Bana Nadamar Yin Sana'ar Fim A Rayuwata - Rabiu Rikadawa

Ibrahim Auwal | November 26, 2018 | 0 Comments

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Rabi’u Rikadawa wanda aka fi sani da Dila ya bayyana cewa ba ya nadamar yin sana’ar fim saboda alheran da suke cikinta ba su da iyaka.

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan rediyon Faransa a makon jiya.

Jarumin ya kuma bayyana irin gudunmawar da suke bayarwa ta hanyar wayar da kan al’umma a matsayin ladan sai dai Allah Ya biya su, amma ba wai kudin da ake sayen fim ya isa ya biya su jajircewar da suke yi wajen fadakar da al’umma ba.

“Ka san Bahaushe ya ce ana kaunar wawa ba a kaunar haihuwarsa.

Mu wadansu irin al’umma ne da suka soyu ga jama’a, sannan wani lokaci kuma jama’ar nan daga cikinsu suke nuna mana kiyayya, ina za su gan ka su buge, wadansu kuma suna nuna mana soyayya, matanmu suna hakuri domin ko ba ma nan za ka ga an je har gidajenmu, su karbe su, idan muna nan kuma mu karbe su, wani lokaci akwai masu zuwa don su ga matar wane, kuna gida za ku ji wata ta yi sallama ta ce wai za ta kewaya, ba hakan ne ya kawo ta ba, so take ta ga yaya matar wane take.

Sai bayan ta fito sai ka ji ta ce ke ce matar wane ko? Daga nan su zauna su yi hira, ka ga duk kauna ce, kaunar da ake mana ce ta gangaro har ta shafi iyalinmu.

“Wani lokaci daga wani abu ya faru sai ka ga an fara yi mana yayyafin zagi, wannan al’amari ba ya daga mini hankali, saboda rashin fahimta ce ta haifar da hakan, duk da wannan dambarwar da ake tafkawa, to ina alfahari da sana’ar fim, ina kuma godiya ga Allahu (SWT) da Ya zabar mini sana’ar fim.

Sana’ar fim tana da albarka, ba ya ga sayar da fuskarka da kake yi ka ci tuwo, babu wurin da za ka je neman wata alfarma ba ka samu ba, sai wani babban mutum mai mukami ya je neman alfarma yana bin hanya, ya kuma dade, amma kana zuwa masu ba da abin daga nesa za su hango ka sai su taso, ga Dila can, wannan ba Rikadawa ba ne?

Ga Daushe nan, su ne za su taso su ce maka ranka ya dade barka da zuwa, da zarar ka ce musu abu kaza kake so, sai su ce zo a yi maka.

Ina so in nuna maka albarka ta wannan sana’a, yau idan wani wanda ba ya wannan sana’a ya rasu iyakacin ’yan uwansa da abokansa ne za su sani, su kadai ne za su yi masa addu’a, amma mu idan muka rasu duniya ce take yi mana addu’a.

Duniya ce take cewa Allah Ya jikan wane. Ka ga wannan ma ba karamin abu ne ba. Idan na fada maka alheran da suke cikin harkar fim ni wurina ba su da iyaka,” inji shi.

Ya ce babban abin da ya sa yake alfahari da sana’ar fim shi ne wayar da kan jama’a da harkar ke yi, inda ’yan fim ke ba da gudunmawa wajen fadakar da al’umma.

Ya ce: “Idan ba zan manta ba tun zamanin da Turawa suka tafi suka bar mu, idan har ana neman a wayar da kan al’umma kan wani abu da ya shige musu duhu, walau fannin noma ko lafiya, hatta irin takin zamanin nan lokacin da ya shigo ana so a yi amfani da su, da masu wasannin kwaikwayo da makada da mawaka aka yi amfani wajen nusar da jama’a ga yadda ake amfani da shi.

Ban mantawa lokacin da kiliya ta koma dama, da masu wasannin kwaikwayo aka yi amfani, a nan mutane suka fahimci kiliya fa ta koma dama, a yanzu da muke tafiya har Allah Ya kawo mu wannan lokaci, idan ka kula ko a fannin siyasa, sannan idan tashe-tashen hankula sun faru mu din ake nema don mu fadakar da jama’a sakon zaman lafiya ya fi zama dan sarki; tashin hankali ba shi da amfani da sauransu.

Ba ya ga nishadantarwa da ke biyo baya, tabbas muna ba da muhimmiyar gudunmuwa ta fannin wayar da kan kan al’umma.”

A karshe Rikadawa ya bukaci gwamnati ta rika taimaka wa masu sana’ar wadanda suka tsufa kamar su Audu Karkuzu da Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja, saboda irin gudunmuwar da suka bayar wajen wayar da kan al’umma.

Daga:  Aminiya

Mawakin Daya Fi Kowane Mawaki Tallata PDP

Ibrahim Auwal | November 25, 2018 | 0 Comments

Alhaji Aliyu Haruna Abdullahi Ningi shi ne mawakin da ya fi kowane mawaki tallata Jam’iyyar PDP a farkon kafuwarta a 1998 inda ya zamanto da wakokinsa ake zuwa yawon kamfe ko bayar da talla don tallata manufofin jam’iyyar a kafafen watsa labarai cikin harshen Hausa.

Sai dai kuma daga baya ya yi mata wata waka da ta zamo tamkar yi mata bakin da ta kasa farfadowa har zuwa faduwarta a zaben bana wato wakar “Shegiyar Uwa Mai Kashe ’Ya’yanta PDP.” Me ya sa ya yi mata wannan waka? Ya bayyana dalilin yi mata wannan waka da sauran batutuwan da suka shafi rayuwarsa:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Cikakken sunana Aliyu Haruna Abdullahi Ningi.An haife ni a kauyen Rumbu da ke karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi a 1972.

Na yi makarantar firamare a Rumbu da Dagauda. Daga nan na tafi sakandare a Burra, kuma saboda takardata ba ta yi kyau ba, sai na sake komawa sakandaren Dagauda inda na je na sake gyara takarduna a 1992.

Daga nan sai na tafi Kwalejin Kimiyya da kere-kere da ke kauran Namoda a Jihar Zamfara a 1994, inda na yi diploma a kan nazarin kudi, na kammala a 1996. A 1997 ne na fara wakar siyasa lokacin mulkin marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha.

Me ya ba ka sha’awar shiga wakar siyasa bayan a makaranta ka karanta harkokin kudi ne?

A lokacin an kafa jam’iyyun UNCP da DPN, to muna da dan takarar da muke goyon bayansa wato Alhaji danlami Garba Bara’u da yake DPN da kuma Alhaji Abdu Sule shi kuma yana UNCP.

To a lokacin da aka yi wancan zabe, saboda UNCP kamar jam’iyyar gwamnati ce, sai aka yi mana karfa-karfa.

Wannan abu ya sa ba mu ji dadi ba, amma ba mu da karfin da za mu iya sayen shafukan jarida ko lokaci a gidajen rediyo don mu bayyana damuwarmu, to shi ne sai na ce ya kamata mu bayyana kokenmu a cikin waka tunda ita ba wata aba ce mai tsada ba.

Wannan shi ne dalilin da ya sa na zauna na fara rubuta waka. Wakata ta farko ita ce: “Mu fada mu fallasa ’yan hana Ningi ci gaba.”

To daga nan sai aka yi ina?

Daga nan sai muka tsunduma a harkar siyasa, kafin Abacha ya rasu akwai manyan mutane da na yi wa waka, kamar su marigayi Alhaji Abubakar Rimi da Alhaji Sule Lamido da Alhaji Isa Yahaya Zarewa da Alhaji Kabir dambatta duk na fara hulda da su a lokaci.

To bayan Janar Abacha ya rasu, sai wadannan mutane iyayen gidana da aka kakkama su, sai aka ce za a fito da jam’iyya.

To kafin a fito da jam’iyyar sai na zauna na yi nazari cewa tunda wadannan iyayen gida nawa ’yan siyasa ne duk jam’iyyar da za su fito ni ma a cikn zan fito.

Sai na fara nazari na tsara wa Jam’iyyar PDP wakoki nau’o’i uku. Lokacin da aka zo kaddamar da Jam’iyyar PDP a Ningi da Wazirin Bauchi Alhaji Bello Kirfi da su tsohon Gwamna Ahmadu Mu’azu da sauran shugabannin PDP suka hallara a nan ne na fara rera wakar siyasa a gaban jama’a.

Da suka ji ta yi, sai suka ce suna bukatar in buga ta, lokacin marigayi Shettiman Katagum (Alhaji Bashir Mustapha), Baraden Bauchi (Alhaji Umaru dahiru) lokacin yana Sakataren Jam’iyyar shi ya ba ni sunayen shugabannin jam’iyyar ya ce in kai masa kaset din. To daga nan aka fara baza wakar.

A cikin wakokin wacce ce kake ji ta fi karbuwa a lokacin?

A lokacin duk sun karbu wato da mai cewa:
“PDP muke so ku zo,
Ga jam’iyya.
Ku sa ta a zuciya al’ummar Najeriya.”
Da mai cewa:
“PDP jam’iyyata, abar so a zukata,
Mutanen Najeriya ku taso mu rike ta.”

To da su aka yi ta amfani a kasar Hausa wajen yada Jam’iyyar PDP.

Ko ka ci gajiyar wadannan wakoki?

A gaskiya ban ci gajiyar wakokin ba, sai bayan shekara biyu da buga wakokin. Domin na buga wakokin a 1998, a 1999 aka yi kamfe aka kafa gwamnati, to amma ban fara cin gajiyar wakokin ba sai a shekarar 2001, inda tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya ba ni mota kirar fijo sabuwa.

Daga baya sai aka ji ka yi mata wakar “Shegiyar Uwa mai kashe ’ya’yanta PDP…” Shin a lokacin ka fice daga cikin jam’iyyar ko wani abin takaici aka yi maka?

Har ga Allah a lokacin ban fita daga Jam’iyyar PDP ba, abin da ke mu da muka tallata ta, sai muka ga manufofinta da aka ba mu mu tallata ta an kauce musu. Da muka ga an kauce daga kansu sai muka ga ya kamata mu sanar da shugabannin jam’iyyar don su fahimci kura-kuran da suke yi don su gyara.

Kamar wadanne abubuwa ne kake ganin suka jawo ka yi wakar ta Shegiyar Uwa?

To abubuwan da suka faru, su ne duk jiga-jigan da suka taru suka kafa Jam’iyyar PDP ana bin su ana korarsu daga jam’iyyar da karfi da yaji. Kuma a lokacin babu ruwan PDP da zabe, duk abin da aka ga dama shi za a yi ba yadda tsarin jam’iyya ya tanada ba. Wannan shi ne abin da ya sosa min rai na yi wannan waka ta Shegiyar Uwa.

Mutanen da suka kafa jam’iyyar suka yi wahalar kafa ta su ake korewa daga jam’iyyar. To ni a matsayina na dillalin da ya yi tallar ta, bai kamata in zuba ido abubuwan suna tafiya haka ba, dole in yi wani abu da zai kare jam’iyyar.

Ba wanda ya sanya ni na yi wakar, a cikin jiga-jigan PDP akwai ma wanda ya yi kokarin kada in saki wakar ta Shegiyar Uwa.

Kana ganin wannan wakar ta kawo gyarar da kake magana?

Ba ta kawo gyarar da ake bukata ba, ku, a rashin wannan gyara ne ya jawo sanadiyyar da jam’iyyar ta ruguje gaba daya a yanzu.

Lokacin da aka yi wadannan abubuwa shi kansa Atiku lokacin da ya dawo PDP ya kira ni, cewa in zo in nazarin wakar da za a gyara PDP.

Na ce ranka ya dade ko na tsara wakar ba za ta yi wani tasiri ba, domin wadancan abubuwan da muke magana a kai gaskiya ne, kuma har yanzu ba a daina yin su a PDP ba.

Kuma in ba a daina yin su ba, babu ta yadda za mu gyara. Ya ce gaskiya ne. muka yi ta kokari, gyara bai yiwu ba, daga baya shi ma ya ga cewa tabbas abin ba zai gyaru ba.

Lokacin da ya sake fita ta biyu ne na yi wata waka mai cewa:

“Jam’iyyata ciwon ajali ya kama ta,
Wane ne ya dunkufa sai ya karya ki.”

Wace shawara za ka ba ’yan siyasa?

Shawarar da zan ba ’yan siyasa ita ce, akwai abubuwa uku da ya kamata su yi la’akari da su. Duk yadda ka kai a siyasa akwai ranar da ba kai ba ne.

Na biyu duk inda ka kai da mulki ka sani akwai wani mulki a saman naka. Na uku duk yadda ka kai a girma ka tabbatar cewa na kasan kasa ya taimaka.

Don haka kai ma ka rika tunawa ya taimaka maka. Wannan zai sa ’yan siyasa su rika tuna baya, suna yin adalci. Domin rashin adalci ke kawo rushewar mulki.

Ga jama’ar kasa kuma su zamo masu hakuri da fatar alheri, su guji mummunan zato ga masu mulki, su rika yi musu addu’a, sai a ga Allah Ya juya hankalin shugaba yana yin abin da ya dace.

Amma kada bambancin ra’ayi ya sa komai kyan abin da shugaba ya yi su ji cewa ba mai kyau ba ne saboda adawar siyasa.

Daga: Aminiya

[Music] Sabuwar Wakar Baba Buhari Akwai Saura - Matan Kannywood

Ibrahim Auwal | November 25, 2018 | 0 Comments

Sabuwar Wakar Da Matan Fim Din Hausa suka yiwa Baba Buhari Mai Taken Akwai Saura Danna Akan Download domin saukar wa

Download Now

Akwai Rashin Gaskiya A Harkar Fim Din Hausa - Fati Nijar

Ibrahim Auwal | November 24, 2018 | 0 Comments

SANIN kowa ne cewa tuni fitacciyar mawak'iya Binta Labaran, wadda aka fi sani da Fati Nijar, ta rikid'e ta zama jaruma kuma furodusa a Kannywood. Fati ta shirya finafinai da dama.

To sai dai kuma tun daga lokacin da ta fara shirya finafinan nata yau kusan shekara biyu kenan, fim d'aya ne kawai ya fito kasuwa, wato ‘Sakatariya’, wanda ita ce jarumar fim d'in. Irin bajintar da ta nuna a fim d'in ya sa ana ganin hakan zai kai ta ga matsayin da ta ke buri na zama fitacciyar jaruma, to kuma sai abin ya zama ba hakan ba;
Fati ba ta k'ara fitar da wani fim ba.

Hakan ya sa ana tambayoyi a bayan fage:

shin wai karaya ta yi ne ko kuma wani dalili ne ya sa ta jingine aikin?

Wakilin mu a Kano ya nemi jin ta bakin jarumar, inda ta amsa wannan tambayar da ma wasu. Ga tattaunawar tasu:

FIM: Hajiya Fati Nijar, kusan shekara biyu kenan tun da ki ka tsunduma cikin harkar shirya fim da fitowa a fim. A lokacin da ki ka fara, kin bugi k'irjin cewar za ki shirya finafinai masu yawa a kamfanin ki na Girma-Girma, to sai dai daga lokacin zuwa yanzu fim d'aya ne ki ka fitar. Ko dai kin karaya ne?

FATI NIJAR : To gaskiya ba karaya na yi ba, kawai dai an d'an samu jinkiri ne ban k'ara fitar da wani ba, shi ne ake ganin kamar na karaya. Masu kallo su zuba ido, nan gaba kad'an za su ga finafinai na da na shirya zan fito da su, kuma akwai wad'anda na ke shirin yi nan gaba kad'an, irin ‘Kasada’ da kuma ‘’Yar Maiganye’.

Sannan kuma akwai shirin da na ke yi na yin finafinai masu dogon zango, irin wad'anda ake nunawa a manyan gidajen talbijin a yanzu.

FIM: Rikid'ewar da ki ka yi daga mawak'iya zuwa jaruma ta mayar da ke wata Fati Nijar ta daban. Ko yaya ki ka ji da ki ka samu kan ki a haka?

FATI NIJAR : To ni dai gaskiya ban ji komai ba, amma dai zan iya cewa na samu d'an canjin yanayi saboda a matsayi na na mawak'iya kuma na koma ina yin aktin duk da cewa akwai bambanci sai dai ba wani yawa ba ne.

FIM: Bayan kasancewar ki jaruma, sai ya zama ke ce mai shirya fim d'in. Yin hakan bai sa aiki ya yi maki yawa ba?

FATI NIJAR : Ai ina ganin abin duk d'aya ne, mawak'i ma zai iya zama furodusa kuma jarumi. Wannan ne ma ya sa na ga ya kamata na rink'a yin furodusin, ba wai na tsaya kawai a wak'a ba.

FIM: Ita harkar furodusin a masana’antar fim yadda ta ke daban da yadda ake kallon ta. Ko yaya ki ka samu kan ki a matsayin ki na furodusa?

FATI NIJAR : A gaskiya akwai wannan. Ka san yadda harkar mutane ta ke, ba za ka iya gane halin mutum ba sai lokacin da harka ta had'a ku, don akwai rashin gaskiya sosai a wajen mutanen mu.

Sai ka ga su na ta yi maka dad'in baki, amma daga ka shiga hannun su, to sai dai Allah Ya fitar da kai.

FIM: A fim d'in ki na farko, ‘Sakatariya’, kin nuna jarumtar da masu kallo su ke ganin kin burge su. Ko yaya ki ke kallon wannan nasarar da ki ka samu a fim d'in?

FATI NIJAR : To haka ne, don wasu jama’a da dama sun ji dad'in aktin d'in da na yi, har ma su na cewa ai tun tuni ya kamata a ce na fara, wasu kuma su na cewa ya kamata na tsaya a wak'a ta.

Ka san mutane kowa da yadda ya ke kallon rayuwa, kuma da man shi fim d'in da na fara yi na fara ne don na samu wata k'warewa a harkar, kuma na yi koyi da sauran mawak'a na duniya; domin idan ka kula da yawa fitattun mawak'a na duniya za ka ga su na yin fim.

FIM: Kin tab'a fad'a mana cewar ki na so ki zama jarumar da ta sha gaban duk wata jaruma a harkar fim. Ko har yanzu ki na da wannan buri?

FATI NIJAR: In-sha Allahu kuwa! Burin ya na nan, kuma da yardar Allah zan cika burin nawa.

Salon fim d'in ‘Sakatariya’ ya bambanta da sauran finafinai ta sigar labari da kuma tsari. Me ya sa ki ka d'auki wannan salon?

FATI NIJAR : Haka ne. Ka san duk finafinan mu yawancin su labarin duk iri d'aya ne, kuma jigon su soyayya. Duk da ba laifi ba ne a nuna soyayya a fim, amma dai bai kamata ta rink'a zama ita ce jigon labari ba. To ni gaskiya ina so na kawo canji ne a masana’antar mu ta fim ta hanyar kawo abubuwan da ba a yin su a ciki.

FIM: To da wak'a da fim wanne ya fi cin lokaci?

FATI NIJAR : A gaskiya wak'a ta fi cin lokaci, saboda shi fim magana ce , kuma kafin ka fara sai ka haddace, amma ita wak'a sai ka tsaya ka yi tunani a k'wak'walwar ka. Sannan sai ka shafe tsawon sa'o'i uku ka na cikin situdiyo. Amma shi fim za ka iya yi a cikin minti talatin, idan an gama sin d'in ka ka yi tafiyar ka.

FIM: Ganin jarumtar da ki ka nuna a ‘Sakatariya’, an yi zaton za a rink'a ganin ki a sauran finafinai na wasu kamfanoni, amma sai ba a ga hakan ba. Ko dai kin tsaya ne a na kamfanin ki kawai?

FATI NIJAR : To ya danganta dai, don gaskiya ina da k'arancin lokaci ne, amma dai ana kawo mini aikin sai dai rashin lokaci, sai dai ina sa ran nan gaba kad'an zan rink'a ware lokaci na yin fim wanda zai zama ko wata shida ne a cikin shekara, don ya zama na samu damar yin finafinai har ma wad'anda ake gayyata ta.

FIM: A yanzu dai ki na nufin k'ofa a bud'e ta ke ga duk wanda zai gayyaci Fati Nijar aiki matuk'ar ya dace da ita?

FATI NIJAR : E, gaskiya haka ne. Duk wanda ya ke ganin na dace da fim d'in sa, to ya na iya zuwa ya same ni mu daidaita.

Sai dai kuma kamar yadda na fad'a maka, ina da k'arancin lokaci, amma dai hakan ba zai hana ni na yi fim ba.

FIM: Daga yadda ki ka kalli harkar fim bayan shigar ki, ki na ganin nan gaba akwai nasara?

FATI NIJAR : E, gaskiya za a iya cin nasara, amma dai sai an cire son zuciya, don gaskiya harkar fim mu na da buk'atar gyara sosai, kuma babbar matsalar da ta kashe harkar ita ce ba ma karb'ar gyara a daidai lokacin da ya dace, sai abu ya b'aci sannan za a zo ana yin kame-kame.

FIM: A yanzu harkar fim ta na cikin wani hali ta fuskar kasuwa. Me ki ke ganin ya kawo hakan?

FATI NIJAR : Gaskiya yanayin finafinan mu ne. Da kamar a ce mu na yin finafinai irin yadda ya dace da rayuwar mu, to da ba za a samu kai a cikin yanayin da ake ciki ba a yanzu.

FIM: Menene ya fi ba ki sha’awa game da harkar fim?

FATI NIJAR : To ka san ita harkar fim akwai nishad'i a cikin ta, kuma shi d'an’adam kullum ba abin da ya ke so kamar ya samu kan sa cikin nishad'i.

Don haka na kan samu kai na cikin farin ciki idan mu ka had'u a wajen lokeshin mu na wasa da dariya.
FIM: A matsayin ki na jaruma, wace shawara za ki ba abokan aikin ki?

FATI NIJAR : To gaskiya shawarar da zan bayar ita ce su zamo masu gaskiya da kamun kai, musamman ma mata, saboda wani lokacin idan mace ta na kama kan ta sai a ce ta na da girman kai, to ba girman kai ba ne.

Don haka mata ya kamata su gane matsayin su na ’ya’ya mata; ba ko’ina za su rink'a zuwa su na yin abu kai-tsaye ba. Don haka mata mu tsare mutuncin mu.

Daga: Mujjalar Fim

[Music] Sabuwar Wakar Da Matan Kannywood Suka Yiwa Buhari 2019

Ibrahim Auwal | November 18, 2018 | 0 Comments
Sabuwar Wakar Da Matan Kannywood Irin Su Jamila Nagudu ,Halima Atete Da Sauran Su Saka Yiwa Buhari A 2019

Danna Akan Download domin saukar wa

[Music] Tunkude Shi Atiku 2019 - Haidar Dabai

Ibrahim Auwal | November 18, 2018 | 0 Comments

Yau mun kawo muku sabuwar wakar Haidar Dabai Wanda Yake Waka Cike Da Basira Yayi Sabuwar Wakar Sa Mai Taken Tunkude Shi Atiku 2019

Danna Akan Download domin saukar wa

Download Now

[Music] I Love You - Dj Sboi

Ibrahim Auwal | November 16, 2018 | 0 Comments

Sabuwar Wakar I Love You Wanda Mawaki DJ Sboi yayi , waka ce cike da kalamai masu nishadantar da zuciya .

Ku Danna Akan Download domin saukar da wakarDownload Now

Banji Dadin Yada Jitar-Jitar Cewa Na Mutu Ba - Inji Idris Moda

Ibrahim Auwal | November 16, 2018 | 0 Comments

Fitaccen dan wasan Hausa Muhammadu Sani Idris Kauru wanda aka fi sani da Moda ya ce an kitsa labarin mutuwarsa da zummar cutar da shi.

A tattaunawar da BBC ta yi da shi a cikin jerin shirye-shiryeta na magance matsalar labaran karya, Moda ya ce bai ji dadi ba lokacin da aka rika yada labaran da ke cewa Allah Ya yi masa rasuwa.

A watan Mayu ne dan wasan na Hausa ya sha fama da rashin lafiyar da ta kai ga kwantar da shi a asibiti. Daga bisani ne aka rika yada jita-jitar cewa ya riga mu gidan gaskiya.

Sai dai hakan ya sa wasu abokan sana’arsa suka ziyarci asibitin suka dauki hotunan da aka watsa domin karyarta labarin mutuwarsa.

Shahararren dan wasan ya shaida wa BBC cewa hankalinsa ya tashi lokacin da ya samu labarin da ake watsawa na mutuwarsa.

“Hakika a wancan lokacin hankalina ya tashi saboda ban yi wata rashin lafiya da na gigice ba, wadda za a ce sakamakon hakan na fita hayyacina ba,” in ji shi.

Moda ya kara da cewa ransa ya yi matukar baci saboda an tashi hankulan iyalai da masoyansa, yana mai cewa wadanda suka baza labarin sun yi ne “domin su cutar da irinmu da muka yi fice.”

Daga : Aminiya

[Music] Sabuwar Wakar PDP Adon Tafiya

Ibrahim Auwal | November 16, 2018 | 0 Comments

Sabuwar wakar da akayi na pdp mai taken Adon Tafiya PDP.

Danna Akan Download domin saukar wa

Download Now

Na Karrama Yan Kannywood Ne Domin Cigaba Da Suke Kawo Wa A Alummah - Aisha Buhari

Ibrahim Auwal | November 15, 2018 | 0 Comments

Gidauniyar Aisha Buhari Foundation ta shirya taron ne domin kaddamar da sabuwar faifan waka da mawakan Kannywood suka shirya mai taken "sakamakon canji ".

Gidauniyar Aisha Buhari Foundation ta shirya taron ne domin kaddamar da sabuwar faifan waka da mawakan suka shirya mai taken "sakamakon canji".

Aisha Buhari tace wakar tana isar da sako game da irin ayyukan cigaba da gwamnatin mai gidanta, shugaba

Muhammadu Buhari , keyi kuma tace muhimmin abu ne jama'a su san irin aikin da gwamnati keyi wajen tallafa ma jama'ar kasa.

A sanarwar da shugaban yadda labarai na uwargidan, Suleiman Haruna , ya fitar, Aisha Buhari ta jinjina ma jaruman masana'antar nishadi ta Kannywood bisa ga gudummawar da suke bada wa wajen wayar da kan al'umma tare da haifar da zaman lafiya.

Ta ce ya zama dole a karramar jarumai domin rawar da suke takawa wajen cigaban gwamnati baya misaltuwa.

Taron wanda aka shirya daren ranar Laraba 31 ga watan oktoba ya samu halarcin shugaban kasa tare da wasu manyan ma'aikatan fadar sa.

Mawakan da jarumai sun nishadantar da baki da wakar inda mawaka 30 suka fito gaban taron wajen kwaikwayar wakar tare da taimakon jaruman fim masu rawa da amshi.

Shahararren mawaki Abdul Amart tare da wasu mawakan Hausa suka shirya wakar 'Sakamakon canji' mai bayyana ayyukan cigaba da gwamantin buhari ta aiwatar a wa'adan sa na farko da yin mulki.

Daga: pulsenigeria

Babu Soyayya Tsakanina Da Mawaki Akon - Inji Rahma Sadau.

Ibrahim Auwal | November 14, 2018 | 0 Comments
Babu Soyayya Tsakanina Da Mawaki Akon - Inji Rahma Sadau.Jarumar fim din hausa tayi magana akan cewa ita babu soyayya tsakaninta da mawakin amurka Aliane Damala Bouga, wanda akafi sanin sa da Akon.

Rahma Sadau ta fadi haka ne a gidan talabijin Arewa 24 a shirin Kundin Kannywood wanda Aminu Sharif Momoh shine yake gabatar da shirin a ranar talata.

"Banyi taba tunanin zan hadu Akon ido da ido ba. Nasan wakokin sa dadewa kafin yanzu domin shi shahararen mawakine . 
Lokacin dana amshi gayyatar shi nayi mamaki matuka naga wannan babbar damace da bazan iya wasa da ita ba" Inji Rahma Sadau

Lokacin da aka tambaye ta akan cewa yana son canza mata addini Rahma Sadau ta karya wannan jita-jitar tace wanda suke yada jita-jitar basu san Akon bane sabida shi mutum ne wanda yake aikata aiki irin na musulmai .

Tace ya gayyace ma suje umrah tare amma tace masa aa sabida tasan mutanen mu yazo zasu fara hada nasu labarin.

Rahma Sadau tayi magana akan sabon fim dinta wanda zai fito Mai taken "Mati A Zazzau"

[Music] Sabuwar Wakar APC Mai Taken Katin Zabe 2019

Ibrahim Auwal | November 12, 2018 | 0 Comments

Sabuwar wakar Dauda kahutu, rarara da sauran mawakan hausa sun saki waka Mai taken Katin Zabe

Danna Akan Download domin saukar wa a wayarku

Download Now

[Music] Sabuwar Wakar Dauda Kahutu Rarara Tare Da Fati Nijar

Ibrahim Auwal | November 11, 2018 | 0 Comments

Sabuwar wakar Dauda kahutu rarara tare mawakiya Fati Nijar Mai Taken Mudai Mun Taru A Tarayya

Ku Danna akan download domin saukar wa zuwa wayoyin ku

Download Now

Sallau Na Shirin Dadin Kowa Yayi Nadamar Sakin Matarsa

Ibrahim Auwal | November 11, 2018 | 0 Comments

Sallau Ya Nuna Nadamar Sakin Matarsa Da Yayi

Dama masana sunce aure igiya yake da ita. Har guda uku matsawar an furta kalmar saki to sakin ya tabbata. To kamar hakane ya faru tsakanin Sallau da tsohuwar matarsa Furera.
.
Komai yana da sila ko dalili amma banda ikon Allah. Dalilin da yasa Sallau ya saki matarsa yana da nasaba da zargi wanda Sallau yake yiwa Furera. Acewar Sallau ya saki matarsane saboda yana zargin tana bin maza ita Kwartuwa ce. To wan nnan shine silar sakin.
.
Amma abin mamaki da alama yanzu Sallau yana yin daya sanin sakin Furera. Domin har yanzu yana sa hotonsu a yanar gizo gizo. Kuma yana yawan yabon ta. To hausawa sunce yawan yabo so ne. Haka ya nuna yana yin daya sanin sakin matarsa.
.
Fatan Allah ya tabbatar da alkairinsa a tsakanin

[Music] Sabuwar Wakar Gwawmna Girma Ya Fadi - Direban Waka

Ibrahim Auwal | November 09, 2018 | 0 Comments
Sabuwar wakar sule direban Waka Mai taken Gwamna girma ya fadi[Waka] Sabuwar Waka Jafar Ya Fede Birin Kano Yaci Dalla

Ibrahim Auwal | November 08, 2018 | 0 Comments

Danna Akan Download Domin saukar da sabuwar Waka Mai taken Jafar Jafar Ya Fede Birin Kano Yaci Dalla ..

Download Now

Jaruma Fati Mohammed Ta Fara Canza Zabin Yan Kannywood Tafiyar Buhari Zuwa Atiku 2019

Ibrahim Auwal | November 07, 2018 | 0 Comments
Bayan Jaruman masana'antar shirya fina finan Hausa dake Arewacin Najeriya Kannywood sun tabbatar tare da jaddada aniyar bayar da cikakken goyon baya ga shugaban kasa Muhammad Buhari, musamman a zabukan shekarar 2019 dake tafe.
A saboda haka ma Fadar Shugaban kasa ta gayyaci jaruman maza da mata don nuna jin dadi goyon bayan daga gare su har ma suka karrama su da Lambobin girmamawa.
To sai dai rahotanni sun bayyana karara cewar Jaruma Fati Mohammed, tana yima Jaruman masana'antar dauki daidai suna sakin tafiyar Shugaban kasa Muhammad Buhari dake APC, suna kama ta Dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, don har hotunan ziyarar da take kaiwa jaruman sun fara bayyana a kafar soshiyal midiya.

Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar yanzu haka Jaruma Fati Mohammed tayi nasarar chanza wa wasu daga cikin Jaruman akalar tunani.

Dama chan dai wasu jarumai suna ta korafe korafe kan cewar lokacin tafiya fadar shugaban kasa tafiya aka yi aka bar su hasalima basu da labari suma dai kawai hotunan ziyarar suka gani a kafafen sada zumunci na zamani.

Daga: Jaridar Dimokuradiyya

Mawaki Akon zai tsaya takarar Shugaban Amurka

Ibrahim Auwal | November 05, 2018 | 0 Comments

Mawaki Akon zai tsaya takarar Shugaban Amurka

Fitaccen maqakin nan na Rap a kasar Amurka wanda dan asalin kasar Senegal ne ya bayyana cewa yana tunanin zai tsaya takarar shugabancin kasa a Amurka a zaben 2020.

Jaridar Guardian ce ta ruwaito hakan daga wata tattaunawa da mawakin ya yi da jaridar Newsweek, inda ya ce, “ina tunanin zan tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2020. Amma ba wai kawai ina so in yi takarar ba ne, ina fata mutane za su nuna cewa muna bukatar ka tsaya takara.”

A game da hanyoyin da Trump ya dauka na kasar, Akon cewa ya yi, “Gaskiya ina cikin takaici. Ban jin dadi. Na san lallai akwai fama sosai.

Dole zan shirya sosai domin yawancin mutane har da fararen fata ma suna cikin damuwa bisa yadda yake tafiyar da kasar. Amman an gaba akwai sauki.”

Daga: Jaridar Aminiya

Shugaban Kasa Buhari Bai Bamu Kudi Ba - Rabiu Rikadawa

Ibrahim Auwal | November 03, 2018 | 0 Comments

Fitaccen jarumin fim din Hausa, Rabi’u Rikadawa wanda aka fi sani da Dila ya bayyana cewa duk wanda ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba su kudi a lokacin da suka kai masa ziyara ba gaskiya ya fada ba.

“Duk wanda ya fada maka an ba ‘yan fim da suka je wajen Shugaba Buhari kudi to ba gaskiya ya fada ba, kowane ne shi.”

Rabi’u Rikadawa ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya zo yin aikin wasan kwaikwayo na BBC media action a Sakkwato a makon da ya gabata, inda ya ce ziyarar da suka kai ba wanda aka tursasa sai ya je,

“Maganar akwai bambancin ra’ayi masana’antarmu ai ko dan da ka haifa a cikinka sai ka same su da bambancin ra’ayi. Haka ne a duniya gaba daya, amma ita tafiya in za ka yi ta za ka nemi masu irin ra’ayinka ka yi tafiya da su don haka muka je ba don a raba mana kudi ba.

“Duk mutumin da hankali ya ratsa shi yakan dubi rayuwa ce ya ge me gaba za ta samar don samun rayuwa mai inganci. Mun dubi tsarin shugaba Buhari mai yin aiki ne da mutane za su amfana, ba wai ya dauko kudi ya baka ba.

“Dubi yadda ya daudo aikin wuta na Mambila, ga aikin hakar mai a Bauchi da Borno da Katsina. Irin wadannan abubuwa da kishinsa ga Arewa muka ga ya kamata mu goyi bayansa.

“A ziyarar mun samu nasara ya fahimce mu ya san halin da muke ciki a masana’antarmu, na abun da ya fi ci mana tuwo a kwarya ta satar fasaha da ake mana. Misali a nan Sakkwato kana iya samun mutum miliyan 7 a cikinsu za a samu miliyan 2 da ke kallon fim din Hausa, amma za ka samu dubu 100 da ke sayen fim dinmu wajen masu satar fasaha suke saye. In an hana satar fasahar nan muka rika samun ko rabin masu kallonmu suna sayen fim gare mu, kudin da muke kashewa za su rika dawowa. Kuma mun yi godiya da tallafin bashi da gwamnati ta baiwa wasunmu suna jujjuyawa.”

A game da kallon da mutane ke musu a matsayin masu bata al’ada da tarbiyar Bahaushe, cewa ya yi, “Ba ka isa ka kawar da mutane daga tunaninsu ba sai dai yau da gobe a hankali domin wannan al’ummar tana da wuyar daukar sauyi.

Ko masallacin fadar Sarkin Kano da aka sanya lasifika sai da aka yi zanga-zangar cewar an kawo bidi’a sai da aka turza kafin aka karbi canjin. Duniya gaba daya canjawa take yi, in ka ki canjawa sai ka zama bigidaje.

“Da ganin wasu fim ka san an shigo da malaman, har lambar yabo sun ba wasu daga cikinmu. Lamarin ba dole kowa ya gamsu da kai ba, in ka ci karo da abin da kake so ka dauka.”

Daga : Jaridar Aminiya

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger