Masu Garkuwa Da Mutane Sun Kashe Shugaban Kungiyar Fityanul Islam Na Karamar Hukumar Jama'a Jihar Kaduna

Ibrahim Auwal | May 26, 2019 | 0 Comments

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Kashe Shugaban Kungiyar Fityanul Islam Na Karamar Hukumar Jama'a Jihar Kaduna

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN 
Yanzu muka samu labarin cewa an tsinci gawar Shugaban Kungiyar Fityanul Islam na karamar hukumar Jama'a dake jihar Kaduna. 


Dama tun makonni biyar da suka gabata wasu mutane wadanda ake tasamanin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da shi, mun samu labarin an tsinci gawar shi a safiyar yau. 

Muna mika ta'aziyya a madadin kungiyan fityanul Islam gaba daya.

Allah ya jikansa ha gafara masa yasa aljanna ce makomarsa, su kuma wadannan miyagun Allah ya tona asirinsu, amin.
Rariya.

Kalli Umar M. Shariff da mahaifiyarshi sunje aikin Umrah

Ibrahim Auwal | May 26, 2019 | 0 Comments

Kalli Umar M. Shariff da mahaifiyarshi sunje aikin Umrah

Tauraron mawakin Hausa kuma jarumi a fina-finan Hausa, Umar M. Shariff kenan a wannan  hoton inda yake tare da mahaifiyarshi da suka je aikin Umrah tare.

Kayatattun hotunan A'isha Tsamiya daga Saudiyya

Ibrahim Auwal | May 26, 2019 | 0 Comments

Kayatattun hotunan A'isha Tsamiya daga Saudiyya

Tauraruwar fina-finan Hausa, A'isha Tsamiya kenan a wadannan hotunan nata data dauka a ksa me tsarki inda taje aikin Umrah, tasha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.
AISHA BUHARI TA SOKI GWAMNATIN SHUGABA BUHARI

Ibrahim Auwal | May 26, 2019 | 0 Comments
Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta ce shirin bayar da tallafi na gwamnati (SIP) da Uwargida Maryam Uwais, mai taimaka wa shugaban kasa a kan shirin tallafi, ke jagoranta, ya gaza a yankin arewa.


Da take magana ranar Asabar yayin wani taro da aka yi a fadar shugaban kasa, Aisha Buhari ta ce an fada mata cewar kimanin mata 30,000 ne daga jihar Adamawa zasu ci moriyar shirin amma sai gashi hakan ta gaza yiwuwa.

Da take magana a kan Uwargida Maryam, Aisha Buhari ta bayyana cewar an ba ta mukamin ne tun farko domin saka wa Kanawa a kan miliyoyin kuri'un da suka zazzaga wa mijinta a zaben shekarar 2015

'Yar asalin jihar Kano, Uwargida Maryam, mata ce ga tsohon alkalin alkalan Najeriya, Jastis Mohammed Lawal Uwais.

"Biliyan N500 da gwamnati ta ware wa shirin SIP na daga cikin alkawuran da jam'iyyar APC tayi na ciyar da dalibai a makarantun firamare da bawa mutanen da talauci ya dama tallafin N5000 duk wata.

"Mai taimaka wa miji na a kan shirin macece 'ya asalin Kano, wacce na tabbata ya bata mukamin ne domin saka wa mutanen Kano a kan kuri'un da suka bashi a zaben shekarar 2015. Ban taba tambayar yadda ake amfani da kudin da gwamnati ta ware ba.

"Na taba haduwa da daya daga cikin hadiman jagoran shirin SIP wanda ya yi min alkawarin cewar za a ke bawa mata 30,000 N10,000 kowanne wata, amma har yau ba a yi hakan ba kuma ban kara ji daga gare shi ba," a cewar uwargidan ta shugaban kasa.

"Ba zan yi magana mai tsawo ba don kar a ce ina sukar gwamnati ko na cika surutu amma ni na san alkawarin da muka daukar wa jama'a shine za ake bawa talakawa futik tallafin N5,000 kowanne wata amma sai gashi da na je Kano naga wani dattijo da ke sayar da kayayyaki da yace jarinsa bai fi 3,000 zuwa 4,000 ba.

"Ban san a wanne wuri shirin ya yi tasiri ba amma dai a arewa, musamman a jihar Adamawa, shirin bayar da tallafin bai amfani jama'a ba. Karamar hukuma daya ce a cikin 22 ta ci moriyar shirin. Hatta a jihar Kano shirin bai tabuka komai saboda mata dake kananan sana'o'i basu samu tallafin komai ba," a cewar Aisha Buhari.
Rariya

 
Support : Creating Website | Johny Template | Mas Template
Copyright © 2011. Arewa Now - All Rights Reserved
Template Modify by Creating Website
Proudly powered by Blogger