ATIKU: Abin da yasa nake kalubalantar nasarar da Buhari yayi

Ibrahim Auwal | February 28, 2019 | 0 Comments

ATIKU: Abin da yasa nake kalubalantar nasarar da Buhari yayi

Dan takarar zaben shugaban kasa Atiku Abbakar wanda ya zo na biyu, ya bayyana dalilan sa na kalubalantar zaben da INEC ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya yi nasara.


Atiku ya rasa kujerar ta shugaban kasa ne, bayan da Buhari ya ba shi tazarar kuri’u sama da miliyan uku.

Tuni dai tun jiya INEC ta mika wa Shugaba Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo takardar shaidar cin zabe jiya Laraba.

Sai dai kuma Atiku ya ce ba zai taya Buhari murna ba, kuma ya kira zaben da cewa fashi da sata ce karara aka yi wa jama’a, na abin da ra’ayin su ya zabar musu.

A taron manema labarai da ya kira, Atiku ya buga misali da Akwa Ibom, ya ce tashinn farko akwai alamomin tambaya dangane da yadda aka samu raguwar wadanda suka yi zabe har zuwa kashi 62 bisa 100, duk kuwa da cewa wadanda suka yi rajista sun zarce wadanda suka yi a 2015.

Ya ce irin wannan tuggun aka kitsa a jihohi kamar Ribas, Delta, Abia da Benuwai.

Atiku ya yi mamakin yadda kashi 82 na wadanda suka yi rajista wai aka ce duk sun fito. Ya kara da cewa haka aka yi a yankuna da dama inda APC ta ke da magoya baya sosai.

Ya yi mamakin duk da matsalar tsaro a cikin jihar, amma a ce an jefa kashi 82 bisa 100 na adadin kuri’un wadanda suka yanki rajista.

Ya kara da cewa bai kuma yarda da sakamakon da ya nuna adadin kuri’un da PDP ta samu a Fadar Gwamnatin Tarayya, Kudu Maso Gabas da Kudu masu Kudu.

“Ba wai ina magana don na yi takarar shugaban kasa ba. Ni ina magana ne a matsayi nan a dan Najeriya, saboda duk wanda ya yi nazarin zaben nan da idon basira zai fahimci cewa babu yadda za a yi ace APC ta samu yawan wadannan kuri’u.

“A kan wasu dalilai da kuma wadannan da na bayyana ne na ke cewa ni Atiku Abubakar ban amince da sakamakon da INEC ta bayyana Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya yi nasara ba.”

Ya yi kira ga magoya bayan sa su dau hakuri, domin ya na da yakinin cewa nasara a gare shi ta ke.
Premiumtimeshausa.

[Next Level] : Munshiga Next Level By Rarara New Song

Ibrahim Auwal | February 27, 2019 | 0 Comments

Kalli yanda Maryam Yahaya ta kada kuri'arta

Ibrahim Auwal | February 24, 2019 | 0 Comments

       Kalli yanda Maryam Yahaya ta kada kuri'arta

Jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan hotunan inda take akan layin zabe, Jiya, Asabar, ta bayyana cewa ta sakawa jam'iyyarta sannan ta ce 4+4.

              

Buratai ya jagoranci tattakin soji

Ibrahim Auwal | February 23, 2019 | 0 Comments
Shugaban rundunar sojin Najeriya, janar Tukur Yusuf Buratai kenan a wadannan hotunan yayin da ya jagoranci tattakin da sojoji suka yi da safiyar yau.Zaben Najeriya: Za a yi ta ta kare tsakanin Atiku da Buhari

Ibrahim Auwal | February 23, 2019 | 0 Comments
'Yan Najeriya na shirin kada kuri'a don zaben shugabannin da za su ja ragamar kasar a matakin shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki.


Misalin karfe 8:00 na safiyar Asabar agogon Najeriya ake sa ran bude rumfunan babban zaben wanda aka dage tsawon mako daya saboda matsaloli da suka shafi raba kayan zabe a sassan kasar.

'Yan takara sama da 70 ne ke neman darewa kujerar shugaban kasa a zaben, amma Shugaba Muhammadu Buhari na APC mai shekara 76, da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na PDP, mai shekara 72 ne suka fi jan hankali a zaben.

Buhari ya ce ba zai fadi zabe ba

Ibrahim Auwal | February 23, 2019 | 0 Comments

Buhari ya ce ba zai fadi zabe ba
Ku latsa alamar lasifika domin sauraren muryar Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu makawa shi ne zai lashe zaben shugaban kasar.
Da yake amsa tambayar wakilin BBC kan ko zai amince idan ya sha kaye, sai ya ce "ni zan ci zabe."
Shugaba Buhari ya kada kuri'arsa ce a birnin Daura da ke jihar Katsina tare ds mai dakinsa Aisha Buhari da rakiyar wasu jami'an gwamnatinsa.
Sai dai abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce a matsayinsa na mai kare mulkin dimokradiyya zai yi biyayya ga sakamakon zaben kasar.
Wasu hotuna sun nuna yadda Shugaba Buhari ya kada kuri'a inda ya zabi kansa.
Mai daukar hoto na kamfanin dillancin labaran Reuters ya dauki hotunan takardun kada kuri'ar Buhari, wadanda suka nuna cewa ya zabi kansa.
BuhariHakkin mallakar hotoREUTERS
Hukumar zaben Najeriya dai tana ba da shawara kada masu kada kuri'a su bayyana wanda suka zaba, saboda hakan ya saba tsarin tarbiyyar dimokradiyya.

Hare-hare

Sa'o'i biyu kafin bude rumfunan zabe ranar Asabar, al'ummar Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar sun ce sun ji fashewar bama-bamai da harbe-harben bindiga.
A wata sanarwa, 'yan sandan jihar sun ce babu wata barazana ga jama'a. "Jami'an tsaro ne suka yi harbe-harben domin tauna tsakuwa," in ji sanarwar.
Jihar Borno dai ta kasance cibiyar mayakan Boko Haram wadda ta yi shirin ganin ba a gudanar da zaben ba.
Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya rawaito cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar ne sun kai hari garin Geidam, inda suka tilasta wa jama'ar garin ficewa daga garin.

Me ya sa aka dage zabe?

Sa'o'i biyar kafin bude rumfunan zabe ne dai a ranar Asabar ta 16 ga Fabrairu hukumar zaben Najeria ta sanar da dage zaben.
Hukumar ta bayar da dalilan da suka janyo dage zaben da suka hada da yunkurin yin magudi da rashin kai kayan aiki mazabu da kuma rashin kyawun yanayi.
Yanzu hukumar ta INEC ta ce ta shirya tsaf domin tafiyar da zaben.
Wannan Layi ne

Yadda zaben yake?

Duk dan takarar da ya samu kuri'un da suka fi yawa, idan dai har ya samu kaso 25 na kuri'un da aka kada a jihohi 24 daga jihohi 36 na kasar.
'Yan takara 73 ne suke neman kujerar shugabancin kasar amma fafatawar ta fi zafi tsakanin 'yan takarar jam'iyyu biyu.
Taken Jam'iyyar shugaba mai ci, Muhammadu Buhari shi ne 'Next Level' wato kai Najeriya zuwa matakin ci gaba.
Ita kuma jam'iyyar adawa ta PDP wadda tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar yake takara na da taken 'to get Nigeria working again', abin da ke nufin jam'iyyar za ta dawo wa najeriyar hayyacinta.
Atiku Abubakar ya kalubalanci Shugaba Buhari da lalata shekaru hudun da ya kwashe a kan karaga.
Dukkanin 'yan takarar guda biyu dai sun fito daga yankin arewacin kasar mai yawan musulmai. Kuma dukkanninsu sun wuce shekara 70 da haihuwa.

Matsalolin Najeriya

Najeriya ce dai kasa mafi girma a yawan jama'a da kuma yawan albarkatun man fetur. To sai dai rashawa da cin hanci da kuma gaza zuba rarar da ake samu daga sayar da man a kasuwar duniya ne ke tarnaki ga cigaban kasar.
A 2016, kasar ta samu komadar tattalin arziki. An kuma samu jan kafa kafin kasar ta samu ta farfado, al'amarin da ke nuni da cewa ba a samar da isassun ayyukan yi ga miliyoyin matasan kasar da ke neman aiki ba.
Za a iya cewa kaso daya bisa hudu na matasan kasar ba su da abun yi.
Wannan Layi ne
Alkaluman masu zabe
•Yan takarar shugaban kasa guda 73
•Masu katin zabe miliyan 73
•Kaso 51 da masu kati 'yan kasa da shekara 35
•Akwai rumfunan zabe dubu 120a fadin kasar.
.......
BuhariHakkin mallakar hotoREUTERS
Shugaba Buhari ya ce ya murkushe kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, to sai dai har yanzu kungiyar na da karfi.
Sannan kuma ana ta yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin arewa maso tsakiyar kasar.
Najeriya dai ta fuskanci mulkin soji har zuwa 1999, duk da cewa an samu gwamnatocin dimokradiyya wadanda ba su yi tsawon rai ba kafin nan.
A bana kasar ke cika shekara 20 da dawo wa turbar dimokradiyya.
A 2015 ne aka zabi shugaba Buhari, lokacin da kasar ta kafa tarihi, inda dan takarar jam'iyyar adawa ya kayar da shugaba mai ci.

'Yan sanda ke tsaron rumfar zabe ba sojoji ba>>INEC

Ibrahim Auwal | February 21, 2019 | 0 Comments
Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce 'yan sanda ne ke da hakkin kula da rumfunan zabe ba sojoji ba.


Shugaban hukumar INEC ne Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a lokacin yake bayani kan shirin zabe da kuma amsa tambayoyi a ranar Alhamis.

An tambayi shugaban INEC ne kan irin rawar da sojoji za su taka a ranar zabe, sai ya amsa da cewa tsarin da aka sani shi ne, ba hakkin sojoji ba ne kula da tsaro a rumfunan zabe, amma ya danganta da gayyatar da suka samu daga 'yan sanda.

Ya ce hukumar INEC na aiki ne da hukumar 'yan sanda amma idan suna fuskantar wata barazana suna iya gayyato sauran jami'an tsaro da suka hada da sojoji domin su taimaka."Sojoji na iya yin aikin da ya rataya a wuyan 'yan sanda a wurin zabe idan har 'yan sandan sun gayyace su."

"Ya danganta da barazanar da ta taso amma aikin tabbatar da tsaro a rumfunan zabe aikin 'yan sanda ne," in ji shugaban hukumar INEC.

Wannan na zuwa ne bayan babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai, a ranar Laraba ya bayyana rawar da sojoji za su taka a ranar zabe.

Yayin da yake gana wa da manyan jami'ai da kwamandojin sojin kasar, Janar Burutai ya yi umurni ga kwamandojinsa su dauki mataki na ba sani ba sabo kan duk wanda ya nemi dagula sha'anin zabe a kasar.

Ya ce rundunar sojin kasar ta dauki mataki kan satar akwati da kayayyakin zabe da aka saba yi a zabukan baya.

Tun da farko shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi gargadi ga barayin akwatin zabe inda ya umurci jami'an tsaron kasar daukar matakin ba sani ba sabo na rashin tausayi ga duk barawon akwatin zaben da suka kama.
BBChausa.

Teema Makamashi ta yadda tafiyar Atiku ta koma goyon bayan Buhari

Ibrahim Auwal | February 21, 2019 | 0 Comments


Tauraruwar fina-finan Hausa, Teema Makamashi wadda ada tana gaba-gaba wajan tallata dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yanzu ta yadda tafiyar Atikun ta koma goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Dama dai tuni Teemar ta saki sakon cewa zata fitar da labari me daukar hankali.
Ali Nuhu ya haskaka a wadannan hotunan

Ibrahim Auwal | February 21, 2019 | 0 Comments
Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Sarki kenan a wadannan hotunan nashi da ya haskaka, muna mai fatan Alheri.
Waye ya fi amfana da dage zaben 2019? Atiku Ko Buhari

Ibrahim Auwal | February 21, 2019 | 0 Comments
Adhoc ObserversHakkin mallakar hotoAFP
Najeriya za ta gudanar da babban zabenta a ranar Asabar bayan dage zaben da aka yi lokacin wani taron manema labarai da shugaban hukumar ya jagoranta.
Dage zaben kwatsam a dare daya ya bai wa 'yan kasar mamaki kuma hakan ya kawo takura ga dubban 'yan Najeriyar musamman wadanda suka sha doguwar tafiya domin kada kuri'arsu.
Cibiyar masana'antu da kasuwanci ta Legas ta ce hakan ya jawo asarar dalar Amurka biliyan 1 da dubu dari biyar.
Hukumar zaben kasar ta kawo dalilai da dama da suka yi sanadiyyar dage zaben wadanda suka hada da zargin makarkashiya da aka yi musamman ta bangaren jigilar kayyayakin zaben da kuma matsalar yanayi da ya hana jirgin sama tashi domin kai takardun zabe.Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriyar da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP duk sun nuna rashin jin dadinsu dangane da dage zaben kuma jam'iyyun sun zargin junansu da kokarin tafka magudin zabe.

Akwai jam'iyyar da dage zaben zai fi zama alheri a gareta?

A sanarwar da aka fitar ranar dage zaben, jam'iyyar APC ta zargi PDP da kokarin dakushe kwarjinin dan takararta Muhammadu Buhari.
A dayan bangaren jam'iyyar PDP wacce dan takararta shi ne Atiku Abubakar ta zargi cewa hukumar zaben ta jinkirta zaben ne domin bayar da dama domin tafka magudin zabe.
Wata mai fashin baki a kan al'amuran yau da kullum Idayat Hassan da ke cibiyar dimokradiyya da ci gaba a Abuja ta bayyana cewa jinkirta zaben da mako guda ba zai yi wani tasiri wajen gudanar da magudin zabe.
President Muhammadu Buhari and Atiku AbubakarHakkin mallakar hotoREUTERS
Ta kwatanta dage zaben da aka yi a yanzu da kuma na 2015 a lokacin mulkin PDP inda suka dage zaben da kusan mako shida saboda zargin da suke yi na hare-haren Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Wancan dage zaben ta bayyana cewa ya zama alheri ga APC inda hakan ya jawo wa PDP bakin jini a matsayin jam'iyyar da ke neman mulki ko ta wane hali.
Amma ta nuna cewa dagen zaben zai iya zama alheri ga APC ma a wannan lokaci saboda za a iya samun karancin fitowar mutane, amma za a iya samun fitowar mutane da dama a wuraren da tun asali ana samun tururuwar fitowar mutane a ranar zabe,
Misali yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas kuma nan ne Buhari ya fi yawan magoya baya.

Shugaba Buhari ya amshi bakuncin wakilan Sarkin Saudiyya

Ibrahim Auwal | February 21, 2019 | 0 Comments
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amshi bakuncin wakilan sarkin kasar Saudiyya, Sarki Salman Bin Abdulaziz jiya a fadarshi ta Villa dake babban birnin tarayya, Abuja.


Kyawawan Hotunan Maryam Yahya

Ibrahim Auwal | February 17, 2019 | 0 Comments
Kyawawan Hotunan Maryam Yahya
Jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan hotunan nata da ta haskaka, tasha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.  
                       


[Music] Wazirin Rarara -Akwai Hujjar Daga Zabe

Ibrahim Auwal | February 17, 2019 | 0 Comments

Sabuwar Wakar Wazirin rarara mai suna ” Akwai Hujjar Daga Zabe ” wannan wakar mawakin yayita akan dalilin dage zabe da akayi.
GA KADAN DAGA BAITIN WAKAR:
– Kubani kidan dage zabe
– Akwai hujjar dage zabe
– Yan uba kar kuyi mana sobe
– Mujira satinmu na gobe– Matsaloline muka hanga
– Dan naji magwauta na mana burga
– Yan PDP na zuga
– Wai buhari ya kasa
– Mu adalci muka dosa
1. Akwai Hujjar Daga Sabe:-
Audio Player
Vm
P
DOWNLOAD MP3

[Music] Rarara Da Babancinedu -Da Tuni Yanzu Baba Yaci Zabe

Ibrahim Auwal | February 17, 2019 | 1Comments

'Da tuni baba ya ci zabe'>>Rarara ya saki sabuwar waka kan dage zabe

Bayan da hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta dage zaben da aka tsara yi ranar Asabar din data gabata, wasu sun rika yiwa mawaki, Rarara tambayar shin wace irin waka zai wa shugaba Buhari yanzu, ganin cewa a lokacin Jonathan da irin haka ta faru yayi waka? Rararan dai yanzu ya basu amsa.

Sabuwar wakar da Rarara ya fitar da yake cewa da tuni baba ya ci zabe yanzu haka ta fara yawo a tsakanin jama'a.

Idan baka jita ba gata nan a kasa:
kalli bidiyon Anan
1. Da Yanzu Angama Da Tuni Yanzu Baba Yaci Zabe:-
Audio Player
Vm
P
DOWNLOAD MP3

Ban yi ridda ba cin mutuncine kawai>>Buba Galadima ya kare kanshi

Ibrahim Auwal | February 17, 2019 | 0 Comments
Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Buba Galadima wanda a yanzu ya koma bangaren adawa yake kuma caccakar gwamnatin APC ta shugaba Buhari ya fito ya kare kanshi akan wani labari dake yawo a shafukan sada zumunta inda yace an zargeshi da yin ridda.

Buba Galadima a cikin wani sako da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta yace an rika yada cewa yayi ridda wanda shi kuma maganar da yayi ya danganta zabe da Allah ai Allah ne karshe a wajan gaskiya shiyasa ya fadi haka:

Buba yace ga gaskiyar abinda ya fadi anan kasa amma aka samu wasu yara da suka raina manya ana biyansu kudi suna ci musu mutunci:


Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya mayarwa da Buba Galadiman cewa har yanzu dai ana nan dan kwata-kwata be kamata yayi misalin da Allah ba:

Jawabin Mai martaba Sarkin Kano akan Shigar Malamai Siyasa

Ibrahim Auwal | February 17, 2019 | 0 Comments
Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II Yayi Bayani Mai Muhimmanci.

Ba’a Hana Mutum Ra’ayi Ba, Kowa Yana da Ra’ayinsa, Amman Kada Ku Shigar Da Kanku Cikin Siyasa. Malamai Su Hau Kan Mumbari ko Hakimai su Tara Jama’a Ace A Zabi Wanannan Jam’iyya Ko Waccan Ba Aikinmu Bane.


Ka Futo Akan Mumbari Ko Gidan Radio Ko Gidan Talabijin Shi Ne Ya Kawo Malamai Suna magana ‘yan siyasa suna Magana, Martabar Da Allah Yayi Muku Na Malamai Da Sarautar Nan Kada Mu Ringa Shigar Da Ita Inda Wani Zai Zage mu, Koya Shiga Cikin Mutuncinku Wannan fagen su ne.

Kwanakin Can Baya Munyi Magana Mukace In Za’a Zabi Shugabanni A Zabi Mai Ilimi, ‘Yan Jarida Sukace Sarkin Kano Yace Kar A Zabi Wani Dan Takara Don Bashi Da Certificate, Ni Ban San Maganar Certificate Ba Kuma Maganar Ilimi Nayi.

Sannan Mai Martaba Sarki Ya Ja Hankalin ‘Yan Siyasa Dangane da Haifar Da Sara Da Suka A Yayin Kamfen, Da Kuma Munanan Kalamai Da ‘Yan Siyasa Keyi, Indai Sarkin Yace Wannan Ba Komai Bane Sai Warware Addu’o’in Zaman Lafiya Da Sarkin Ke Jagoranta.

Sannan Ya Nemi Da A Gurfanar Da Duk ‘Yan Siyasar Da Sukayi Kira Kan A Zubda Jinin Al’umma A Gaban Hukuma. A Karshe Mai Martaba Sarkin Yayi Jan Hankali Sosai Dangane Da Wannan Zabe Dake Karatomu. Ubangiji Allah Ya Karawa Sarki Ingantacciyar Lafiya Da Nisan Kwana Mai Amfani. Ameen.

Fati Shu'uma Sanye Da Kayan Campaign Na Buhari

Ibrahim Auwal | February 17, 2019 | 0 Comments
Fati Shu'uma Sanye Da Kayan Campaign Na Buhari


Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Shu'uma kenan a wannan hoton nata da take sanye da hular yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta haskaka, muna mata fatan Alheri.

Karanta abinda Jega yace akan dage zabe

Ibrahim Auwal | February 16, 2019 | 0 Comments

Karanta abinda Jega yace akan dage zabe

Tsohon shugaban hukumar zabe me zaman kanta, INEC watau farfesa Attahiru Jega ya bayyana ra'ayinshi akan dage ranar zabe da INEC din tayi, Jega yace shima be ji dadin dage zaben ba amma yana kira ga 'yan Najeriya da su yadda da kaddara.

INEC ta nemi afuwar 'yan Najeriya

Ibrahim Auwal | February 16, 2019 | 0 Comments

INEC ta nemi afuwar 'yan Najeriya

Hukumar zaben Najeriya INEC ta nemi afuwar 'yan kasar bayan da ta dage zaben da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar.


An dage babban zaben shekarar 2019 ne sa'o'i kalilan kafin fara shi, inda aka dage shi zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar 2019.

Wani darakta a hukumar zaben kasar Festus Okaye ya ce har bayan karfe 12;00 na daren ranar Asabar hukumar tana da tabbacin za ta iya gudanar da zaben.

Jami'in ya ce sun samu matsala ne akalla a bakwai daga cikin jihohi 36 da ke fadin kasar.


Mista Festus ya ce hukumar zaben ta yi takaicin abin da ya faru kuma saboda haka tana neman afuwa daga 'yan kasar.

Daga nan ya ba da tabbacin cewa hukumar zaben ta dukufa wajen ganin ta gudanar da zaben kamar yadda aka tsara a mako mai zuwa.

Ya bukaci 'yan kasar da su ba hukumar goyon baya don ganin ta gudanar da sahihin zabe.

Mutane da dama ne suka rika bayyana rashin jin dadinsu da matakin da hukumar ta dauka na dage zaben a ranar Asabar, musamman a kafafen sada zumunta.
BBChausa.
 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger