YA KAMATA MU NEMI AFUWAR SHEIKH DR. AHMAD GUMI

Ibrahim Auwal | January 31, 2019 | 0 Comments

YA KAMATA MU NEMI AFUWAR SHEIKH DR. AHMAD GUMI

A baya can, mun kasance masu kausasa harce idan Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya yi magana akan siyasar Nijeriya, a yanzu mun fahimci cewa mun yi kuskure idan muna masa raddi akan abar banza siyasar Nijeriya.


Maganar gaskiya yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya lamari ne mai girma da rikitarwa wanda da wahala ace an kawo karshen cin hanci da rashawa, duk ta'asar da 'dan siyasa zai tabka, da duk irin cin amanar da zai aikata da satar dukiyar al'umma ko da tallafawa ayyukan ta'addanci ne, to yana dawowa cikin jam'iyya mai mulki magana ya kare.

Na taba jin Dr. Ahmad Gumi ya furta wata kalma wanda sai a yanzu ne na fahimci gaskiyar abinda ya furta, yace a batun yaki da cin hanci da rashawa karya ne 'they are all corrupt'. Ma'ana dukkan su maciya rashawa ne.
Duk inda mutum ya kai ga biyewa bangare daya a 'yan siyasar Nijeriya to zai iya kunyata daga karshen al'amari.

Allah Ya sauwake
Daga Datti Assalafiy

Shugaba Buhari ya daga hannun gwamna Ganduje ya bukaci a zabeshi karo na biyu

Ibrahim Auwal | January 31, 2019 | 0 Comments

Shugaba Buhari ya daga hannun gwamna Ganduje ya bukaci a zabeshi karo na biyu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya daga hannun gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a wajan yakin neman zaben da yaje yi jihar inda, ya bukaci da a sake zabenshi a matsayin gwamnan jihar Kano.Gwamna Ganduje dai yana cikin wata kwamacalar karbar kudin da aka ganshi a cikin wani bidiyo da jaridar Daily Nigerian ta wallafa bidiyon da ya dauki hankula sosai a kasarnan.

Gwamnan dai ya musanta cewa ba shine a bidiyon ba, siddabarun zamani aka yi amfani dashi wajan hada bidiyon.

Sannan gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari nada muradu uku da take yakin neman zabe dasu, samar da tsaro, yaki da rashawa, da kuma habbaka tattalin arziki.

Shugaban jam'iyyar APC dai, Adams Oshiomhole ya taba bayyana cewa duk laifin da dan siyasa yayi idan ya koma jam'iyyar ta APC to an yafe mai laifin, kalaman shugaba Buhari yayi gum akansu.

Ko Buhari zai daga hannun Ganduje a ziyararsa ta Kano? 31 Janairu 2019

Ibrahim Auwal | January 30, 2019 | 0 Comments
Shugaba Muhammadu Buhari
A ranar Alhamis ne ake sa ran shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai kai ziyarar yakin neman zabe jihar Kano.
Zuwan Buhari Kano don yakin neman zabe, ya zo da takaddama a tsakanin 'yan siyasa da sauran al'umma a ciki da wajen jihar, musamman bisa la'akari da hotunan bidiyon, da ake zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da karbar rashawa

Duk da dumbin muhimmancin wannan ziyara ga shugaban kasar da ma gwamnan jihar na nuna wa abokan adawa karfin farin jinin da suke da shi a jihar wadda ta kasance mai yawan jama'a a kasar, takaddama da ce-ce-ku-ce, sun zamewa zuwan shugaban kasar wani tarnaki.
Magoya bayan gwamnan jihar, na fatan cewa wannan ziyara ta shugaba Buhari, za ta kawo karshen rade-radin tsamin dangantakar da ake zargi ta shiga tsakanin Ganduje da Buhari.
Wasu dai na cewa wai shugaban kasar a yanzu, baya ma son hada hanya da 
Wannan dambarwa dai ta taso ne watanni hudu da suka shude a lokacin da aka fara kwaza labarin cewa an dauki hotunan gwamnan na Kano na karbar cin hanci daga hannun 'yan kwangila, kafin daga bisani jaridar Daily Nigerian ta fitar da wasu hotunan bidiyon da suka nannaga wannan zargi.
Gwamnatin jihar Kano dai ta musanta wannan zargi, inda daga bisani ma ta shigar da dan jaridar da ya wallafa bidiyon a kotu.
Duk da wannan dambarwa, akwai dumbin magoya bayan shugaban kasar da suke maraba da zuwansa, wasun su ma domin su ji inda gwamnatinsa ta kwana game da wannan zargi da ake yi wa gwamnan na jihar Kano.
Wani daga cikin magoya bayan shugaban kasar ya shaida wa BBC cewa' Talakawa sun zuba ido su gani ko mai girma shugaban kasa idan ya zo jihar Kanon, zai daga hannun gwamna Ganduje ko kuma akasin haka'.
Wannan batu na karbar goro da ake zargin gwamnan na Kano, shi kowa ke jira ya ji matsayin shugaban kasar a kai.
A bangaren 'yan adawa a jihar kuwa, cewa suka yi su sam ba sa maraba da wannan ziyara ta shugaban kasar.
'Yan adawan sun shaida wa BBC cewa, su fa ba sa farin ciki da wannan ziyara domin kuwa ba bu abin da shugaba Buharin ya yi wa jihar Kano sai gidan 'Kurkuku'.
Zuwan shugaba Buhari jihar Kano dai ya bijiro da dumbin tambayoyi da suka hada:
  • Ko idan ya zo zai daga hannun gwamna Ganduje, idan ya daga hannun na sa ina makomar kimar shugaban?
  • Shin ko ziyarar shugaban kasar za ta kawo mafita ga zarge-zargen cin hancin Ganduje?
Sanin amsoshin wadannan tambayoyin, sai an ga abubuwan da suka biyo baya bayan zuwan Buhari Kanon

Idan na yi rashin nasara a zabe me zuwa zan yadda>>Atiku

Ibrahim Auwal | January 30, 2019 | 0 Comments

Idan na yi rashin nasara a zabe me zuwa zan yadda>>Atiku

A wata hira da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP,Atiku Abubakar da mataimakinshi, Peter Obi a gidan talabijin na NTA ya bayyana cewa idan ya fadi zabe me zuwa zai hakura.Atiku ya bayyana cewa idan dai an gudanar da zaben gaskiya babu magudi babu abinda zai hanashi yadda da kaye tunda ba wannanne karin farko da yake faduwa a zabe ba.

Shugaba Buhari yaje yakin neman zabe Ebonyi

Ibrahim Auwal | January 30, 2019 | 0 Comments

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan a yayin da ya isa jihar Ebonyi dan yin yakin neman zabenshi, ya saka kayan Inyamurai yayin ziyarar tashi.Dan Uwan Shugaba Buhari Na Neman Dan Majalisar Tarayya A Katsina

Ibrahim Auwal | January 30, 2019 | 0 Comments

Dan Uwan Shugaba Buhari Na Neman Dan Majalisar Tarayya A Katsina

Dan Uwan Shugaba Buhari Kenan, Wato Fatihu Muhammad, Yayin Da Yake Zagayen Neman Kujerar Majalisar Tarayya Ta Daura.
Rariya.

Karin hotunan yanda Rahama Sadau ta yi murnar kammala Karatunta

Ibrahim Auwal | January 29, 2019 | 0 Comments

Karin hotunan yanda Rahama Sadau ta yi murnar kammala Karatunta

Wadannan karin hotunan yanda tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta yi murnar kammala karatunta tare da 'yan uwanta kenan, sun haskaka, muna musu fatan Alheri.


Ba mu da kudin da za mu rika rabawa mutane>>Shugaba Buhari

Ibrahim Auwal | January 29, 2019 | 0 Comments

Ba mu da kudin da za mu rika rabawa mutane>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa,gwamnatinshi bata da kudin da zata rika rabawa mutane, maimakon haka zata yi amfani da kudinne wajan yin ayyukan raya kasa.Buhari ya bayyana hakane jiya, Litinin wajan taron karawa juna sani da jam'iyyar APC ta shiryawa membobinta akan yanda zasu watsa manufofinta ga masu zabe.

Shugaban ya bayyana cewa, zasu yi amfani da kudin gwamnatine wajan yin ayyukan raya kasa irinsu, tituna, titunan jirgin kasa dadai sauransu dan haka ya bukaci wadanda suka samu horaswa a taron da su je su jawo hankalin 'yan Najeriya da su zabi APC tare da gayamusu muhimmancin kuri'arsu.

Shugaban ya kara da cewa a kullun rana ta Allah da Tunanin Najeriya da al'ummarta yake kwana yake tashi.

Majalisar tarayya ta tabbatar da dubu 30 mafi karancin Albashi

Ibrahim Auwal | January 29, 2019 | 0 Comments

Majalisar tarayya ta tabbatar da dubu 30 mafi karancin Albashi

Majalisar wakilai ta tabbatar da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin Albashi a kasarnan, majalisar ta tabbatar da hakanne a zaman da ta yi na yau, Talata inda hakan ya saba da dubu 27 da majalisar koli ta aminta dashi.Zaman majalisar wanda kakakin majalisar, Yakubu Dogara ya jagoranta, ya bayyana cewa sun amincene da rahoton wani kwamiti da suka kafa akan mafi karancin Albashin sannan sun yi la'a kari da irin halin matsin da ake ciki a kasarnan wajan daukar wannan mataki.

Yanzu dai za'a mikawa majalisar dattijai wannan kudiri dan ta tabbatar dashi, a cikin kudirin me kamfani ko wata ma'aikata da yawan ma'aikatan da yake biya albashi basu kai mutum 25 ba baya cikin wannan tsari na biyan mafi karancin Albashi.

An Tura Mayaka Mata Domin Fatattakar Boko Haram

Ibrahim Auwal | January 29, 2019 | 0 Comments

An Tura Mayaka Mata Domin Fatattakar Boko Haram

Rundunar Sojojin Sama ta Kasa, NAF ta bada sanarwar tura zaratan sojojin sama mata da ake kira Mata Zaratan Yaki zuwa yankin Arewa maso Gabas domin yin gumurzu da Boko Haram.


Babban Hafsan Hafsoshin Sama, Sadique Abubakar ya ce a yanzu haka akwai da dama da ke gwabza yaki tare da zaratan musamman a wurare daban daban.

Ya shaida wa PRNigeria cewa NAF babu ruwanta da nuna bambanci, kuma ta na kara cicciba kowane jinsi domin ya samu karin horo da goguwar kwarewa a aikin sa.

“ Mu na kiran su da suna Mata Zaratan Yaki ne saboda sun horu, sun gogu kuma sun samu kwarewa wajen iya gwabza gumurzun fada a duk inda aka kai su, ko kuma inda suka samu kan su.

“ Su ma wadannan matan kamar abokan aikin su maza su ke. Sun kware sosai wajen kakkabe abokan gaba masu ta’adda musamman wajen iya kai farmaki daga sama, tare da bada dauki ga sojojin da ke gumurzu da Boko Haram a kasa.

Ya ce sun samu horo a cikin Najeriya da kuma kasashen Turai.

Shaye-shaye ko neman kananan yara za'ayi da kudin>>Teema Makamashi ta mayar da martani akan kudin da Ummi Zeezee tace abokan aikinta sun cinye

Ibrahim Auwal | January 29, 2019 | 0 Comments
Bayan da taurruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta caccaki wasu daga cikin abokan aikinta akan cinye kudin da ta yi zargin sun yi wanda tace dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya bayar a rabawa 'yan Kannywood, abokiyar aikinta, Teema Makamashi ta mayar da martani me ban mamaki.Teema ta baiwa Ummi amsar cewa, Wallahi ba abinda zai musu karshema shanye kudin za ayi a shaye shaye ko kuma anemi yara kanana da kudin azzalumai kawai.

Wannan dai ya jawo wasu na tambayar cewa kada kudi yasa su rika tonawa abokan sana'arsu asiri.

Ku Zabi Mai Gaskiya Da Rikon Amana, Cewar Sheikh Bala Lau

Ibrahim Auwal | January 29, 2019 | 0 Comments

Ku Zabi Mai Gaskiya Da Rikon Amana, Cewar Sheikh Bala Lau

Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa Ikamatus Sunnah na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci jama'ar Najeriya da su duba Mutum mai gaskiya da rikon amana su zabe shi a matsayin Shugaban Kasa, a babban zaben dake tafe.


Sheikh Lau ya cigaba da cewar, babban abinda ake nema a Shugabanci shine gaskiya da rikon amana a wajen Shugaba, dukkanin Shugaban da aka san shi da kamanta gaskiya da rikon amana shine Shugaban da ya dace Jama'a su zaba, kuma lallai Jama'a su guji dukkanin shugaba wanda yayi kaurin suna ta fuskar cin amana da rashin gaskiya.

Malamin yayi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gidanshi dake Kaduna dangane da batun zabe da ya kunno kai.

Imam Bala Lau ya kuma yi nasiha ga dukkanin 'yan takara musanman na Shugaban Kasa da cewar su amince da sakamakon zabe da Hukumar zabe zata fadi, domin hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a kasa, da dorewar shi kanshi mulkin na Dimokuradiya.

Shugaban Izalan ya kuma yi kira ga Hukumar Zabe ta kasa da cewar, tubalin zaman lafiyar kasa yana a hannun su ne, domin sune kadai suke da alhakin sanar da sakamakon zabe, to don Allah kada su amince wani ya saye su da kudi domin su canza sakamakon zabe, su sani cewa amana ce aka basu, kuma Allah zai tambaye su akan wannan amana gobe Kiyama.
Rariya.

Ummi Zeezee ta bayyana manyan 'Barayin Kannywood 5' bayan da ta zargesu da cinye kudin da Atiku ya bayar a rabawa 'yan Kannywood

Ibrahim Auwal | January 29, 2019 | 0 Comments

Ummi Zeezee ta bayyana manyan 'Barayin Kannywood 5' bayan da ta zargesu da cinye kudin da Atiku ya bayar a rabawa 'yan Kannywood

Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta yiwa wasu daga cikin abokan sana'arta kaca-kaca akan wasu kudi da tace dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya bayar a rabawa 'yan Kannywood masu yinshi amma suka raba kudin tsakaninsu.Abokan aikin nata da ta kira fitattun barayi 5 na Kannywood sune, Sani Musa Danja, Fati Muhammad, Zaharadeen Sani, Buhari Alamin da me bayar da umarni, Eemrana.

A cikin wani zungureren rubutu da tayi a shafinta na sada zumunta tace taso ta dauresu akan wannan abu amma mahaifiyarta ta hanata tace ta barsu da Allah.

Ga abinda tace kamar haka:

” Zuwa ga Fati Mohd, Sani Danja, Zaharaddeen Sani, Al’amin Buhari and director eemrana….

” A ranar JUMA’AR data gabata mai girma dan takaran shugaban kasa ta jam’iyar PDP Alhaji atiku Abubakar ya shirya wani taro da zaiyi da yan fim da kuma mawaka na kannywood dan gane da siyasarsa sai dai kuma Allah bai bashi ikon zuwa ba sai ya wakilta sir Bukola Saraki Wanda daya zo taron ya bada kyautan makudan kudi miliyoyi ga jarumai da kuma mawakan kannywood Wanda suke PDP suke kuma yiwa wazirin adamawa kamfen.

“Ammah sai gashi saboda son zuciya irin taku kuda na lissafo sunayenku kuka raba kudin a iya tsakaninku kawai ko wanne acikinku ya dau naira million hudu da rabi saboda zalinci tsantsa.

” To shi ai bukola sarakin ba ku kadai ya bawa kudin ba da zaku rabashi kawai a tsakanin ku shi cewa yayi ya bayar ga duk yan PDP na kannywood masu yin atiku wai ammah sai kuka fara kawo uzurin karya cewar wai acikinku ko wani mutum ya gaiyato mutum hamsin ne domin taron shiyasa kuka raba kudin a tsakaninku Wanda kuma karya ne ba wasu mutane hamsin hamsin da kuka kawo taron domin nima na je taron kuma a matsayina na babbar yar PDP mai manyan mukamai har biyu baku bani nawa kudin ba.

” Sai bayan an tashi daga taron ne na kira actor zaharaddeen sani awaya ina tambayar nawa kudin wai shine dan renin hankali ya aikomin da naira dubu 25k kawai sai kace ya daukeni yar jagaliyar siyasa koko ince ya daukeni matsiyaciya ko yar yunwa.

” Dan haka wannan wasika na muku ne domin in muku gargadi.

” Wallahi wallahi wallahi in aka sake hada taron daya shafi atiku abubakar kuka raba kudi bani aciki to duk sai na kulleku a DSS na abuja baza a barku ba har sai kun biyani kudina domin na tabbatar acikinku ba mai connection din da nake dashi a Nigeria kuma ko wannan kudin ma dakuka dannemin rabo na naso na rufeku duka shine danayiwa mamana waya na gayamata ta hanani tace rigima ba dadi in barku da Allah kawai zai sakamin shiyasa na rabu daku bawai dan ina tsoronku ba domin naga sauran mutanen da sukaje taron kuka hanasu hakkinsu tsoro ya hanasu magana.

” Dan haka acikinku in akwai dan iska to dan allah in an sake bada kyautan kudi akan siyasar atiku mutum yaci nawa yaga mezaifaru!macutan banza kawai!!"

HAKO MAN FETUR: Jihar Bauchi Na Dab Da Zama Kamar Jihohin Niger Delta

Ibrahim Auwal | January 29, 2019 | 0 Comments

HAKO MAN FETUR: Jihar Bauchi Na Dab Da Zama Kamar Jihohin Niger Delta

Nan gaba kadan da yardar Allah jihar Bauchi ita ma za ta zamo kamar jihohin Niger Delta masu arzikin man fetur.Wadannan hotuna da kake gani 'kari ne game da rahotannin da muke kawo muku game da kokarin da Shugaba Buhari yake yi don raya kasar mu musamann Arewa, aikin tonon rijiyoyin mai a kauyen Kolmari dake karamar hukumar Alkaleri, cikin jihar Bauchi.

Hakika akwai jin dadi ga 'yan kasar nan cikin shekaru kadan masu zuwa in sha Allah.
Rariya.

KALLI ALJANIN DA AKE TUNAIN YA HALARCI TARON KWANKWASIYYA

Ibrahim Auwal | January 28, 2019 | 0 Comments

KALLI ALJANIN DA AKE TUNAIN YA HALARCI TARON KWANKWASIYYA

Wata halitta da jama'a suke tunanin Aljani ne ya bayyana cikin suffar dattijo 'WAI' ya sauko daga sararin samaniya a kan keke, lokacin da ake taron Kwankwasiyya a karamar hukumar Birni.


Da mutane suka tambaye shi, me ya kawo ka? Sai yace "Nazo ne domin naga Kwankwaso"
Sarauniya.

Rahama Sadau ta kammala karatun jami'a

Ibrahim Auwal | January 28, 2019 | 0 Comments

Rahama Sadau ta kammala karatun jami'a

Tauraruwar fina-finan Hausa,Rahama Sadau ta kammala karatun jami'ar da take yi a Cyprus wanda ta samu shaidar kallama karatu daga jami'ar Eastern Mediterranean, Rahamar ta bayyana hakane a shafukanta na sada zumunta inda tace kamin a kammala kamar ba za'a gama ba.


Muna tayata murna da fatan Allah ya sawa karatu Albarka.

Najeriya ta gargadi kasashen ketare kan yi mata katsalandan

Ibrahim Auwal | January 28, 2019 | 0 Comments

Najeriya ta gargadi kasashen ketare kan yi mata katsalandan

Gwamnatin Najeriya ta gargadi kasashen ketare da su kaucewa yin katsalandan kan al’amuran da suka shafi kasar, wanda ka iya haifar da rudani, rashin yadda da juna tsakanin ‘yan Najeriya, da kuma haifar da shakku kan sahihancin zabukan kasar.Gargadin na kunshe cikin sanarwar da kakakin gwamnatin Najeriyar Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja.

Gwamnatin Najeriya dai ta maida martani ne kan tsokacin da wasu kasashen ketare da suka hada da Amurka Birtaniya da kuma kungiyar EU suka yi, kan matakin shugaban kasar Muhammadu Buhari, na dakatar da Alkalin Alkalai mai shari’a Walter Onnoghen, tare da nada Mai shari’a Ibrahim Tanko a matsayin mukaddashi.

Sanarwar ta yi amfani da kakkausan harshe wajen sukar duk wani yunkurin yin katsalandan kan al’amuran Najeriya da kai iya rura wutar sabani tsakanin ‘yan kasar ko kuma haddasa rashin yadda da tsarin dimokaradiyar da take kai.

Majalisar dattijan Najeriya dai, ta tsaida Talata mai zuwa, a matsayin ranar da za ta tattauna kan matakin bangaren zartarwa na dakatar da Onnoghen.

Shugaban majalisar dattijan Bukola Saraki, wanda ya bukaci zaman na musamman a ranar Talatar, ana sa ran ganawarsa da sauran jagororin majalisar a ranar Lahadi.

Ranar Juma’ar da ta gabata Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya dakatar da alkalin alkalai Walter Onnoghen, har sai an kammala yi masa shari’a kan zargin kin bayyana wasu kadarori da ya mallaka, cikin har da kudaden kasashen ketare a asusunsa, inda aka maye gurbinsa da mai shari’a Ibrahim Tanko a matsayin mukaddashin alkalin alkalan.
RFIhausa.

Kannywood Atiku zata zaba>>Yakubu Muhammad

Ibrahim Auwal | January 28, 2019 | 0 Comments

Kannywood Atiku zata zaba>>Yakubu Muhammad

Taurarron fina-finan Hausa, Yakubu Muhammad ya bayyana cewa, masana'antar Kannywood dan takarar shugaba kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zata zaba saboda suna fatan zai tallafa musu idan ya zama shugaban kasa.Yakubu Muhammad ya bayyana hakane a wajan wani taro na musamman da wakilan Atiku Abubakar suka yi na jin ra'ayin jama'a a Kaduna, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Yakubu yace suna yin fina-finai marasa inganci wanda matsalar rashin shugabanci na gari ne ya jawo hakan.

Sannan a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai iya tuna cewa, ya bayar da tallafin miliyan 200 ga masana'antun nishadantarwa. Dan haka Atiku zasu yi.

ZABE: INEC na bukatar ma’aikata 15, 545 a Kwara, miliyan 1.2 a Najeriya>>Yakubu

Ibrahim Auwal | January 27, 2019 | 0 Comments

ZABE: INEC na bukatar ma’aikata 15, 545 a Kwara, miliyan 1.2 a Najeriya>>Yakubu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta ce za ta tura ma’aikatan gudanar da zabe har 15, 545 a jihar Kwara domin gudanar da zaben 2019.


Kwamishinan Zabe na Tarayya da ke Jihar Kwara, Garba Attahiru Madami ne ya bayyana haka a Ilorin babban birnin jihar.

Ya ce ana bukatar ma’aikatan wucin-gadi 13, 199 da za su yi aikin gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya.

Sauran sun hada da jami’an zaben na dindindin.

Sannan kuma ya ce za a tura masu bautar kasa, wato NYSC har 7, 567 domin gudanar da zaben.

A wani jikon kuma, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC ta na bukatar akalla jami’an gudanar da zabe da jami’an tsaro a kalla milyan 1.2 domin gudanar da zaben 2019 a fadin kasar nan.

Yakubu ya bayyana hakan ne a Kano, inda ya jaddada cewa INEC na bukatar akalla jami’an tsaro 360 da za su kula da rumfunan zabe a lokacin da ake gudanar da zabuka a ko’ina cikin kasar nan.

Shugaban na INEC ya yi wannan bayani ne ta bakin Sa’ad Idris, Shugaban Cibiyar Zabe ta Kasa da ya wakilce shi.

An shirya taron ne a Kano domin sanin makamar aiki lokacin zabe ga jami’an tsaro.

Tare da hadin guiwar Cibiyar Tallafa wa Zabuka ta Kungiyar Tarayya Turai aka shirya taron.

Kasancewa Najeriya na da masu jefa kuri’a har milyan 84, Yakubu ya ce Najeriya ce ta biyu a yawan masu jefa kuri’a a kasar da ake dimokradiiya a duniya.

Yakubu ya hori jami’an tsaro su yi aiki tsakanin su da Allah kamar yadda doka ta tanadar domin a tabbar da samun ingantacce, sahihi kuma karbabbe.
Premiumtimeshausa.

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger