Home » » Shekaru Goma (Kenan Atiku Abuakar Yana Daukar Nauyin Ciyarwa A Masallacin Makkah Da Madina>>Almustapha Bin Abdallah Al-Aradhy

Shekaru Goma (Kenan Atiku Abuakar Yana Daukar Nauyin Ciyarwa A Masallacin Makkah Da Madina>>Almustapha Bin Abdallah Al-Aradhy

Ibrahim Auwal | January 09, 2019 | 0 Comments

Shekaru Goma (Kenan Atiku Abuakar Yana Daukar Nauyin Ciyarwa A Masallacin Makkah Da Madina>>Almustapha Bin Abdallah Al-Aradhy

Wani bawan Allah daga  garin Makkah ta Kasar Saudia, mai Suna Almustapha Bin Abdallah Al-Aradhy wanda kuma ma'aikaci ne a masallacin Haramin Makka yace yau shekaru Goma kenan Alhaji Atiku Abubakar yana daukar nauyin ciyar da miliyoyin al’ummar musulmi a Haramin Makka da Madina a yayin aikin Hajji da Umrah a kasar Makka.


Almustapha ya wallafa wannan bayani ne a shafin sa na Twitter a ranar 6 ga watan Janairun 2019.
Almustapha Al-Aradhy yace :- "Ina farin ciki tare da  godiya ga Allah da ya nuna mun wani bawan Allah daga kasar Najeriya mai Suna Atiku Abubakar, wanda kuma shine mutum da ya tilo daga kasashen Afirika wanda yake daukar nauyin ciyar da miliyoyin musulmi a Haramin Makkah da Madina”. 
Da yake zantawa da wakilin Saudi Gazette ta wayar tarho, Almustapha Bin Abdallah Al-Aradhy yace “Na san Atiku Abubakar ne a Haramin Makka tun a shekarar 2009 lokacin da ya fara daukar nauyin ciyar da al’umma a lokacin bude baki na  watan Ramadan, da masu Azumin Litinin da Alhamis, kasancewar shi Atiku mutum ne mai yawaita Azumin Litinin da Alhamis a kowani mako”. 
“Tabbas wannan bawan Allah Atiku ya cancanci na yaba masa kasancewar sa mutum daya tilo daga Afirika da yake daukar nauyin ciyarwa a masallacin Haramin Makka da Madina.” A cewar Almustapha Bin Abdallah Al-Aradhy.
Rariya.
Share this article :

0 Comments:

Post a Comment

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger