu Sanda.

[Music] Baba Atiku Kai Muka Zaba 2019

Ibrahim Auwal | October 24, 2018 | 0 Comments

Dauko Sabuwar Wakar PDP Wacce Akayi Ma Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar Mai Taken Baba Atiku Kai Muka Zaba 2019


Download Now

[Music] Hafeez - Umar M Sharif

Ibrahim Auwal | October 16, 2018 | 0 Comments

Sabuwar Wakar Umar M Shariff Wanda Akayi A Fim Din Hafeez Ta Goto saiku Danna Akan Download Domin Daukowa

Download Now

[Waka] Baba Ya Amshi Na Goro

Ibrahim Auwal | October 16, 2018 | 0 Comments

Wata Sabuwar Waka Wanda Akayi Ma Gwamnan  Akan  Kudin Da Ake Tunanin Ya Karba.

A makon da ya gabata ne jaridar Daily Nigerian da ke wallafa labaranta a intanet ta saki labarin da ke cewa wani gwamna a yankin arewa maso yammacin kasar wanda ke neman zarcewa a mulki karo na biyu, yana karbar makudan kudade a wajen wasu 'yan kwangila.

Download Now

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger